DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 10-11
Kwatanci Game da Basamariye Mai Kirki
Yesu ya yi wannan kwatancin domin ya ba da amsar tambayar nan: “Shin, wane ne maƙwabcina?” (Lu 10:25-29) Yesu ya san cewa ikilisiyar Kirista za ta ƙunshi “dukan mutane,” har da Samariyawa da mutane daga wasu ƙasashe. (Yoh 12:32) Yesu ya yi amfani da wannan kwatancin don ya koya wa mabiyansa yadda za su riƙa yin iya ƙoƙarinsu don su ƙaunaci mutane har da waɗanda ba su cika sha’ani da su ba.
KA TAMBAYI KANKA:
‘Yaya nake ɗaukan ’yan’uwan da al’adarmu ba ɗaya ba ce?’
‘Na fi yin tarayya da waɗanda na fi so kawai?’
‘Ya dace na ƙaunaci ’yan’uwan da suka fito daga wurare dabam-dabam?’ (2Ko 6:13)
Zan so in gayyaci . . . don
mu yi wa’azi tare
ya zo gidana mu ci abinci tare
mu yi Ibada ta Iyali tare a mako mai zuwa