Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp23 Na 1 p. 5
  • Allah Ya Damu da Kai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Ya Damu da Kai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Ina So In Mutu​—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min Idan Ina Tunanin Kashe Kaina?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Shin Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taꞌazantar da Ni Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Yi Alkawarin Ba Wa Mutane Cikakkiyar Lafiyar Kwakwalwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • Matsalar Ƙwaƙwalwa a Faɗin Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
wp23 Na 1 p. 5
Wani mutum yana zaune a kasa kusa da gadonsa yana karanta Littafi Mai Tsarki.

Allah Ya Damu da Kai

A LITTAFI MAI TSARKI ne za mu iya samun shawara mafi kyau, domin Kalmar Allah ce. Ba littafin kiwon lafiya ba ne amma zai taimaka mana mu san yadda za mu bi da yanayoyi masu wuya, da matsalolin da suke damunmu a zuciya da waɗanda suke damunmu a jiki da kuma ƙwaƙwalwa.

Mafi muhimmanci ma, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Mahaliccinmu Jehobaha ya san abubuwan da suke damunmu fiye da kowa. Yana shirye ya taimaka mana da duk wata matsalar da muke fama da ita. Ga wasu ayoyi daga Littafi Mai Tsarki da za su iya kwantar mana da hankali:

“Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.”​—ZABURA 34:18.

“Gama ni Yahweh Allahnka ne, ina riƙe da hannun damanka. Ni ne kuma nake ce maka, ‘Kada ka ji tsoro, ni ne mai taimakonka.’”​—ISHAYA 41:13.

Amma ta yaya Jehobah zai taimaka mana idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa? A talifofi na gaba, za ka ga yadda Jehobah ya damu da mu a hanyoyi da dama.

a Jehobah ko kuma Yahweh shi ne sunan Allah.​​—Zabura 83:18.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba