Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Maris p. 15
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Ka Koya wa Dalibanka Yadda Za Su Rika Nazari da Kansu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Yin Tambayoyi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Maris p. 15

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Zama Aminan Jehobah

Jehobah yana so mu bauta masa domin muna ƙaunarsa. (Mt 22:37, 38) Idan ɗalibanmu suna ƙaunar Jehobah, hakan zai taimaka musu su yi canje-canje kuma su tsaya daram sa’ad da suke fuskantar jarrabawa. (1Yo 5:3) Ƙauna da suke wa Jehobah ne za ta sa su yi baftisma.

Ka taimaka wa ɗalibanka su ga cewa Allah yana ƙaunarsu. Za ka iya tambayarsu cewa: “Mene ne wannan ya koya maka game da Jehobah?” ko kuma “Ta yaya hakan ya nuna cewa Allah yana ƙaunarka?” Ka sa su fahimci yadda Jehobah yake taimaka musu a rayuwa. (2Tar 16:9) Ka ba wa ɗalibanka misalan yadda Jehobah ya amsa addu’o’inka kuma ka ƙarfafa su su riƙa lura da yadda Jehobah yake amsa addu’o’insu. Muna farin ciki matuƙa sa’ad da ɗalibanmu suka san cewa Jehobah yana ƙaunarsu, kuma suna nuna cewa suna ƙaunarsa.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU ZAMA AMINAN JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Zama Aminan Jehobah.” Fuskar Rose a bace sa’ad da ta ke amsa waya.

    Wace matsala ce Rose ta fuskanta?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Zama Aminan Jehobah.” Anita tana magana da Rose.

    Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose?

  • Hoto daga bidiyon “Ku Taimaka Wa Dalibanku Su Zama Aminan Jehobah.” Rose tana tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka mata.

    Ta yaya Rose ta shawo kan matsalar?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba