DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ta Yaya Ayuba Ya Kasance da Tsabta a Ɗabiꞌarsa?
Ayuba ya yi yarjejeniya da idanunsa (Ayu 31:1; w10 4/15 21 sakin layi na 8)
Ayuba ya san sakamakon da yin zunubi ke jawowa (Ayu 31:2, 3; w08 10/1 27 sakin layi na 4)
Ayuba ya tuna cewa Jehobah yana lura da halayensa (Ayu 31:4; w10 11/15 5-6 sakin layi na 15-16)
Kasancewa da tsabta a ɗabiꞌa yana nufin mu zama da tsarki da rashin ƙazanta, ba kawai a abin da muke yi ba amma har a zuciyarmu.—Mt 5:28.