Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w22 Yuli pp. 2-7
  • Yesu Kristi Ya Soma Mulki!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Kristi Ya Soma Mulki!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA MU SAN LOKACIN DA AKA KAFA MULKIN ALLAH
  • YADDA MUKA SAN CEWA KRISTI YA ZAMA SARKIN MULKIN ALLAH
  • YADDA ZA A HALAKA MAƘIYAN MULKIN ALLAH
  • KU BA DA GASKIYA CEWA JEHOBAH ZAI KĀRE MUTANENSA A NAN GABA
  • Ka Koyi Darussa Daga Annabcin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Mai Da Hankali Ga Kalmomin Annabci Na Allah Don Kwanakinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
w22 Yuli pp. 2-7

TALIFIN NAZARI NA 28

Yesu Kristi Ya Soma Mulki!

“Ikon mulki a kan duniya yanzu ya zama na Ubangijinmu da Almasihunsa.”​—R. YAR. 11:15.

WAƘA TA 22 Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Wane tabbaci ne muke da shi, kuma me ya sa?

SA’AD DA ka ga abubuwan da ke faruwa a duniya, kana ganin yanayin duniya zai gyaru ne? Iyalai ba sa nuna wa juna ƙauna. Mutane suna daɗa son kai da kuma mugunta. Mutane da yawa ba sa yarda da hukumomi. Amma abubuwan nan za su iya tabbatar maka cewa yanayin duniya zai gyaru. Me ya sa? Domin mutane suna nuna halayen da Littafi Mai Tsarki ya ce za su nuna a “kwanakin ƙarshe.” (2 Tim. 3:​1-5) Duk wani mai son gaskiya ba zai yi mūsun cikar annabcin nan ba. Kuma cikar annabcin ya tabbatar mana cewa Yesu Kristi ya soma sarauta a sama. Amma wannan ɗaya ne kawai daga cikin annabce-annabcen da Littafi Mai Tsarki ya yi game da Mulkin Allah. Bincika wasu annabce-annabce da suka cika a ’yan shekarun nan zai ƙarfafa bangaskiyarmu.

Wani yana saka sashen karshe na wasan daurin gwarmai. Sashen yana dauke da hoton wani dutse da ya bugi siffa na karfe. Sassan wasan daurin gwarman suna kwatanta annabce-annabcen da ke littafin Daniyel da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. 1. Wani dutse da ya sauko daga kan tudu ya bugi tafin kafar wani siffa na karfe. 2. Wata babbar bishiya. 3. Dawakai guda hudu suna gudu da mahaya a kansu. 4. Wata karuwa tana zaune a kan wata dabba mai jar kala.

Kamar yadda ake harhaɗa ƙananan abubuwa don a sami katon abu guda daya, haka ma idan muka haɗa annabce-annabcen da ke littafin Daniyel da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, za mu gane cewa ƙarshe ya kusa kamar yadda Jehobah ya yi mana alkawari. (Ka duba sakin layi na 2)

2. Mene ne za mu tauttana a wannan talifin, kuma me ya sa? (Ka yi kalami a kan hoton da ke shafin farko.)

2 A wannan talifin, za mu tattauna (1) annabcin da ya taimaka mana mu san lokacin da aka kafa Mulkin Allah, (2) annabce-annabcen da suka taimaka mana mu san cewa Yesu ya zama sarki a sama, (3) annabce-annabcen da suka nuna yadda za a halaka maƙiyan Mulkin. Kamar yadda tela yake amfani da yadi dabam-dabam don ya ɗinka riga, za mu ga yadda waɗannan annabce-annabcen suka haɗu suka zama ɗaya don su nuna mana cewa ƙarshe ya kusa ya zo kamar yadda Jehobah ya yi mana alkawari.

YADDA ZA MU SAN LOKACIN DA AKA KAFA MULKIN ALLAH

3. Wane tabbaci ne annabcin da ke Daniyel 7:​13, 14 ya ba mu game da Sarkin Mulkin Allah?

3 Annabcin da ke Daniyel 7:​13, 14 ya tabbatar mana cewa Yesu Kristi ne ya cancanci ya yi sarauta a Mulkin Allah. Mutane daga dukan al’ummai za su bauta masa kuma babu wanda zai gāje shi a matsayin sarki. Wani annabci kuma a littafin Daniyel ya nuna cewa Yesu zai zama sarki bayan lokaci bakwai a alamance. Shin zai yiwu mu san lokacin da Yesu ya zama sarki?

4. Ka bayyana yadda Daniyel 4:​10-17 suka taimaka mana mu san shekarar da aka naɗa Yesu sarki. (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

4 Karanta Daniyel 4:​10-17. “Lokaci bakwai” da aka ambata a annabcin yana wakiltar tsawon lokaci da ya kai shekaru 2,520. Lokacin ya soma ne a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu sa’ad da mutanen Babila suka cire sarki na ƙarshe daga kursiyin Jehobah a Urushalima. Kuma ya ƙare a shekara ta 1914 sa’ad da Jehobah ya naɗa Yesu a matsayin sarki. Yesu ne yake da “hakkin” zama sarki.b​—Ezek. 21:​25-27.

5. A wace hanya ce za mu amfana daga annabcin da aka yi game da “lokaci bakwai”?

5 Ta yaya za mu amfana daga annabcin nan? Sanin ma’anar annabcin da aka yi game da “lokaci bakwai” yana tabbatar mana cewa Jehobah zai cika alkawarunsa a kan lokaci. Kamar yadda ya cika alkawarin da ya yi na naɗa Yesu sarki, mun san cewa Jehobah zai cika sauran alkawuran da ya yi a daidai lokacin da ya tsara. Hakika, ranar Jehobah “ba za ta yi latti ba!”​—Hab. 2:3.

YADDA MUKA SAN CEWA KRISTI YA ZAMA SARKIN MULKIN ALLAH

6. (a) Waɗanne abubuwa ne suke faruwa da suka nuna cewa Yesu ya soma sarauta? (b) Ta yaya suka tabbatar da annabcin da aka yi a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​2-8?

6 Sa’ad da Yesu ya kusan kammala hidimarsa a nan duniya, ya annabta wasu abubuwan da za su faru da za su taimaka wa mabiyansa su san cewa ya soma sarauta a sama. Ya annabta cewa za a yi yaƙi da yunwa da kuma girgizar ƙasa. Ƙari ga haka, ya annabta cewa za a yi cututtuka “a wurare dabam-dabam.” Kuma misalin hakan shi ne annobar korona. Waɗannan abubuwa da suke faruwa su ne “alamar” zuwan Kristi. (Mat. 24:​3, 7; Luk. 21:​7, 10, 11) Fiye da shekaru 60 bayan mutuwarsa da komawarsa sama, Yesu ya ƙara tabbatar wa Yohanna cewa abubuwan nan za su faru. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​2-8.) Tun daga lokacin da Yesu ya soma sarauta a shekara ta 1914 waɗannan abubuwan sun soma faruwa.

7. Me ya sa aka soma samun matsaloli da yawa tun Yesu ya zama sarki?

7 Me ya sa yanayin duniya ya ƙara lalacewa sa’ad da Yesu ya zama Sarki? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:2 ta yi bayani mai muhimmanci. Abu na farko da Yesu ya yi sa’ad da ya zama sarki shi ne yaƙi. Da waye ke nan? Da Iblis da kuma aljanunsa. Abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 12, ya nuna cewa Shaiɗan bai yi nasara ba, kuma aka kore shi da aljanunsa zuwa nan duniya. Hakan ya jawo wa dukan ’yan Adam matsaloli domin Shaiɗan yana cike da fushi.​—R. Yar. 12:​7-12.

Mata da miji suna kallon hoton tashin hankali da ake nunawa a talabijin. Akwai Littafi Mai Tsarki da wasu littattafanmu a kan teburi da ke gabansu.

