Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 1 pp. 14-15
  • Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Yin Addu’a
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 1 pp. 14-15

Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?

Da Pamela ta kamu da cutar kansa, ta je asibiti. Ban da haka, ta yi addu’a Allah ya taimaka mata ta jimre. Addu’a ta taimaka mata kuwa?

Pamela ta ce: “A lokacin da nake jinyar kansar, nakan ji tsoro sosai.” Ta kuma ce, “amma idan na yi addu’a ga Jehobah, hankalina yakan kwanta kuma nakan daina jin tsoro. Har yanzu ina fama da zafin ciwon, amma yin addu’a yana taimaka min kada in yi sanyin gwiwa. Idan mutane suka tambaye ni ya jiki, nakan ce, ‘Ina fama amma ina farin ciki.’ ”

Ba sai mun jira muna bakin mutuwa kafin mu yi addu’a ba. Dukanmu muna fuskantar matsaloli iri-iri kuma muna bukatar taimako don mu jimre. Kana ganin addu’a za ta iya taimakawa?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Danƙa wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai, ko kaɗan ba zai bar masu adalci su jijjigu ba.” (Zabura 55:22) Hakika, wannan alkawari mai ban ƙarfafa ne! Ta yaya addu’a za ta taimaka maka? Idan ka yi addu’a a hanyar da ta dace, Allah zai taimaka maka da matsalolinka.​—Don ƙarin bayani, ka dubi akwatin nan, “Me Za Ka Samu Idan Ka Yi Addu’a?”

Me Za Ka Samu Idan Ka Yi Addu’a?

Kwanciyar hankali

Mutumin da aka kore shi daga aiki, yana tafiya hankalinsa kwance kuma yana murmushi.

‘Ku faɗa wa Allah bukatunku. Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.’ (Filibiyawa 4:​6, 7) Idan ka gaya wa Allah abin da yake damunka, zai taimaka maka ka kasance da kwanciyar hankali kuma ka yi abin da ya dace.

Hikima daga Allah

Matar da dazu take karanta addu’a daga wani littafi, tana karanta Littafi Mai Tsarki a gidanta.

“In waninku yana bukatar hikima, sai ya roƙi Allah wanda yake ba kowa hannu sake ba tare da gori ba, zai kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) A yawancin lokuta, ba ma iya yanke shawarar da ta dace sa’ad da muke cikin matsala. Idan ka roƙi Allah ya ba ka hikima, zai taimaka maka ka tuna da wasu ƙa’idodi daga Kalmarsa da za su taimaka maka.

Ƙarfin jimrewa

Ma’auratan da suke asibiti dazu sun fita shan iska a wani lambu. Maigidan yana taimaka wa matar ta jingina da kyau a kan sandar tafiya.

“Ikon da ya fi duka daga wurin Allah ne.” (2 Korintiyawa 4:7) Da yake Jehobah shi ne Allah mafi iko, zai iya ba ka ƙarfin magance matsalolin da kake fuskanta ko kuma ya taimaka maka ka jimre matsalolin. (Ishaya 40:29) Littafi Mai Tsarki ya kira Jehobah, “Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya!” Zai “yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalarmu.”​—2 Korintiyawa 1:​3, 4.

ZA KA YI ADDU’A?

Jehobah ba zai tilasta maka ka yi addu’a ba. Maimakon haka, ya ba ka damar yin addu’a don yana ƙaunar ka. (Irmiya 29:​11, 12) Amma idan ka taɓa yin addu’a a dā kuma kana ganin Allah bai amsa ba fa? Kada ka yi baƙin ciki ko ka fid da rai. Ba a kowane lokaci ne iyayen kirki za su biya bukatar yaransu yadda yaran suke so ba. Mai yiwuwa iyayen suna da wata hanya da ta fi dacewa da za su yi hakan. Amma ko da wane mataki ne suka ɗauka, iyayen kirki suna taimaka wa yaransu.

Haka ma Jehobah, Ubanmu mai ƙauna, yana so ya taimaka maka. Idan ka yi tunani sosai a kan abubuwan da muka tattauna a mujallar nan kuma ka bi shawarwarin, Allah zai amsa addu’arka a lokacin da ya dace.​—Zabura 34:15; Matiyu 7:​7-11.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba