Dauda yana fuskantar Goliyat
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
‘Yaƙin Na Jehobah Ne’
Dauda ya kasance da bangaskiya domin abin da ya sani game da Jehobah, da kuma yadda ya taimaka masa (1Sam 17:36, 37; wp16.5 11 sakin layi na 2-3)
Ko da yake Goliyat ya fi Dauda girma, Dauda ya mai da hankali ga yadda Jehobah ya fi Goliyat (1Sam 17:45-47; wp16.5 11-12)
Jehobah ya sa Dauda ya yi nasara a kan wani magabci mai iko da ke tsoratar da su (1Sam 17:48-50; wp16.5 12 sakin layi na 4; ka duba hoton shafin farko)
A wasu lokuta, muna fama da matsaloli kamar, tsanantawa ko kuma wani halin da bai dace ba. Idan muna ganin matsalolin sun fi ƙarfinmu, zai dace mu tuna cewa matsalolinmu ba kome ba ne ga Jehobah mai iko duka.—Ayu 42:1, 2.