Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Nuwamba p. 7
  • “Ba da Kyauta ga Jehobah”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ba da Kyauta ga Jehobah”
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Muna Gode wa Jehobah don Ƙaunarku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kudin Yin Ayyukansu?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Darajar Anini Biyu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Nuwamba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

“Ba da Kyauta ga Jehobah”

Wani yana saka gudummawa a cikin akwatin ba da gudummawa; wani yana ba da gudummawa ta wayar selula

Ta yaya za mu yi “bayarwa ta yardar rai” ga Jehobah a yau? (1Tar 29:​5, 9, 14) Ga hanyoyi dabam-dabam da za mu iya bi don mu tallafa wa ayyukan da ƙungiyar Jehobah take yi a ikilisiyarmu da ma na faɗin duniya.

GUDUMMAWA DA AKE YI TA INTANE KO WANDA AKE SAKAWA A AKWATUNA SUNA TALLAFA WA:

  • Ba da gudummawa don taimaka wa aikin da ake yi a fadin duniya

    AYYUKA DA MUKE YI A DUK DUNIYA

    gina da kuma kula da manyan ofisoshinmu da ofisoshin fassara

    kula da makarantunmu

    kula da masu hidima ta musamman

    tanadar da kayan agaji

    shirya bidiyoyi, buga littattafai da kuma abubuwan da muke wallafawa a intane

  • Ba da gudummawa don ayyukan da ake yi a ikilisiya

    KUƊAƊEN DA IKILISIYOYI SUKE KASHEWA

    gyare-gyaren da ake yi da kuma kula da Majami’ar Mulki

    wa’adi da ikilisiyoyi suka yi a kan yawan kuɗin da za a riƙa aika wa ofishinmu don:

    • gina Majami’un Mulki da kuma Majami’un manyan taro a dukan duniya

    • tsarin tallafawa a faɗin duniya

    • wasu ayyukan da ƙungiyar take yi a faɗin duniya

TARON YANKI DA NA DA’IRA

Ana amfani da duk gudummawar da aka yi a lokacin taron yanki wajen tallafa wa ayyukanmu a faɗin duniya. Daga cikin wannan gudummawar ne ake kula da dukan bukatun da suka taso a lokacin taron yanki ko taro na musamman ko kuma taro na ƙasashe.

Ana amfani da gudummawa da ake yi don taron da’ira wajen yin rancen wurin da za a yi taron, da kuma kula da wurin da dai sauransu. ’Yan’uwa a wannan da’irar suna iya zaɓan su ba da ƙarin kuɗi don a tallafa wa aikin da ake yi a faɗin duniya.

donate.jw.org

KA DUBA ƘARIN BAYANI A DANDALINMU

Ga hanyoyin da za ka iya bi don ka ga yadda za ka iya ba da gudummawa:

  • ka shiga donate.jw.org

  • ka danna “ka ba da gudummawa” a sashen Game Da Mu da ke jw.org/ha

  • ka shiga sashen “Donations” da ke ƙarƙashin shafin farko na manhajar JW Library

A wasu ƙasashe, akwai wani talifi mai jigo “Tambayoyi da Ake Yawan Yi” game da gudummawa. Talifin ya ba da amsoshi ga tambayoyi da ake yawan yi game da gudummawa.

Bidiyon nan Yadda Za a Ba da Gudummawa ta Na’ura ya nuna hanyoyi dabam-dabam da za mu iya bi don mu ba da gudummawa.

WASU HANYOYIN BA DA GUDUMMAWA

Wasu hanyoyin da ake bi kafin a ba da gudummawa sukan bukaci shiri tun da wuri ko kuma shawara daga wurin lauya. Irin waɗannan gudummawar su ne:

  • wasiyya da ajiya

  • fegi da gida da hannayen jari da inshora

  • rance

Idan kana son ka yi irin wannan gudummawa, ka tuntuɓi ofishinmu ta wurin adireshinmu da ke shafin donate.jw.org.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba