TALIFIN NAZARI NA 7
‘Ka Kasa Kunne Ka Ji Kalmomin Masu Hikima’
‘Kasa kunne ka ji kalmomin masu hikima, yi nazarin koyarwata a zuciyarka.’—K. MAG. 22:17.
WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta waɗanne hanyoyi ne muke samun gargaɗi, kuma me ya sa muke bukatar sa?
DUKANMU muna bukatar gargaɗi a wasu lokuta. Mu da kanmu za mu iya neman shawarar wasu. A wasu lokuta kuma, wani ɗan’uwa zai iya lura cewa muna so mu yi wani abin da “zai kai mu ga yin laifi,” sai ya gargaɗe mu. (Gal. 6:1, New World Translation) Ban da haka, za a iya yi mana gyara bayan mun yi kuskure mai tsanani. Ko ta wace hanya ce aka yi mana gargaɗi ko aka ba mu shawara, zai dace mu saurara. Idan mun yi hakan, za mu amfana kuma zai ceci ranmu.—K. Mag. 6:23.
2. Bisa ga Karin Magana 12:15, me ya sa ya dace mu riƙa bin gargaɗi?
2 Nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin ya ƙarfafa mu cewa mu ‘kasa kunne mu ji kalmomin masu hikima.’ (K. Mag. 22:17) Babu ɗan Adam da ya san kome da kome. Wasu sun fi mu ilimi da kuma ƙwarewa. (Karanta Karin Magana 12:15.) Don haka, bin gargaɗi zai nuna cewa mu masu sauƙin kai ne. Hakan zai nuna cewa mun san kasawarmu, kuma mun san muna bukatar taimakon wasu don mu iya cim ma maƙasudanmu. An hure Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: “Tare da shawara mai yawa, akwai cin nasara.”—K. Mag. 15:22.
Wanne daga cikin biyun nan ya fi maka wuyan karɓa? (Ka duba sakin layi na 3-4)
3. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya samun gargaɗi?
3 Hanya ɗaya da muke samun gargaɗi ita ce ta karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafanmu. Yayin da muke yin hakan, za mu iya samun abin da zai taimaka mana mu yi gyara a rayuwarmu. (Ibran. 4:12) Amma akwai wata hanya kuma da za mu iya samun gargaɗi. Alal misali, wani ɗan’uwa da ya manyanta zai iya gaya mana inda muke bukatar mu yi gyara a rayuwarmu. Idan ƙauna ta sa wani ya yi mana gargaɗi, zai dace mu nuna godiya ta saurararsa da kuma bin gargaɗin.
4. Bisa ga Mai-Wa’azi 7:9, mene ne bai kamata mu yi ba idan aka yi mana gargaɗi?
4 A gaskiya, zai iya mana wuya mu ji gargaɗin da wani ya yi mana. Za mu ma iya yin fushi. Me ya sa? Ko da yake mukan yarda cewa mu ajizai ne, zai iya mana wuya mu ji gargaɗi idan wani ya gaya mana inda muke bukatar mu yi gyara. (Karanta Mai-Wa’azi 7:9.) Za mu iya ba da hujjoji, ko mu ce mutumin yana da mummunan nufi ko kuma mu yi fushi domin yadda ya ba mu gargaɗin. Za mu ma iya cewa: ‘Bai isa ya yi mini gargaɗi ba. Ai shi ma yana da nasa kasawa!’ Kuma idan ba ma so a gaya mana gaskiya, za mu iya yin watsi da gargaɗin, ko mu nemi wani da zai gaya mana abin da muke so mu ji.
5. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
5 A wannan talifin, za mu tattauna misalai a Littafi Mai Tsarki na mutanen da suka karɓi gargaɗi da waɗanda ba su yi hakan ba. Za mu kuma tattauna abin da zai taimaka mana mu karɓi gargaɗi don mu amfana.
SUN ƘI GARGAƊI DA AKA YI MUSU
6. Wane darasi ne muka koya daga abin da Rehobowam ya yi bayan an ba shi shawara?
6 Ka yi la’akari da misalin Rehobowam. Sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, talakawansa sun roƙe shi cewa ya sauƙaƙa musu kaya mai nauyi da babansa Sulemanu ya ɗora musu. Rehobowam ya yi abin da ya dace sa’ad da ya tuntuɓi dattawan Isra’ila don ya san matakin da zai ɗauka. Dattawan sun gaya masa cewa idan ya biya bukatun mutanen, mutanen za su ci gaba da goyon bayansa. (1 Sar. 12:3-7) Amma da alama Rehobowam bai ji daɗin shawarar ba. Sai ya nemi shawarar mazan da suka yi girma tare. Da alama mutanen suna da shekara 40 da ’yan kai. Hakan yana nufin cewa suna da ɗan ƙwarewa. (2 Tar. 12:13) Amma a wannan karon sun ba shi shawara marar kyau. Sun gaya masa cewa ya ƙara wa mutanen nauyin kayan. (1 Sar. 12:8-11) Da yake an ba shi shawarwari biyu, ya kamata Rehobowam ya yi addu’a ga Jehobah, kuma ya tambaye shi wace shawara ce ya kamata ya bi daga cikin biyun. A maimakon haka, sai ya bi shawarar da zuciyarsa ta fi so, wato shawarar tsararsa. Hakan ya jawo sakamako marar kyau ga Rehobowam da dukan al’ummar Isra’ila. Ba a kowane lokaci ne za a iya ba mu shawarar da muke so mu ji ba. Amma idan shawarar ta jitu da Kalmar Allah, zai dace mu bi ta.
7. Wane darasi ne muka koya daga abin da ya faru da Sarki Uzziya?
7 Sarki Uzziya ya ƙi gargaɗi. Ya shiga wani sashe na haikalin Jehobah inda firistoci ne kaɗai ke da izinin shiga, kuma ya yi ƙoƙarin miƙa turaren ƙonawa. Firistocin Jehobah sun ce masa: “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙona turare ga Yahweh. Wannan aikin firist ne!” Mene ne Uzziya ya yi? Da a ce ya ji gargaɗin da aka yi masa kuma ya bar haikalin ba tare da ɓata lokaci ba, da Jehobah ya gafarta masa. A maimakon haka, “Uzziya ya yi fushi.” Me ya sa ya ƙi gargaɗin? Da alama yana ganin cewa da yake shi sarki ne, yana da izinin yin duk wani abin da ya ga dama. Da yake ya yi abin da bai da izinin yi, Jehobah ya buge shi da kuturta, kuma Uzziya ya zama kuturu har mutuwarsa. (2 Tar. 26:16-21) Abin da ya faru da Uzziya ya koya mana cewa ko da wane irin matsayi ne muke da shi, idan mun ƙi bin gargaɗin da ke Littafi Mai Tsarki, za mu rasa amincewar Jehobah.
SUN KARƁI SHAWARA
8. Mene ne Ayuba ya yi sa’ad da aka yi masa gargaɗi?
8 Akasin misalan mutane biyun da muka riga muka tattauna, Littafi Mai Tsarki ya ba da labaran mutane da aka yi musu albarka domin sun bi gargaɗin da aka yi musu. Ka yi la’akari da misalin Ayuba. Ko da yake shi mai tsoron Allah ne, shi ba kamili ba ne. Sa’ad da aka jarraba shi, ya faɗi wasu abubuwa da ba daidai ba. Saboda haka, Jehobah da kuma Elihu sun yi masa gargaɗi. Mene ne Ayuba ya yi? Ya nuna sauƙin kai kuma ya karɓi gargaɗin. Ya ce: “Na faɗa abin da ban gane ba. . . . Domin wannan ina ƙyamar kaina, na tuba tare da zuba kura da toka a kaina.” Jehobah ya yi ma Ayuba albarka domin ya nuna sauƙin kai.—Ayu. 42:3-6, 12-17.
9. Ta yaya Musa ya kafa misali mai kyau na bin gargaɗi?
9 Musa ma ya kafa mana misali mai kyau domin ya ji gargaɗin da aka yi masa bayan ya yi kuskure. Akwai lokacin da aka ɓata masa rai, kuma hakan ya sa bai ɗaukaka Allah ba. Don haka, Jehobah ya hana shi shiga Ƙasar Alkawari. (L. Ƙid. 20:1-13) Sa’ad da Musa ya roƙi Jehobah ya canja matakin da ya ɗauka, sai Jehobah ya gaya masa cewa: “Kada ka ƙara yin roƙo a kan wannan zance.” (M. Sha. 3:23-27) Musa bai yi fushi saboda hakan ba. Amma ya amince da matakin da Jehobah ya ɗauka, kuma Jehobah ya ci gaba da amfani da shi ya ja-goranci al’ummar Isra’ila. (M. Sha. 4:1) Musa da Ayuba sun kafa mana misali mai kyau na yadda za mu riƙa karɓan gargaɗi. Ayuba ya karɓi gyara kuma bai ba da hujjoji ba. Musa ya nuna cewa ya karɓi gyara ta wajen riƙe amincinsa har bayan da aka hana shi shiga Ƙasar Alkawari.
10. (a) Mene ne Karin Magana 4:10-13 suka faɗa game da amfanin jin gargaɗi? (b) Mene ne wasu ’yan’uwa suka yi sa’ad da aka yi musu gargaɗi?
10 Za mu amfana idan muka bi misali mai kyau da bayin Allah kamar Ayuba da Musa suka kafa. (Karanta Karin Magana 4:10-13.) ’Yan’uwanmu masu bi da yawa sun yi hakan. Ka yi la’akari da abin da wani ɗan’uwa mai suna Emmanuel da yake zama a ƙasar Kwango ya faɗa game da wani gargaɗin da aka yi masa, ya ce: “’Yan’uwa da suka manyanta a cikin ikilisiya sun lura cewa ina gab da yin wani abin da zai ɓata dangantakata da Jehobah, kuma sun taimaka mini. Na karɓi gargaɗin kuma hakan ya sa na guje wa matsaloli da yawa.”b Ga abin da wata majagaba mai suna Megan da take ƙasar Kanada ta faɗa game da gargaɗi: “Gargaɗi ba abin da nake so in ji ba ne, amma abin da ya kamata a gaya min ne.” Wani ɗan’uwa kuma mai suna Marko daga ƙasar Kuroshiya, ya ce: “An dakatar da ni daga yin wasu ayyuka a cikin ikilisiya. Amma yanzu idan na tuna da abin da ya faru, nakan gaya wa kaina cewa gyarar da aka yi mini ya taimaka mini in kyautata dangantakata da Jehobah.”
11. Mene ne Ɗan’uwa Karl Klein ya faɗa game da jin gargaɗi?
11 Wani mutum kuma da ya amfana daga jin gargaɗi shi ne Ɗan’uwa Karl Klein, wanda ya yi hidima a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. A labarin da ya rubuta game da kansa, Ɗan’uwa Klein ya faɗi yadda Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya yi masa gargaɗi. Su abokai ne sosai a lokacin. Ɗan’uwa Klein ya ce da farko ya yi fushi don gargaɗin da Ɗan’uwa Rutherford ya yi masa. Ya ce: “Bayan haka, da Ɗan’uwa Rutherford ya gan ni, sai ya ce, ‘Karl ya ne?’ Amma da yake ina kan fushi, ban buɗe baki na amsa masa da kyau ba. Sai ya ce, ‘Karl, ka yi hankali, Iblis yana so ya sa maka tarko!’ Hakan ya sa ni kunya, sai na ce, ‘Haba Ɗan’uwa Rutherford, ba na fushi.’ Amma ya san cewa ina fushi da shi har ila. Sai ya ce, ‘Shi ke nan, amma ka yi hankali. Iblis yana so ya ɗana maka tarko.’ Abin da ya faɗa gaskiya ne! Idan muka riƙe ɗan’uwanmu a zuciya don ya gaya mana abin da ya kamata ya gaya mana, hakan zai iya sa mu faɗa a tarkon Iblis.”c (Afis. 4:25-27) Ɗan’uwa Klein ya bi gargaɗin da Ɗan’wa Rutherford ya yi masa, kuma sun ci gaba da zama abokai.
ME ZAI TAIMAKA MANA MU JI GARGAƊI?
12. Bisa ga Zabura 141:5, a wace hanya ce sauƙin kai zai taimaka mana mu karɓi gargaɗi?
12 Me zai taimaka mana mu ji gargaɗi? Muna bukatar mu zama masu sauƙin kai. Mu tuna cewa mu ajizai ne kuma za mu iya yin abin da ba daidai ba a wasu lokuta. Kamar yadda muka tattauna ɗazu, Ayuba ya yi tunanin da bai dace ba. Amma daga baya ya canja ra’ayinsa kuma Jehobah ya yi masa albarka saboda hakan. Me ya sa? Domin Ayuba ya nuna sauƙin kai. Ya yi hakan ta wajen jin gargaɗin Elihu duk da cewa ya girme Elihu sosai. (Ayu. 32:6, 7) Sauƙin kai zai taimaka mana mu ji gargaɗi ko da mun ɗauka cewa bai kamata a yi mana gargaɗin ba ko kuma mun girme wanda ya yi mana gargaɗin. Wani dattijo a Kanada ya ce, “Da yake ba za mu iya sanin halinmu da kyau ba, sai wasu sun gaya mana ne za mu iya samun ci gaba.” Wane ne a cikin mu ba ya so ya daɗa kasancewa da halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa, da kuma ƙwarewa a yin wa’azi da koyarwa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan mutum mai adalci ya buge ni, ƙauna marar canjawa ce. Idan ya gargaɗe ni, zai zama kamar māi a kaina, wanda kaina ba zai ƙi ba. Zan ci gaba da yi musu addu’a har a lokacin da suke cikin wahala.”—Zabura 141:5, NWT.
13. Yaya ya kamata mu ɗauki gargaɗi da ake mana?
13 Ka ɗauki gargaɗi a matsayin hanya da Jehobah yake nuna maka ƙauna. Jehobah yana so mu yi nasara. (K. Mag. 4:20-22) Shi ya sa a duk lokacin da ya yi mana gargaɗi ta wurin Kalmarsa, ko littattafanmu, ko kuma ɗan’uwa da ya manyanta, yana nuna mana ne cewa yana ƙaunarmu. Ibraniyawa 12:9, 10 sun ce yana yi mana hakan “saboda amfaninmu ne.”
14. Me ya kamata mu mai da hankali a kai idan aka yi mana gargaɗi?
14 Ka mai da hankali ga gargaɗi da aka yi maka, ba yadda aka ba da gargaɗin ba. A wasu lokuta, za mu iya ji kamar ba a ba mu gargaɗi a hanyar da ta dace ba. A gaskiya, yana da muhimmanci wanda yake ba da gargaɗi ya yi hakan a hanyar da za ta yi sauƙi ma wanda yake ji ya karɓa.d (Gal. 6:1) Amma idan mu ne ake yi wa gargaɗi, zai dace mu mai da hankali ga gargaɗin ko da muna ganin kamar ba a ba mu gargaɗin a hanyar da ta dace ba. Za mu iya tambayar kanmu: ‘Ko da yake ban ji daɗin yadda aka ba ni gargaɗin ba, abin da aka gaya min gaskiya ne? Zan iya mai da hankali a kan gargaɗin maimakon wanda ya ba da gargaɗin?’ Za mu amfana idan mun yi iya ƙoƙarinmu mu bi gargaɗi.—K. Mag. 15:31.
KA NEMI SHAWARA DON KA AMFANA
15. Me ya sa ya dace mu nemi shawara?
15 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu nemi shawara. Karin Magana 13:10 ta ce: “Hikima tana wurin mai neman shawara.” Wannan maganar gaskiya ce! Waɗanda suke neman shawara da kansu maimakon su jira har sai wani ya zo ya gargaɗe su, za su sami ci gaba fiye da waɗanda ba sa neman shawara. Don haka, ka nemi shawara daga wasu.
Me ya sa ’yar’uwa matashiyar ta nemi shawarar ’yar’uwa da ta manyanta? (Ka duba sakin layi na 16)
16. A waɗanne yanayi ne za mu iya neman shawara?
16 A wane lokaci ne za mu iya neman shawara daga wurin ’yan’uwanmu? Ka yi la’akari da yanayoyin da za mu iya yin hakan. (1) Wata ’yar’uwa za ta iya gaya ma mai shela da ya ƙware ya bi ta nazari da ɗalibinta, kuma bayan nazarin, za ta iya tambayar sa yadda za ta inganta koyarwarta. (2) Wata ’yar’uwa matashiya da take so ta sayi kayan sakawa, za ta iya neman shawarar ’yar’uwa da ta manyanta don ta gaya mata ko kayan ya dace. (3) Wani ɗan’uwa da aka ba shi jawabi na farko, zai iya gaya ma ɗan’uwa da ya manyanta ya saurari yadda zai ba da jawabin kuma ya ba shi shawara a kan yadda zai inganta yadda yake ba da jawabi. Ɗan’uwa da ya yi shekaru da yawa yana ba da jawabi ma zai iya gaya ma ɗan’uwa da ya ƙware ya saurari yadda yake ba da jawabi, don ya ba shi shawara. Sa’an nan ya yi amfani da shawarar.
17. A wace hanya ce za mu amfana daga gargaɗi?
17 A kwana a tashi, Jehobah zai yi mana gargaɗi ta wurin Kalmarsa ko kuma ta wurin ’yan’uwanmu. Idan hakan ya faru, ka tuna da abubuwan da muka tattauna a talifin nan. Ka nuna sauƙin kai, ka mai da hankali ga gargaɗin, ba yadda aka ba ka gargaɗin ba. Ba waninmu da aka haife shi da hikima. Amma idan muka ‘kasa kunne ga shawara, muka karɓi koyarwa,’ Kalmar Allah ta yi mana alkawari cewa, za mu ‘zama masu hikima.’—K. Mag. 19:20.
WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci
a Bayin Jehobah sun san cewa yana da muhimmanci su bi gargaɗi da aka yi musu daga Littafi Mai Tsarki. Amma ba a kullum ne yake yi mana sauƙi mu bi gargaɗi da aka yi mana ba. Me ya sa? Mene ne zai taimaka mana mu amfana daga gargaɗin da aka yi mana?
b An canja wasu sunayen.
d A talifi na gaba, za mu tattauna yadda waɗanda suke ba da gargaɗi za su yi hakan da hikima.