Gabatarwa
Waɗanne abubuwa masu kyau ne Allah ya ce zai yi wa mutane? Me ya tabbatar mana cewa ba a canja saƙon da ke rubutacciyar Kalmar Allah ba? A talifofin da ke biye, za ka ga wasu alkawuran da Allah ya yi mana, da dalilin da ya sa ya kamata mu gaskata da su, kuma za a bayyana abin da za ka yi don ka sami albarkunsa.