Gabatarwa
Shin abubuwan da suke faruwa yanzu suna nuna cewa duniya ta kusan ƙarewa ne? Idan haka ne, me ya kamata mu yi don mu tsira wa ƙarshen duniya? Me zai faru bayan ƙarshen duniya ya zo? Za mu ga amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar a wannan mujallar.