Ba ma farin ciki idan muka ji labarai marasa daɗi, amma ganin yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika suna tabbatar mana cewa Yesu ya soma sarauta (Ka duba sakin layi na 8)

8. Ta yaya za mu amfana yayin da muke ganin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika?

8 Ta yaya za mu amfana daga waɗannan annabce-annabcen? Abubuwan da ke faruwa a duniya da kuma yadda halayen mutane suke canjawa za su taimaka mana mu san cewa Yesu ya zama Sarki. Saboda haka, maimakon mu ɓata rai sa’ad da muka ga mutane suna nuna son kai da mugunta, ya kamata mu tuna cewa abubuwan da suke yi yana cika annabcin Littafi Mai Tsarki domin Yesu ya soma sarauta! (Zab. 37:1) Kuma yayin da Armageddon yake daɗa kusa, yanayin duniya zai ƙara lalacewa. (Mar. 13:8; 2 Tim. 3:13) Muna godiya ga Ubanmu mai ƙauna wanda ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa matsaloli suka yi yawa a duniya.

YADDA ZA A HALAKA MAƘIYAN MULKIN ALLAH

9. Ta yaya annabcin da ke Daniyel 2:​28, 31-35 ya kwatanta gwamnati ta ƙarshe mafi iko a duniya, kuma a yaushe gwamnatin ta bayyana?

9 Karanta Daniyel 2:​28, 31-35. A yau ma, muna ganin cikar wannan annabcin. Mafarkin Nebuchadnezzar ya nuna “abin da zai faru nan gaba,” wato a kwanakin ƙarshe bayan da Kristi ya soma sarauta. Maƙiyan Yesu a duniya za su ƙunshi gwamnati ta ƙarshe mafi iko a nan duniya da aka annabta a cikin Littafi Mai Tsarki. Gwamnatin tana wakiltar tafin ƙafa da aka yi da “baƙin ƙarfe gauraye da laka.” Wannan gwamnatin ta riga ta bayyana. Ta bayyana a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya sa’ad da ƙasar Birtaniya da Amirka suka ƙulla ƙawance ta musamman. Mafarkin da Nebuchadnezzar ya yi ya annabta aƙalla abubuwa guda biyu game da wannan gwamnatin da za su bambanta shi da sauran gwamnatocin da suka wuce.

10. (a) Mene ne Daniyel ya annabta game da gwamnatin haɗin gwiwa ta Birtaniya da Amirka da muke gani a yau? (b) Wane abu ne ya kamata mu guje wa? (Ka duba akwatin nan “Kana Ganin Haɗarin?”)

10 Na farko, gwamnatin haɗin gwiwa ta Birtaniya da Amirka tana wakiltar baƙin ƙarfe da aka gauraye da laka, ba kamar sauran gwamnatocin da suka wuce da aka wakilce su da zallar ƙarfe kamar zinariya da azurfa ba. Lakar tana wakiltar “zuriyar mutane” ko kuma ’yan Adam. (Dan. 2:​43, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Kamar yadda ake gani a yau, suna amfani da zaɓe da gangamin ƙungiyoyin fararen hula, da ƙungiyoyin ƙwadago don su hana wannan gwamnatin yin wasu abubuwan da take so ta yi.

Kana Ganin Haɗarin?

Kafar karfe da kuma laka da ke jikin babban siffar da Daniyel ya gani a cikin wahayi. A daidai wurin kafafun mutane suna zanga-zanga, jami’an tsaro suna rike da abin kariya, shugabannin duniya suna yin taro, membobin Majalisar Dinkin Duniya suna taron koli.

A annabcin Daniyel, lakar da ke tafin ƙafafun babbar siffar tana wakiltar mutane. Suna iya yin tasiri a kan ’yan siyasa da kuma yadda suke mulki. (Dan. 2:​41-43, THS) Shin hakan zai iya shafan mu ne? E! Idan ba mu kāre zuciyarmu ba, za mu iya soma sa hannu a harkokin siyasa. Alal misali, za mu iya soma goyon bayan waɗanda suke so a yi canji ta wajen zanga-zanga da ƙungiyoyin siyasa. (K. Mag. 4:23; 24:21) Ta yaya za mu guje ma hakan? Ya kamata mu tuna cewa Shaiɗan ne yake mulkin duniya. (1 Yoh. 5:19) Kuma Mulkin Allah ne kaɗai zai cire wahalolinmu.​—Zab. 146:​3-5.

