TARIHI
Jehobah Ya Kiyaye Ni don Na Dogara Gare Shi
IDAN mutane suka tambaye ni game da rayuwata, nakan gaya musu cewa, “Ina kamar kaya ne a hannun Jehobah!” Abin da nake nufi shi ne, kamar yadda zan iya ɗaukan kayana kuma in je duk inda na ga dama, haka ma nake son Jehobah da ƙungiyarsa su aike ni duk inda suke so, kuma a lokacin da suka ga ya dace. Hakan ya sa na yarda in yi wasu ayyuka da a wasu lokuta suka sa ni cikin haɗari. Amma darasin da na koya shi ne, idan na dogara ga Jehobah, zai kāre ni.
YADDA NA KOYA GAME DA JEHOBAH KUMA NA DOGARA GARE SHI
An haife ni a 1948 a wani ƙaramin ƙauye da ke kudu maso gabashin Najeriya. Ƙanin babana mai suna Moustapha da kuma yayana mai suna Wahabi sun yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Babana ya rasu saꞌad da nake shekara tara kuma hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Wahabi ya gaya min cewa za mu iya ganin babanmu a lokacin tashin matattu. Abin da ya faɗa ya taꞌazantar da ni kuma ya sa na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Na yi baftisma a shekara ta 1963. Daga baya, sauran ꞌyanꞌuwana maza guda uku su ma sun yi baftisma.
A 1965, na ƙaura zuwa wurin yayana mai suna Wilson a Legas. Kuma a wurin, na ji daɗin yin cuɗanya da ꞌyanꞌuwa da suke hidimar majagaba na kullum a ikilisiyar Igbobi. Yadda suke farin ciki da ƙwazo a hidimarsu ya burge ni. Kuma a watan Janairu, 1968, ni ma na soma hidimar majagaba.
Wani ɗanꞌuwa mai suna Albert Olugbebi da ke hidima a Bethel ya shirya wani taro na musamman da mu matasa a lokacin. A taron, ya ce ana bukatar majagaba na musamman a arewacin Najeriya. Ban manta da abin da Ɗanꞌuwa Olugbebi ya gaya mana da himma ba. Ya ce: “Ku matasa ne, kuma za ku iya amfani da lokacinku da ƙarfinku ku bauta wa Jehobah. Akwai aiki sosai a arewacin Najeriya!” Ina so in yi koyi da annabi Ishaya kuma in yi hidima a duk inda Jehobah ya ce in yi. Don haka, sai na cika fom na majagaba na musamman.—Isha. 6:8.
A watan Mayu, 1968, an tura ni hidimar majagaba na musamman a birnin Kano da ke arewacin Najeriya. A lokacin ne ake Yaƙin Biafra (wanda aka yi daga shekara ta 1967 zuwa 1970). Yaƙin ya jawo wahaloli da kuma kashe-kashe da dama a arewacin Najeriya. Daga baya ne yaƙin ya koma gabashin Najeriya. Wani ɗanꞌuwa ya yi ƙoƙari ya sa ni in ƙi zuwa wurin domin ba ya so wani abu ya faru da ni. Amma na ce masa: “Na gode da yadda ka damu da ni. Idan Jehobah yana so in je arewacin Najeriya, ina da tabbacin cewa zai kasance tare da ni.”
YADDA NA DOGARA GA JEHOBAH A YANKIN DA AKE YAƘE-YAƘE
Abubuwan da na gani a lokacin yaƙin a Kano sun sa ni baƙin ciki. Yaƙin ya yi ɓarna sosai a wannan babban birnin. A wasu lokuta saꞌad da muke waꞌazi, mukan ga gawawakin mutanen da aka kashe a ƙasa. Ko da yake akwai ikilisiyoyi da yawa a Kano, yawancin ꞌyanꞌuwan sun gudu sun bar wurin. Masu shela da suka rage ba su kai 15 ba. Suna jin tsoro kuma sun yi sanyin gwiwa. ꞌYanꞌuwan sun yi farin ciki sosai saꞌad da mu majagaba na musamman guda shida muka isa wurin. Mun ƙarfafa su kuma sun sami ƙarfin gwiwa. Mun taimaka musu su soma yin taro da zuwa waꞌazi. Ƙari ga haka, mun soma aika rahoton waꞌazi ga ofishinmu, da gaya musu adadin littattafan da muke bukata a waꞌazi.
