DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 25-26
Abu Mafi Muhimmanci a Mazauni
25:9, 21, 22
Akwatin Yarjejeniya shi ne abu mafi muhimmanci da ke cikin mazauni da kuma inda Isra’ilawa suka yi zango. Gajimare da ke tsakanin cherubim guda biyu da ke saman Akwatin yana nuna cewa Allah yana tare da su. A Ranar Ɗaukar Alhakin Zunubi, babban firist yakan shiga Wuri Mafi Tsarki kuma ya warwatsa jinin bijimi ko na akuya a gaban akwatin don gafarar zunuban Isra’ilawa. (L.Fi 16:14, 15) Hakan na wakiltar yadda Yesu wanda shi ne Firist Mafi Girma ya je gaban Jehobah a sama kuma ya miƙa amfanin hadayarsa.—Ibr 9:24-26.
Ku jera waɗannan nassosin don su jitu da albarkun da muke samuwa don fansar Yesu:
NASSOSI
- 1Yo 1:8, 9 
- Ibr 9:13, 14 
ALBARKU
- begen rayuwa har abada 
- gafarar zunubai 
- zuciya mai tsabta 
Me ya zama dole mu yi don mu more albarkun nan?