11. Ta yaya gwamnatin haɗin gwiwar Birtaniya da Amirka suka tabbatar mana cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe?

11 Na biyu, da yake gwamnatin Birtaniya da Amirka ne suke wakiltar tafin ƙafafun babban siffar da Daniyel ya gani, su ne gwamnati na ƙarshe mafi iko da aka annabta a Littafi Mai Tsarki. Bayan su, ba za a sami wata gwamnatin ’yan Adam kuma ba. Amma Mulkin Allah zai kawar da su da sauran gwamnatocin ’yan Adam a yaƙin Armageddon.c​—R. Yar. 16:​13, 14, 16; 19:​19, 20.

12. Ta yaya za mu amfana daga annabcin Daniyel game da babbar siffa na mafarkin Nebuchadnezzar?

12 Ta yaya wannan annabcin zai amfane mu? Annabcin Daniyel ya ƙara ba mu tabbaci cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Fiye da shekaru 2,500 da suka shige, Daniyel ya annabta cewa bayan Babila, za a sami ƙasashe huɗu mafi iko a duniya da za su yi mulki ɗaya bayan ɗaya, kuma mulkinsu zai shafi mutanen Allah. Ƙari ga haka, ya bayyana cewa gwamnatin haɗin gwiwar Birtaniya da Amirka ce za ta zama ta ƙarshe. Wannan bayanin ya ƙarfafa mu kuma ya ba mu bege cewa nan ba da jimawa ba, Mulkin Allah zai kawar da dukan gwamnatocin ’yan Adam kuma ya yi iko a kan duniya gabaki ɗaya.​—Dan. 2:44.

13. Mene ne sarki na “takwas” da “sarakuna goma” da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​9-12 suke wakilta, kuma ta yaya annabcin nan yake cika a yau?

13 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​9-12. Abubuwan da suka faru a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya sun sa wani annabcin da aka yi game da kwanakin ƙarshe ya cika. Shugabannin ƙasashen duniya sun so a sami zaman lafiya a duniya. Saboda haka, a Janairu 1920, sun kafa Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya. Daga baya, a Oktoba 1945, suka maye gurbinta da Majalisar Ɗinkin Duniya. Littafi Mai Tsarki ya kira ƙungiyar nan sarki na “takwas.” Amma ita ba gwamnati mafi iko a duniya ba ce. Gwamnatoci da suke taimaka mata ne suke ba ta iko da take da shi. Littafi Mai Tsarki ya kira waɗannan gwamnatocin “sarakuna goma.”

14-15. (a) Mene ne Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​3-5 suka bayyana game da Babila Babba? (b) Mene ne yake faruwa da mabiyan addinan ƙarya?

14 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​3-5. A cikin wahayin da Allah ya nuna masa, manzo Yohanna ya ga wata karuwa wato “Babila Mai Girma” ko kuma Babila Babba, wadda take wakiltar daular addinin ƙarya. Ta yaya wahayin nan yake cika? Tun da daɗewa, addinan ƙarya suna cuɗanya da gwamnatocin duniya kuma suna goyon bayan su. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai sa waɗannan gwamnatocin su “aikata nufinsa.” Wane sakamako ne hakan zai jawo? Waɗannan gwamnatocin duniya, wato “sarakuna goma” za su juya wa addinan ƙarya baya kuma su halaka su.​—R. Yar. 17:​1, 2, 16, 17.

15 Ta yaya muka san cewa an kusan halaka Babila Babba? Don mu amsa tambayar nan, ya kamata mu tuna cewa wani abin da ya ba wa birnin Babila na dā kāriya shi ne Kogin Yufiretis. Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya kwatanta miliyoyin mutane masu goyon bayan Babila Babba da “ruwa” mai ba da kāriya. (R. Yar. 17:15) Amma kuma ya bayyana cewa wannan ruwan zai bushe. Hakan yana nufin cewa daular addinan ƙarya na duniya za ta rasa mabiyanta da yawa. (R. Yar. 16:12) A yau, annabcin nan yana cika domin mutane da yawa suna barin addinan ƙarya kuma suna neman mafita daga matsalolinsu a wasu wurare dabam.

