Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Maris p. 7
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Ka Amince da Taimakon Jehobah ta Wurin Yin Addu’a
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Yin Tambayoyi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Maris p. 7

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So

Waɗanda suke da ɗabi’u masu kyau ne kawai, za su more dangantaka na kud da kud da Jehobah. (1Bi 1:14-16) Idan ɗalibanmu suka daina halaye marasa kyau, iyalinsu za su amfana, za su kasance da ƙoshin lafiya kuma ba za su riƙa kashe kuɗi a banza ba.

Ka bayyana musu ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a, da dalilin da ya sa za su bi ƙa’idodin da kuma amfaninsu. Ka mai da hankali wajen taimaka wa ɗalibanka su canja ra’ayinsu, ta hakan za su yi abin da Jehobah yake so. (Afi 4:22-24) Ka tabbatar musu cewa Jehobah zai taimaka musu su daina halin da ya zama musu jiki. (Fib 4:13) Ka koya musu yadda za su yi addu’a sa’ad da suka fuskanci jarabar yin zunubi. Ka taimaka musu su san yanayoyin da za su iya jefa su cikin matsala kuma su guje su. Ka ƙarfafa su su riƙa yin abubuwan da za su amfane su maimakon abubuwa marasa kyau. Za ka yi farin ciki sa’ad da ka ga yadda Jehobah yake taimaka wa ɗalibanka su yi canje-canje a rayuwarsu.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU DAINA HALAYEN DA JEHOBAH BA YA SO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So.” Anita da Rose sun tattauna da dattawa.

    Ta yaya dattawa da Anita suka nuna cewa sun amince da Rose?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So.” Anita tana nazari da Rose.

    Ta yaya Anita ta ƙara taimaka wa Rose?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So.” Rose tana addu’a Jehobah ya tamaka mata.

    Ta yaya Rose ta nemi taimakon Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba