DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 33-34
Halayen Jehobah Masu Ban Sha’awa
34:5-7
Musa ya koyi halayen Jehobah, kuma hakan ya taimaka masa ya bi da Isra’ilawa cikin haƙuri. Mu ma idan muka fahimci halayen Jehobah sosai, za mu riƙa tausaya ma ’yan’uwanmu.
“Mai jinƙai ne”: Jehobah yana kula da bayinsa cikin ƙauna da tausayi kamar yadda iyaye suke kula da ’ya’yansu
“Marar saurin fushi”: Jehobah yana haƙuri da bayinsa, ba ya mai da hankali ga kurakuransu amma yana ba su lokaci domin su canja
“Mai yawan ƙauna”: Jehobah yana ƙaunar bayinsa sosai kuma dangantakarsa da su ba za ta mutu ba
KA TAMBAYI KANKA, ‘Ta yaya zan yi koyi da yadda Jehobah yake nuna jinƙai da tausayi?’