Sai dukanmu majagaba na musamman muka soma koyan Hausa. Da yake muna yi wa mutanen waꞌazi a yarensu, hakan ya sa da yawa daga cikinsu sun saurare mu. Amma mabiyan addinin da aka fi bi a Kano ba sa son waꞌazinmu. Don haka, muna bukatar mu yi hankali sosai. Akwai lokacin da wani mutum ya bi ni da abokin waꞌazi na da wuƙa, amma mun yi gudu sosai da har mutumin ya kasa kama mu. Duk da matsalolin da muka fuskanta, Jehobah ya “kiyaye” mu kuma ya sa an samu ƙarin masu shela a wurin. (Zab. 4:8) A yau, akwai masu shela fiye da 500 da suke ikilisiyoyi guda 11 a Jihar Kano.
MUN FUSKANCI TSANANTAWA A NIJAR
Ina yin hidimar majagaba na musamman a birnin Yamai da ke Nijar
Bayan na yi ꞌyan watanni a Kano, sai aka tura ni tare da wasu majagaba na musamman guda biyu zuwa Yamai babban birnin Jumhuriyar Nijar, a watan Agusta 1968. Mun gano cewa a Yammacin Afrika, Nijar tana cikin ƙasashe mafi zafi a duniya. Ban da cewa ƙasar tana da zafi sosai, muna bukatar mu koyi yaren da aka fi yi a ƙasar, wato Farasanci. Duk da waɗannan matsalolin, mun dogara ga Jehobah kuma muka soma yin waꞌazi a babban birnin tare da masu shela kalila da suke zama a wajen. Kafin ka sani, kusan dukan mutanen da suka iya karatu a Yamai sun samu littafin nan Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami. Mutane sukan zo wurinmu don su karɓi littafin.
Ba da jimawa ba, mun gano cewa hukumomi a wurin ba sa son Shaidun Jehobah. A watan Yuli 1969, mun haɗu don mu yi taron daꞌira na farko da za a yi a ƙasar, kuma mutane 20 ne kawai suka halarta. Mun yi marmarin ganin lokacin da masu shela guda biyu za su yi baftisma. Amma a rana ta farko na taron, ꞌyan sanda sun zo kuma suka dakatar da taron. Sun ɗauki dukan majagaba na musamman da mai kula da daꞌirar zuwa ofishin ꞌyan sanda. Bayan sun yi mana tambayoyi, sai suka umurce mu mu sake dawowa washegari. Da muka ga cewa akwai matsala, sai muka yi jawabin baftisma a gidan wani kuma muka yi wa masu shelar baftisma a ɓoye a wani rafi.
Gwamnati ta dokace ni da kuma majagaba na musamman guda 5 cewa mu bar ƙasar. Kwana biyu kawai suka ba mu mu bar ƙasar, kuma mu da kanmu ne za mu shirya yadda za mu yi hakan. Mun bi umurnin kuma muka koma ofishinmu da ke Najeriya inda aka ba mu sabon hidima.
An tura ni wani ƙauye mai suna Orisunbare a Najeriya kuma na ji daɗin yin waꞌazi a wurin sosai tare da masu shela kalilan da suke zama a wurin. Bayan watanni shida, ofishinmu da ke Najeriya ya gaya min cewa in koma Nijar ni kaɗai. Na yi mamaki da farko kuma na ɗan damu amma daga baya na yi marmarin sake haɗuwa da ꞌyanꞌuwa a Nijar.
