Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Disamba p. 3
  • Mu Nuna Kauna ga Jehobah ta Wajen Amincewa da Horonsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Nuna Kauna ga Jehobah ta Wajen Amincewa da Horonsa
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙauna Ce Take Sa Jehobah Ya Yi Mana Horo
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Horo, Alama Ce Ta Kaunar Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Disamba p. 3

RAYUWAR KIRISTA

Mu Nuna Ƙauna ga Jehobah ta Wajen Amincewa da Horonsa

Yankan zumunci na ƙare ikilisiya kuma horo ne ga waɗanda suka yi zunubi kuma suka ki tuba. (1Ko 5:​6, 11) Muna nuna ƙauna idan muna goyon bayan horon Jehobah. Ta yaya hakan zai yiwu idan yankan zumuncin ya jawo baƙin ciki ga mutumin da iyalinsa da kuma dattawa?

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, idan muka goyi bayan Jehobah muna nuna cewa muna ƙaunar sunansa da kuma tsari da ya kafa mana game da tsarki. (1Bi 1:​14-16) Ban da haka ma, muna nuna ƙauna ga wanda aka yi masa yankan zumunci. Ko da yake horo na da zafi, “yakan haifar da adalci da salama.” (Ibr 12:​5, 6, 11) Idan mun yi cuɗanya da wanda aka yi masa yankan zumunci ko kuma wanda ya bar ƙungiyar Jehobah, ba ma goyon bayan horon Jehobah ke nan. Ku tuna cewa Jehobah yana yi wa mutanensa horo “da shari’ar gaskiya.” (Irm 30:11) Fatanmu shi ne mutumin ya koma ga Ubanmu mai jinkai. Amma kafin mutumin ya komo, za mu ci gaba da goyon bayan yadda Jehobah yake ba da horo kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi.​—Ish 1:​16-18; 55:7.

KU KALLI WASAN KWAIKWAYON NAN KU NUNA AMINCI DA DUKAN ZUCIYARKU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Aminci da Dukan Zuciyarku.’ Ben da matarsa Gabriella suna kuka bayan sun karanta wasikar da dansu wanda ya bar gida ya rubuto musu.

    Yaya iyaye suke ji sa’ad da ɗansu ya daina bauta wa Jehobah?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Aminci da Dukan Zuciyarku.’ ’Yan’uwa suna karfafa Ben da matarsa Gabriella bayan an tashi taro.

    Ta yaya ikilisiya za ta iya taimaka ma iyayen?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Aminci da Dukan Zuciyarku.’ Gabriella tana tunani a kan labarin tawayen da Korah ya yi.

    Wane labarin Littafi Mai Tsarki ne ya koya mana cewa mu riƙa ƙaunar Jehobah fiye da membobin iyalinmu?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Ku Nuna Aminci da Dukan Zuciyarku.’ Bayan taro, Gabriella tana nuna wa mijinta Ben sakon tes da dansu ya turo.

    Ta yaya za mu nuna ma Jehobah ƙauna fiye da wani memban iyalinmu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba