RAYUWAR KIRISTA
Ka Zama Ƙwararren Ma’aikaci
Kafinta da ya ƙware ya san yadda yake amfani da kayan aikinsa. Haka ma, “ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gare shi” ya san yadda zai yi amfani da littattafanmu da kyau. (2Ti 2:15, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ka amsa tambayoyi na gaba don ka ga ko ka san yadda za ka yi amfani da littattafanmu da kyau a wa’azi.
KA SAURARI ALLAH DON KA RAYU HAR ABADA
Don su wa aka shirya wannan ƙasidar?—mwb17.03 5 sakin layi na 1-2
Ta yaya za ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita?—km 7/12 3 sakin layi na 6
Waɗanne ƙarin littattafai ne kake bukata don ka taimaka ma ɗalibinka ya yi baftisma?—km 7/12 3 sakin layi na 7
ALBISHIRI DAGA ALLAH!
Ta yaya wannan ƙasidar ta yi dabam da sauran littattafanmu na nazari?—km 3/13 5 sakin layi na 3-5
Me ya kamata ka yi ƙoƙarin yi sa’ad da kake ba da ita?—km 9/15 3 sakin layi na 1
Ta yaya za ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita?—mwb16.01 8
A wane lokaci ne ya kamata ka soma amfani da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?—km 3/13 7 sakin layi na 10
ME ZA MU KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?
Ta yaya aka shirya yadda za a yi amfani da taƙaitawa da kuma ƙarin bayani na littafin?—mwb16.11 5 sakin layi na 2-3
SU WANE NE SUKE YIN NUFIN JEHOBAH A YAU?
A wane lokaci ne ya kamata ka yi amfani da wannan ƙasidar?—mwb17.03 8 sakin layi na 1
Ta yaya aka shirya yadda za a tattauna ta?—mwb17.03 8, akwati