Sai na koma Yamai. Ina isowa, sai washegari na haɗu da wani ɗan kasuwa daga Najeriya da ya gane cewa ni Mashaidi ne kuma ya soma yi min tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Na yi nazari da shi kuma bayan da ya daina shan taba da yawan shan giya, sai ya yi baftisma. Bayan haka, na ji daɗin yin waꞌazi tare da ꞌyanꞌuwa maza da mata a wurare dabam-dabam a Nijar kuma na yi farin cikin ganin yadda mutane suka soma bauta wa Jehobah kaɗan-da-kaɗan. A lokacin da na zo ƙasar, Shaidun Jehobah guda 31 ne kawai a wurin, amma da na bar ƙasar, Shaidun Jehobah sun kai 69.
“BA MU SAN YAYA ꞌYANꞌUWA SUKE A ƘASAR GINI BA”
A watan Disamba 1977, na koma Najeriya don a horar da ni. Bayan an yi mako uku ana horar da ni, mai shirya ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu na Najeriya, wato Malcolm Vigo ya sa na karanta wata wasiƙa daga ofishin Saliyo. ꞌYanꞌuwan suna neman majagaba wanda yake da ƙoshin lafiya, marar aure, kuma ya iya Turanci da Farasanci, don ya je ƙasar Gini kuma ya yi hidima a matsayin mai kula da daꞌira. Ɗanꞌuwa Vigo ya gaya min cewa abin da suka horar da ni a kai ke nan. Ya gaya min cewa ba aiki mai sauƙi ba ne. Sai ya ce mini: “Ka yi tunani da kyau kafin ka amince da hidimar nan.” Nan da nan sai na ce masa, “Tun da Jehobah ne yake so in je wurin, zan je.”
Sai na shiga jirgi na tafi Saliyo kuma na haɗu da ꞌyanꞌuwa da ke ofishinmu a wurin. Wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu ya gaya min cewa: “Ba mu san yaya ꞌyanꞌuwanmu maza da mata suke a ƙasar Gini ba.” Ko da yake ꞌyanꞌuwanmu da ke Saliyo ne suke kula da waꞌazi da ake yi a Gini, ꞌyanꞌuwan ba sa iya yin magana da masu shela saboda rigingimun siyasa da ake yi a ƙasar. ꞌYanꞌuwan sun yi iya ƙoƙarinsu don su aiki wanda zai ziyarci ꞌyanꞌuwa a Gini amma sun kasa. Don haka, sun gaya min in je babban birnin Gini, wato Konakiri don in ga ko zan iya samun izinin zama a wurin.
“Tun da Jehobah ne yake so in je wurin, zan je”
Da na isa Konakiri, sai na je ofishin jakadanci na Najeriya kuma na haɗu da jakadar Najeriya. Na gaya masa cewa ina so in yi waꞌazi a Gini. Ya gaya min in bar ƙasar domin za a iya kama ni ko ma a kashe ni. Ya ce min: “Ka koma Najeriya ka yi waꞌazi a wurin.” Sai na gaya masa, “Ina so in zauna a nan.” Sai ya aika wa Ministan harkokin cikin gida na Gini wasiƙa kuma ya ce masa ya taimaka mini, sai mutumin ya taimaka min.
Ba da jimawa ba bayan haka, Sai na koma ofishinmu da ke Saliyo kuma na gaya wa ꞌyanꞌuwan abin da ministan ya ce. ꞌYanꞌuwan sun yi farin ciki sosai don yadda Jehobah ya sa zuwa na Gini ya yi nasara.
Saꞌad da nake hidimar mai kula da daꞌira a Saliyo
Daga 1978 zuwa 1989, na yi hidimar mai kula da daꞌira a Gini da Saliyo, da kuma hidimar wakilin mai kula da daꞌira a Laberiya. Da farko dai, na yi ta rashin lafiya sosai. A wasu lokuta yakan faru ne saꞌad da na ziyarci ikilisiyoyin da ke ƙauye. Amma ꞌyanꞌuwan za su yi iya ƙoƙarinsu don su kai ni asibiti.
Akwai lokacin da na kamu da cutar cizon sauro mai tsanani da kuma tsutsar ciki. Da na samu sauƙi, sai ꞌyanꞌuwan suka gaya min cewa dā ma suna shirya inda za su binne ni don sun zata zan mutu. Duk da waɗannan matsaloli masu wuya, ban taɓa yin tunanin daina yin hidimata ba. Kuma na ci-gaba da kasance da tabbacin cewa, Jehobah ne kaɗai zai iya kiyaye mu kuma ko da mun mutu, zai iya ta da mu daga mutuwa.
NI DA MATATA MUN DOGARA GA JEHOBAH
Ranar aurenmu a 1988
A 1988, na haɗu da Dorcas, ita majagaba ce, tana ƙaunar Jehobah sosai kuma tana da sauƙin kai. Mun yi aure kuma muka ci-gaba da hidimar mai kula da daꞌira tare. Dorcas ta yi iya ƙoƙarinta a dukan hidimar da muka yi, kuma a shirye take ta yi sadaukarwa don Jehobah. Ni da ita, mukan yi tafiya mai nisan kilomita 25 da kafa daga wata ikilisiya zuwa wata ikilisiya kuma muna hakan ɗauke da kayanmu a kai. Amma idan za mu je ikilisiyoyin da suka fi hakan nisa, mukan yi amfani da duk wani abin hawa da muka samu kuma hanyoyin ba su da kyau sosai.
Dorcas tana da ƙarfin zuciya sosai. Alal misali, mukan tsallake rafin da akwai kadoji a ciki. Akwai wani lokacin da muka yi tafiya na kwana biyar kuma gadan da ya kamata mu bi ya karye, don haka mun shiga kwalekwale. Da matata ta tashi don ta fita daga kwalekwalen, sai ta faɗi a cikin rafin kuma wurin na da zurfi. Ni da ita ba mu iya iyo ba, kuma akwai kadoji a cikin rafin. Amma mun sami wasu matasa da suka shiga cikin ruwan suka fito da ita. Mun daɗe muna mafarki mai ban tsoro game da wannan abin, amma mun ci-gaba da hidimarmu.
Yaranmu Jahgift da kuma Eric, kyauta ne daga wurin Jehobah
A farkon 1992, mun yi mamaki da muka gano cewa Dorcas tana da juna biyu. Mun yi tunanin ko za mu daina hidimar majagaba na musamman. Mun gaya wa kanmu cewa, “Jehobah ya ba mu kyauta!” Sai muka ba wa ꞌyarmu suna, Jahgift wato Kyauta daga wurin Jehobah. Shekara huɗu bayan mu haifi Jahgift, sai muka haifi ƙaninta, Eric. Hakika, yaranmu guda biyu kyauta ne daga wurin Jehobah. Jahgift ta yi hidima a ofishin fassara da ke Konakiri na ꞌyan lokuta, Eric kuma bawa ne mai hidima.
Ko da yake Dorcas ta daina hidimar majagaba na musamman, ta ci-gaba da yin hidimar majagaba na kullum duk da cewa tana renon yaranmu. Ni kuma, Jehobah ya taimaka min in ci-gaba da yin hidimar majagaba na musamman. Da yaranmu suka yi girma, sai Dorcas ta sake soma hidimar majagaba na musamman. Yanzu ni da ita muna hidimar masu waꞌazi a ƙasashen waje a Konakiri.
JEHOBAH YA KIYAYE MU
A kowanne lokaci, ina zuwa duk inda Jehobah ya aike ni. Ni da matata mun ga yadda Jehobah ya kāre mu da kuma yi mana albarka. Da yake mun dogara ga Jehobah ba abin duniya ba, hakan ya taimaka mana mu guji matsaloli da yawa. Abubuwan da muka fuskanta a rayuwa, sun koya wa ni da Dorcas cewa Jehobah “Allahnmu Mai Cetonmu” ne kaɗai zai iya kiyaye mu. (1 Tar. 16:35) Ina da tabbacin cewa dukan waɗanda suka dogara ga Jehobah, Jehobah zai ci-gaba da kāre su.—1 Sam. 25:29.