ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI
Kana da Bangaskiya?
Sai da bangaskiya za mu iya faranta wa Allah rai. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce “ba duka suka ba da gaskiya ba,” wato ba kowa ne yake da halin nan ba. (2 Tas. 3:2) A wannan ayar, manzo Bulus yana magana ne a kan “mugayen mutane” da suke tsananta masa. Amma abin da ya faɗa ya shafi wasu ma. Alal misali, wasu da gangan suke ƙin yin imani cewa akwai Allah kuma shi ne ya halicci kome. (Rom. 1:20) Wasu kuma suna ganin suna da bangaskiya don sun gaskata cewa akwai Allah. Amma hakan kawai ba zai gamsar da Allah ba.
Muna bukatar mu gaskata cewa akwai Allah, kuma yana “ba da lada” ga masu bangaskiya sosai. (Ibran. 11:6) Ruhu mai tsarki ne yake sa mutum ya ba da gaskiya. Kuma mutum zai iya roƙon Jehobah ya ba shi ruhu mai tsarki. (Luk. 11:9, 10, 13) Wata hanya ta musamman kuma da za mu iya samun ruhu mai tsarki ita ce ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki, domin ruhu mai tsarki ne ya ja-goranci marubutansa. Bayan mun karanta shi, mu yi tunani a kan abin da muka karanta, kuma mu yi ƙoƙarin binsa a rayuwarmu. Yin haka zai sa ruhun Allah ya taimaka mana mu yi rayuwar da za ta nuna cewa mu masu bangaskiya ne. Kuma irin bangaskiyar nan ne yake faranta wa Allah rai.