Shin, Allah Yana Jin Addu’arka?
Kana ganin Allah yana jin ka a duk lokacin da ka yi addu’a kuwa?
MENE NE LITTAFI MAI TSARKI YA CE?
- Allah yana ji. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa “Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi, ga waɗanda suke kira gare shi cikin gaskiya. . . . Yakan kuma ji kukansu.”—Zabura 145:18, 19. 
- Allah yana so ka yi addu’a. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “A cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.”—Filibiyawa 4:6. 
- Allah ya damu da kai sosai. Allah yana sane da matsalolin da suke damun ka kuma yana so ya taimake ka. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ka danƙa masa dukan damuwarka,’ domin ‘shi ne mai lura da kai.’—1 Bitrus 5:7.