Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w20 Yuni pp. 2-7
  • “A Kiyaye Sunanka da Tsarki”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “A Kiyaye Sunanka da Tsarki”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MUHIMMANCIN SUNA
  • YADDA AKA FARA ƁATA SUNAN
  • JEHOBAH YANA TSARKAKE SUNANSA
  • ABIN DA ZA KA YI
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Sunan Jehobah Yana da Muhimmanci a Gare Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Me Ya Sa Sunan Jehobah Yake da Muhimmanci ga Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
w20 Yuni pp. 2-7

TALIFIN NAZARI NA 23

“A Kiyaye Sunanka da Tsarki”

“Sunanka, ya Yahweh na har abada ne.”​—Zab. 135:13.

WAƘA TA 10 Mu Yabi Jehobah Allahnmu!

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1-2. Waɗanne batutuwa ne suke da muhimmanci ga Shaidun Jehobah?

WAƊANNE batutuwa masu muhimmanci ne muke fuskanta a yau? Batutuwan su ne goyon bayan sarautar Jehobah da kuma tsarkake sunansa. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna son tattauna waɗannan batutuwa masu ban sha’awa. Amma akwai bambanci tsakanin goyan bayan sarautar Jehobah da kuma tsarkake sunansa ne? A’a.

2 Dukanmu mun san cewa wajibi ne mu tsarkake sunan Allah. Mun kuma koya cewa wajibi ne mu nuna cewa yadda Jehobah yake sarauta shi ne ya fi kyau. Dukan waɗannan batutuwa suna da muhimmanci.

3. Mene ne sunan Allah ya ƙunsa?

3 Sunan Jehobah ya ƙunshi kome game da Allahnmu, har da yadda yake sarauta. Saboda haka, idan muka ce tsarkake sunan Jehobah batu ne mai muhimmanci, muna nufin ya dace a nuna cewa yadda yake sarauta ne ya fi kyau. Sunan Jehobah yana da alaƙa sosai da yadda yake sarauta a matsayinsa na Maɗaukakin Sarki.​—Ka duba akwatin nan “Batutuwa Game da Tsarkake Sunan Allah.”

Batutuwa Game da Tsarkake Sunan Allah

Hoton da ke wakiltar Jehobah zaune a kursiyinsa. Wuta mai walkiya ta kewaye kursiyin.

Kowa yana fuskantar wani batu mai muhimmanci: Batun shi ne tsarkake sunan Allah. (Ezek. 36:23; Mat. 6:9) Da gaske ne cewa mai sunan nan Jehobah, mai tsarki ne da adalci kuma yana nuna ƙauna a dukan abubuwan da yake yi? Akwai wasu abubuwan da wannan batun ya ƙunsa. Da yake Shaiɗan ya sa mutane su ƙi sarautar Allah, wajibi ne a amsa wannan tambayar: Shin Jehobah ne ya cancanci yin sarauta kuma sarautarsa ce ta fi kyau? Ƙari ga haka, domin Adamu da Hauwa’u da ’ya’yansu da yawa da kuma wasu mala’iku sun goyi bayan Shaiɗan, wajibi ne a amsa wannan tambaya da ke da alaƙa da wanda aka yi ɗazu: Shin da akwai wasu cikin ’yan Adam da mala’iku da za su kasance da aminci, wato su kāre sunan Allah kuma su bauta masa domin suna ƙaunar sa? Littafin Ayuba ya mai da hankali ga batun kasancewa da aminci.​—Ayu. 2:​3, 4; 27:5.

4. Ta yaya Zabura 135:13 ya kwatanta sunan Allah, waɗanne tambayoyi ne za a amsa a wannan talifin?

4 Babu wani suna kamar na Jehobah. (Karanta Zabura 135:13.) Me ya sa sunan Allah yake da muhimmanci sosai? Ta yaya aka soma ɓata sunan Allah? Ta yaya aka tsarkake sunan Allah? Ta yaya za mu kāre sunan Allah? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

MUHIMMANCIN SUNA

5. Mene ne wasu za su iya cewa sa’ad da suka ji cewa wajibi ne a tsarkake sunan Allah?

5 Littafi Mai Tsarki ya ce: “A kiyaye sunanka da tsarki.” (Mat. 6:9) Yesu ya ce ya kamata tsarkake sunan Allah ya zama abu mafi muhimmanci da za mu yi addu’a a kai. Me Yesu yake nufi? A tsarkake wani abu yana nufi a sa ya kasance da tsarki ko kuma tsabta. Amma, wasu suna iya cewa, ‘Ai sunan Allah yana da tsarki da kuma tsabta!’ Muna bukatar mu yi tunani a kan abin da suna ya ƙunsa.

6. Me ya sa suna yake da muhimmanci?

6 Suna ba kalma ba ce da ake rubutawa ko furtawa kawai ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma suna mai kyau da samun dukiya.” (K. Mag. 22:1; M. Wa. 7:1) Me ya sa suna yake da muhimmanci sosai? Domin ya ƙunshi ayyuka da halaye da kuma yadda mutane suke ganin mai sunan. Don haka, yadda ake rubuta suna ko furta shi ba shi ne yake da muhimmanci ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da mutane suke tunaninsa sa’ad da suka ga an rubuta wani suna ko suka ji an furta sunan.

7. Ta yaya mutane suka ɓata sunan Allah?

7 Mutane suna ɓata sunan Allah sa’ad da suka yi ƙaryace-ƙaryace game da shi. Sa’ad da mutane suka ga munanan abubuwa suna faruwa, suna ɗora wa Jehobah laifi kuma ta hakan suna ɓata sunansa. Lokaci na farko da aka ɓata sunan Allah shi ne a lambun Adnin. Ka yi la’akari da abin da za mu iya koya daga aukuwar nan.

YADDA AKA FARA ƁATA SUNAN

8. Mene ne Adamu da Hauwa’u suka sani, waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi?

8 Adamu da Hauwa’u sun san sunan Allah kuma sun san abubuwa da yawa game da shi. Alal misali, sun san cewa shi ne Mahalicci, domin ya ba su rai da kuma wurin zama mai kyau. (Far. 1:​26-28; 2:18) Amma za su ci gaba da tunani game da dukan abubuwan da Jehobah ya yi musu ne? Shin za su ci gaba da nuna ƙauna ga Jehobah da kuma gode masa? An sami amsoshin waɗannan tambayoyin sa’ad da wani maƙiyin Allah ya jarraba Adamu da Hauwa’u.

9. Kamar yadda Farawa 2:​16, 17 da 3:​1-5 suka nuna, mene ne Jehobah ya gaya wa ma’aurata na farko, kuma ta yaya Shaiɗan ya yaudare su?

9 Karanta Farawa 2:​16, 17 da 3:​1-5. Ta yin amfani da maciji, Shaiɗan ya tambayi Hauwa’u, ya ce: “Ko Allah ya ce, lallai ba za ku ci daga kowane itacen da yake a gonar ba?” Wannan tambaya tana ɗauke da ƙarya game da Allah, kuma Hauwa’u ta soma tunanin da bai dace ba game da Allah. Ainihin umurnin da Jehobah ya ba su shi ne, su ci kowane ’ya’yan itatuwa, amma ban da ɗaya da ke gonar. Babu shakka, akwai itatuwa dabam-dabam da Adamu da Hauwa’u za su iya cin ’ya’yansu. (Far. 2:9) Jehobah karimi ne sosai. Amma, Allah ya nuna wa Adamu da Hauwa’u itacen da ba za su ci ’ya’yansa ba. Tambayar da Shaiɗan ya yi ta sa su ga kamar Allah ba karimi ba ne. Wataƙila Hauwa’u ta yi tunani cewa, ‘Allah yana hana ni wani abu mai kyau ne?’

10. Ta yaya Shaiɗan ya ɓata sunan Allah, kuma wane sakamako hakan ya jawo?

10 A lokacin, Hauwa’u tana yi wa Jehobah biyayya. Hauwa’u ta gaya wa Shaiɗan umurnin da Allah ya ba su. Ta daɗa da cewa ba za su ma taɓa itacen ba. Ta san cewa za su mutu idan suka ƙi bin umurnin Allah. Amma Shaiɗan ya ce: “Ko kaɗan, ba za ku mutu ba.” (Far. 3:​2-4) A yanzu Shaiɗan ya fito gar-da-gar, ya ɓata sunan Allah ta wajen gaya wa Hauwa’u cewa Jehobah maƙaryaci ne. Hakan ya sa Shaiɗan ya zama Iblis ko mai tsegumi. Shaiɗan ya yaudari Hauwa’u sosai domin ta yarda da ƙaryar da ya tabka. (1 Tim. 2:14) Ta dogara da shi fiye da Jehobah. Ta yin hakan, Hauwa’u ta tsai da shawarar da ta jawo mugun sakamako. Ta yanke shawarar yin rashin biyayya ga Jehobah. Sai ta soma cin ’ya’yan itacen da Jehobah ya hana su ci. Bayan haka, sai ta ba Adamu kuma shi ma ya ci ’ya’yan itacen.​—Far. 3:6.

11. Me ya kamata iyayenmu na fari su yi, amma mene ne suka kāsa yi?

11 Ka yi tunanin abin da ya kamata Hauwa’u ta gaya wa Shaiɗan. Da a ce ta gaya masa: “Ban san ka, amma na san Jehobah kuma ina ƙaunar sa, na dogara gare shi. Shi ne ya ba mu kome da muke da shi. Kada ka kuskura ka faɗi wani mugun abu game da Jehobah. Tafi ka ba ni wuri!” Da Jehobah ya yi farin cikin jin irin furucin nan daga ’yarsa da yake ƙauna! (K. Mag. 27:11) Adamu da Hauwa’u ba sa ƙaunar Jehobah, shi ya sa suka yi rashin biyayya kuma suka kāsa kāre sunansa.

12. Ta yaya Shaiɗan ya sa Hauwa’u ta soma shakkar Jehobah, kuma mene ne Adamu da Hauwa’u suka kāsa yi?

12 Kamar yadda muka gani, Shaiɗan ya soma ɓata sunan Allah ta wajen sa Hauwa’u ta yi shakka ko Jehobah Uba ne nagari. Adamu da Hauwa’u ba su kāre sunan Allah daga ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan ba. Hakan ya sa ya yi musu sauƙi su saurari Shaiɗan kuma su yi wa Jehobah tawaye. Shaiɗan yana amfani da waɗannan dabarun a yau. Yana ɓata sunan Jehobah ta wajen tabka ƙaryace-ƙaryace game da shi. Mutanen da suke amincewa da waɗannan ƙaryace-ƙaryacen suna ƙin sarautar Jehobah.

JEHOBAH YANA TSARKAKE SUNANSA

13. Ta yaya littafin Ezekiyel 36:23 ya nuna ainihin saƙon Littafi Mai Tsarki?

13 Shin Jehobah ya yi shiru ne kawai yana kallo yayin da ake ɓata sunansa? A’a! Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da Jehobah ya yi don ya wanke kansa daga ƙarairayi da aka tabka game da shi a lambun Adnin. (Far. 3:15) Hakika, ga yadda za mu iya taƙaita saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki: Jehobah ya yi amfani da Mulkinsa wajen tsarkake sunansa. Kuma Mulkin zai kawo adalci da salama a duniya. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da bayani da ya taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake tsarkake sunansa.​—Karanta Ezekiyel 36:23.

14. Ta yaya abin da Allah ya yi don tawayen da aka yi a Adnin ya tsarkake sunansa?

14 Shaiɗan ya yi iya ƙoƙarinsa don ya hana Jehobah cika nufinsa. Amma bai yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna abin da Jehobah ya yi, kuma hakan ya nuna cewa babu wani kamar Jehobah Allah. Hakika, abin da Shaiɗan da dukan magoyan bayansa suka yi ya sa Jehobah baƙin ciki sosai. (Zab. 78:40) Amma ya yi amfani da hikima da haƙuri da adalci don ya bi da wannan matsalar. Ƙari ga haka, ya nuna ikonsa a hanyoyi da yawa. Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa Jehobah yana nuna ƙauna a dukan abubuwan da yake yi. (1 Yoh. 4:8) Allah ya ci gaba da tsarkake sunansa.

Maciji ya rataye a bishiya. Hotuna: 1. Hauwa’u ta mika wa Adamu ʼya’yan itacen. 2. Wani limami yana rike da giciye da Littafi Mai Tsarki yayin da yake yin wa’azi. Akwai hoton mutane a bayansa da ke cikin wutar jahannama. 3. Wani malami yana rike da kokon kai kuma yana nuna a hoto cewa ʼyan Adam sun wanzu ne ta juyin halitta.

Shaiɗan ya yi wa Hauwa’u ƙarya game da Jehobah, kuma ya kwashe shekaru da yawa yana yin hakan (Ka duba sakin layi na 9-10, 15)c

15. Ta yaya Shaiɗan yake ɓata sunan Allah a yau, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo?

15 Har ila, Shaiɗan yana ɓata sunan Allah. Yana sa mutane shakkar cewa Allah mai iko ne da adalci da hikima da kuma ƙauna. Alal misali, Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mutane su gaskata cewa Jehobah ba Mahalicci ba ne. Kuma idan mutane suka amince da wanzuwar Allah, Shaiɗan yana sa su yi imani cewa ƙa’idodin Allah suna taƙura musu kuma ba su dace ba. Yana koya wa mutane cewa Jehobah azzalumi ne, marar tausayi da ke ƙona mutane a wutar jahannama. Sa’ad da suka gaskata da irin ƙarairayin nan, hakan yana sa su ƙi goyon bayan sarautar Jehobah. Shaiɗan zai ci gaba da ɓata sunan Allah har sai an hallaka shi. Kuma zai yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Jehobah. Zai yi nasara kuwa?

ABIN DA ZA KA YI

16. Mene ne za ka iya yi da Adamu da Hauwa’u suka kāsa yi?

16 Jehobah ya ba ’yan Adam zarafin tsarkake sunansa. Saboda haka, za ka iya yin abin da Adamu da Hauwa’u suka kāsa yi. Duk da cewa muna zama da mutanen da ke ɓata sunan Allah, muna da zarafin kāre sunan. Mu gaya musu cewa Jehobah Allah ne mai tsarki, mai adalci, mai nagarta da kuma ƙauna. (Isha. 29:23) Za ka iya goyon bayan sarautar Jehobah. Kuma ka taimaka wa mutane su fahimci cewa mulkin Allah ne kaɗai zai taimaka wa mutane su sami salama da farin ciki.​—Zab. 37:​9, 37; 146:​5, 6, 10.

17. Ta yaya Yesu ya sa a san sunan Allah?

17 Muna bin misalin Yesu Kristi sa’ad da muka kāre sunan Allah. (Yoh. 17:26) Yesu ya sanar da sunan Allah ta wajen yin amfani da sunan da kuma koya wa mutane game da shi. Alal misali, Yesu ya ƙaryata Farisawa da suke koyar da cewa Jehobah azzalumi ne marar tausayi kuma ba a iya kusantarsa. Ban da haka, Yesu ya taimaka wa mutane su san cewa Jehobah Allah ne mai sanin yakamata, mai haƙuri da ƙauna da kuma gafartawa. Ta yadda Yesu ya yi koyi da halayen Jehobah, ya taimaka wa mutane su san Jehobah sosai.​—Yoh. 14:9.

18. Mene ne za mu yi don mu fallasa ƙaryace-ƙaryace da ake yi game da Jehobah?

18 Kamar Yesu, muna iya gaya wa mutane abin da muka sani game da Jehobah. Mu koya musu cewa shi Allah ne mai ƙauna da alheri. Sa’ad da muke haka, muna fallasa ƙarairayin da ake yi game da Jehobah, muna tsarkake sunansa kuma hakan zai sa mutane su soma tsarkake sunansa. Mu ma za mu iya yin koyi da Jehobah, kuma za mu iya yin hakan duk da cewa mu ajizai ne. (Afis. 5:​1, 2) Sa’ad da muka sa mutane su san Jehobah ta ayyukanmu da furucinmu, muna tsarkake sunansa. Muna wanke sunan Jehobah, ta wajen sa mutane su sami ’yanci daga ƙaryace-ƙaryace da aka koya musu.b Ƙari ga haka, muna nuna cewa ’yan Adam ajizai suna iya kasancewa da aminci.​—Ayu. 27:5.

Wani dan’uwa yana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da wani mutum a gidansa.

Muna so mu taimaka wa ɗalibanmu su fahimci cewa Jehobah mai ƙauna ne da alheri (Ka duba sakin layi na 18-19)d

19. Ta yaya littafin Ishaya 63:7 ya nuna ainihin abin da ya kamata mu koya wa mutane?

19 Akwai wani abu kuma da za mu iya yi don mu tsarkake sunan Allah. Sa’ad da muke koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, muna yawan cewa Jehobah ne yake da ikon sarauta. Babu shakka, hakan gaskiya ne. Amma, duk da cewa yana da muhimmanci mu koya musu dokokin Allah, ainihin burinmu shi ne mu taimaka wa mutane su ƙaunaci Jehobah, kuma su kasance da aminci a gare shi. Saboda haka, muna bukatar mu riƙa gaya wa mutane game da halayen Jehobah, mu riƙa shelar halayensa. (Karanta Ishaya 63:7.) Yayin da muke hakan, za mu taimaka wa mutane su riƙa ƙaunar Jehobah da kuma yi masa biyayya don suna so su kasance da aminci a gare shi.

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Me za mu yi don halinmu da koyarwarmu su sa mutane su riƙa tunani mai kyau game da Jehobah sa’ad da suka ji sunansa kuma mu sa su kusace shi? Za a tattauna wannan tambayar a talifi na gaba.

MENE NE RA’AYINKA?

  • Ta yaya muka san cewa tsarkake sunan Jehobah yana da muhimmanci?

  • Me ya sa muke bukatar mu tsarkake sunan Allah?

  • Mene ne za mu yi don mu tsarkake sunan Jehobah?

WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka

a Wane batu mai muhimmanci ne dukan ’yan Adam da mala’iku suke fuskanta? Me ya sa wannan batun yake da muhimmanci sosai, kuma ta yaya ya shafe mu? Sanin amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah.

b A wasu lokuta, an faɗa a littattafanmu cewa bai kamata mu ce ana bukatar a wanke sunan Allah ba. Me ya sa? Domin babu wanda ya taɓa cewa Allah bai cancanci a riƙa kiransa da sunan nan Jehobah ba. Amma an yi gyara a yadda muka fahimci wannan batun a taron shekara-shekara da aka yi a 2017. Mai kujerar taron, ya ce: “Ba laifi ba ne mu yi addu’a cewa a wanke sunan Allah daga zargi ba domin ana bukatar a wanke duk zargin da Shaiɗan ya yi game da [sunan].”​—Ka duba shirin Janairu 2018 a jw.org®. Ka duba LABURARE > TASHAR JW.

c BAYANI A KAN HOTUNA: Iblis ya ɓata sunan Allah ta wajen gaya wa Hauwa’u cewa Allah maƙaryaci ne. Shekaru da yawa yanzu, Shaiɗan yana yaɗa koyarwar ƙarya cewa Allah azzalumi ne kuma shi ba Mahalicci ba ne.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Yayin da wani ɗan’uwa yake nazari da wani, yana ambata halayen Allah da zai yi koyi da su.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba