KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Guji Abokan Banza
Wajibi ne ɗaliban Littafi Mai Tsarki su yi tarayya da abokan kirki domin su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Za 15:1, 4) Abokan kirki za su taimaka musu su yi abin da ya dace.—K. Ma 13:20; lff darasi na 48.
Sa’ad da kuke taimaka musu su guji abokan banza, ku bi su a hankali. Zai iya yi musu wuya su daina cuɗanya da abokansu da ba sa bauta wa Jehobah. Saboda haka, ku nuna kuna ƙaunarsu sosai ta wurin tarayya da su ko a ranaku da ba za ku yi nazari ba. Hakan ya ƙunshi tura saƙo, ko kira a waya, ko kuma ziyartar su. Yayin da suke samun ci gaba, za ku iya gayyatar su liyafa da ’yan’uwa. Hakan zai sa su ga cewa abin da suke samu ya fi waɗanda suka rasa. (Mk 10:29, 30) Za ku yi farin ciki yayin da kuke ganin ana ƙaruwa a ƙungiyar Jehobah.
KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU DAINA TARAYYA DA ABOKAN BANZA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Su waye ne abokan banza?—1Ko 15:33
Yaya Rose take tsammanin Kiristoci suke shaƙatawa?
Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose ta sami abokan kirki?