16. Ta yaya za mu amfana daga annabce-annabcen da aka yi game da bayyanuwar Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙarshen Babila Babba?

16 Ta yaya za mu amfana daga waɗannan annabce-annabcen? Bayyanuwar Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma yadda addinan ƙarya suke rasa mabiya, sun ƙara tabbatar mana cewa muna kwanakin ƙarshe. Ko da yake mutane da yawa sun daina goyon bayan Babila Babba, ba wannan ba ne zai kawo ƙarshen addinan ƙarya. Kamar yadda muka tattauna a baya, Jehobah zai sa ‘sarakuna goman,’ wato gwamnatoci da suke goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya su “aikata nufinsa.” Waɗannan gwamnatocin za su halaka Babila Babba nan tāke kuma hakan zai ba wa kowa da kowa a duniya mamaki.d (R. Yar. 18:​8-10) Wataƙila yadda za a halaka Babila Babba zai jawo matsaloli a duniya, amma bayin Allah suna da aƙalla dalilai biyu da za su sa su farin ciki. Za a halaka addinan ƙarya domin sun daɗe suna gāba da Jehobah kuma jim kaɗan, za a cece mu daga wannan muguwar duniya!​—Luk. 21:28.

KU BA DA GASKIYA CEWA JEHOBAH ZAI KĀRE MUTANENSA A NAN GABA

17-18. (a) Ta yaya za mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Daniyel ya annabta cewa “ilimi [na gaskiya] kuma zai ƙaru.” Hakan yana faruwa! A yanzu, mun fahimci annabce-annabce da aka yi game da zamaninmu. (Dan. 12:​4, 9, 10) Yadda waɗannan annabce-annabcen suke cika, sun taimaka mana mu daɗa daraja Jehobah da kuma Kalmarsa. (Isha. 46:10; 55:11) Saboda haka, ku ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarku ta wajen yin nazarin Nassosi kuma ku taimaka wa mutane su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Jehobah zai kāre waɗanda suka dogara gare shi kuma zai ba su “cikakkiyar salama.”​—Isha. 26:3.

18 A talifi na gaba, za mu mai da hankali ga annabce-annabcen da aka yi game da ikilisiyar Kirista a kwanakin ƙarshe. Kamar yadda za mu gani, annabce-annabcen ma sun nuna cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Za mu ga ƙarin tabbacin da ya nuna cewa Yesu wanda shi ne Sarkinmu yana yi wa mabiyansa ja-goranci.

TA YAYA WAƊANNAN ANNABCE-ANNABCEN SUKA NUNA CEWA YESU YA SOMA SARAUTA?

  • Daniyel 4:​10-17

  • Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​2-8

  • Daniyel 2:​28, 31-35; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​3-5, 9-12

WAƘA TA 61 Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!

a Muna rayuwa a lokacin da ya fi muhimmanci a tarihi! Yesu Kristi ya soma sarauta kamar yadda annabce-annabce da yawa a Littafi Mai Tsarki suka nuna. A wannan talifin, za mu tattauna wasu daga cikin annabce-annabcen nan don mu ƙarfafa bangaskiyarmu, kuma mu kasance da kwanciyar hankali da ƙarfin zuciya.

b Ka duba darasi na 32 batu na 4 a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, ka kuma kalli bidiyon nan Mulkin Allah Ya Soma Sarauta a 1914, a jw.org.

c Don samun ƙarin bayani a kan annabcin Daniyel, ka karanta Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2012, shafuffuka na 14-19.

d Don samun ƙarin bayani game da abubuwan da za su faru ba da daɗewa ba, ka duba babi na 21 na littafin nan Mulkin Allah Yana Sarauta!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba