TALIFIN NAZARI NA 35
WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
Yadda Za A Taimaka wa Waɗanda Aka Cire Daga Ikilisiya
“Za a yi murna sosai a sama a kan mai zunubi guda ɗaya wanda ya tuba, fiye da masu adalci casaꞌin da tara, waɗanda ba sa bukatar tuba.”—LUK. 15:7.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga dalilin da ya sa ake bukata a cire wasu daga ikilisiya da kuma yadda dattawa za su taimake su su tuba kuma su komo ga Jehobah.
1-2. (a) Idan mutum yana yin zunubi kuma ya ƙi ya tuba, yaya Jehobah yake ɗaukansa? (b) Mene ne Jehobah yake so wanda ya yi zunubi ya yi?
BA KOWANE hali ne Jehobah yake yarda da shi ba, kuma ya tsane zunubi. (Zab. 5:4-6) Shi ya sa yake bukatar mu bi ƙaꞌidodin da ke Kalmarsa. Jehobah ya san cewa mu ajizai ne, don haka za mu yi kuskure. (Zab. 130:3, 4) Amma ba ya ƙyale waɗanda “ba su da hali irin na Allah,” da suke “mai da alherin Allah ya zama hanyar neman jin daɗi na rashin kunya.” (Yahu. 4) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “za a yi wa marasa halin Allah hukunci” a yaƙin Armageddon.—2 Bit. 3:7; R. Yar. 16:16.
2 Amma Jehobah ba ya so wani ya halaka. Kamar yadda muka ji a talifofin da suka gabata, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana so “kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) Dattawa kuma suna koyi da Jehobah ta wurin yin haƙuri da masu zunubi yayin da suke taimaka musu su komo ga Jehobah. Amma ba kowa ne yake yarda da taimakonsu ba. (Isha. 6:9) Duk da ƙoƙarin da dattawa suke yi, wasu sukan ci-gaba da yin zunubi. Me dattawa za su yi idan hakan ya faru?
“KU KAWAR DA MUGUN NAN DAGA CIKINKU”
3. (a) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce a yi wa wanda ya yi zunubi kuma ya ƙi ya tuba? (b) Me ya sa za mu iya cewa idan aka cire mutum daga ikilisiya, shi ya so?
3 Idan mai zunubin ya ƙi ya tuba, dole dattawa su bi abin da 1 Korintiyawa 5:13 ta ce, wato ‘su kawar da mugun daga cikinsu.’ Mai zunubin ya san cewa idan ya ƙi ya tuba, za a cire shi daga ikilisiya. Don haka, idan aka cire shi, shi ya so. Abin da ya shuka ne yaa girba. (Gal. 6:7) Me ya sa muka ce haka? Domin mai zunubin ne ya ƙi ya tuba duk da ƙoƙarin da dattawa suka yi ta yi don su taimaka masa. (2 Sar. 17:12-15) Halinsa ya nuna cewa ba ya so ya yi wa Jehobah biyayya.—M. Sha. 30:19, 20.
4. Me ya sa ake yin sanarwa idan aka cire wanda ya ƙi tuba daga ikilisiya?
4 Idan aka cire mai zunubin da ya ƙi ya tuba daga ikilisiya, akan sanar da cewa yanzu shi ba Mashaidin Jehobah ba ne.b Me ya sa ake wannan sanarwa? Ba don a kunyatar da shi ba ne. Amma don a taimaki ꞌyanꞌuwa su bi abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ne, cewa ‘kada mu haɗa kai’ da shi, kuma ‘kada mu ko ci abinci tare’ da shi. (1 Kor. 5:9-11) Akwai dalili mai kyau da ya sa aka ba da umarnin nan. Manzo Bulus ya ce: “Ɗan yisti kaɗan yake kumburar da dukan dunƙulen burodi.” (1 Kor. 5:6) Idan ba a cire mai zunubin da ya ƙi ya tuba daga ikilisiya ba, hakan zai iya sa wasu ꞌyanꞌuwa su daina riƙe amincinsu.—K. Mag. 13:20; 1 Kor. 15:33.
5. Yaya ya kamata mu ɗauki wanda aka cire daga ikilisiya, kuma me ya sa?
5 To, yaya ya kamata mu ɗauki wanda aka cire daga ikilisiya? Ya kamata mu tuna cewa mutumin zai iya dawowa. A yanzu dai shi kamar tunkiya da ta ɓata ne, kuma idan tunkiya ta ɓata za ta iya dawowa cikin garken. Mu tuna cewa ɗanꞌuwan ya yi alkawari cewa zai bauta wa Jehobah. Yanzu ba ya cika wannan alkawarin, kuma hakan babban kuskure ne. (Ezek. 18:31) Duk da haka, zai iya dawowa tun da Jehobah bai rufe kofa ba tukuna. Ta yaya dattawa za su taimaka wa wanda aka cire daga ikilisiya?
YADDA DATTAWA ZA SU TAIMAKA WA WANDA AKA CIRE DAGA IKILISIYA
6. Mene ne dattawa za su yi don su taimaka wa wanda aka cire daga ikilisiya?
6 Idan aka cire wani daga ikilisiya, shin, dattawa za su daina ƙoƙarin taimaka masa ya komo ga Jehobah ne? Aꞌa. A lokacin da dattawa za su gaya wa mutum cewa za a cire shi daga ikilisiya, za su kuma bayyana masa abin da zai yi don a dawo da shi. Ƙari ga haka, a yawancin lokaci za su gaya wa wanda ya yi zunubin cewa, za su sake tattaunawa da shi bayan ꞌyan watanni don su ji ko zai canja raꞌayinsa. Idan ya yarda, dattawa za su sake zama da shi kuma su ƙarfafa shi ya tuba kuma ya komo ga Jehobah. Ko da a wannan lokacin ya ƙi ya tuba, dattawa za su ci-gaba da ƙoƙarin tattaunawa da shi jifa-jifa don su taimaka masa ya tuba.
7. Ta yaya dattawa za su nuna tausayi kamar Jehobah idan suna shaꞌani da wanda aka cire daga ikilisiya? (Irmiya 3:12)
7 Jehobah yana tausaya wa waɗanda aka cire daga ikilisiya. Don haka dattawa ma ba za su daina tausaya musu ba. Alal misali, da Israꞌilawa suka daina bin Jehobah, bai ce sai sun tuba kafin ya taimaka musu ba. A maimakon haka, tun suna kan yin zunubin Jehobah ya yi ta roƙonsu su tuba. Kamar yadda muka gani a talifi na biyu a wannan Hasumiyar Tsaro, Jehobah ya ce wa annabi Hosiya ya yafe wa matarsa duk da cewa a lokacin tana kan bin maza. Kuma Jehobah ya yi haka ne don ya nuna wa mutanensa irin tausayin da yake da shi. (Hos. 3:1; Mal. 3:7) Kamar Jehobah, dattawa ma suna so wanda ya yi zunubi ya tuba kuma ya komo. Ƙari ga haka, suna marmarin su taimaka masa ya yi hakan.—Karanta Irmiya 3:12.
8. Ta yaya labarin ɗan nan da babansa da Yesu ya bayar ya nuna yawan tausayi da jinƙan Jehobah? (Luka 15:7)
8 Ka tuna da labarin saurayin nan da babansa. Da baban ya ga ɗansa yana dawowa gida, sai “ya tashi da gudu ya je ya rungumi ɗansa, ya yi ta yi masa sumba.” (Luk. 15:20) Shin, ka lura cewa bai jira ɗansa ya zo ya nemi gafara tukuna kafin ya karɓe shi ba? A maimakon haka shi ne ya je ya sami ɗan, domin yana ƙaunarsa. Irin halin da dattawa za su nuna wa wanda aka cire daga ikilisiya ke nan. Suna marmari su ga “ya dawo.” (Luk. 15:22-24, 32) Idan mai zunubi ya tuba kuma ya dawo, Jehobah da Yesu da malaꞌiku da kuma ikilisiya suna farin ciki sosai!—Karanta Luka 15:7.
9. Mene ne Jehobah yake so masu zunubi su yi?
9 A tattaunawarmu mun ga cewa Jehobah ba ya barin waɗanda suka yi zunubi kuma suka ƙi su tuba a ikilisiya. Amma kuma ba ya ƙin su kwatakwata. Yana so su komo gare shi. A Hosiya 14:4 Jehobah ya gaya mana abin da zai yi musu. Ya ce: “Zan gafarta musu. Zan ƙaunace su da zuciyata a sake, gama fushina a kansu ya kwanta.” Da yake tunanin da Jehobah yake musu ke nan, dattawa ma ba za su ɓata lokaci ba da zarar sun ga alama cewa mutum ya tuba. Kuma zai yi kyau waɗanda suka bar Jehobah su yi ƙoƙari su dawo ba tare da ɓata lokaci ba.
10-11. Ta yaya dattawa za su taimaka wa waɗanda aka cire daga ikilisiya da daɗewa?
10 Ta yaya dattawa za su taimaka wa waɗanda aka cire daga ikilisiya da daɗewa? Wataƙila wasunsu sun riga sun daina yin zunubin da ya sa aka cire su. Ƙila ma sun manta da abin da ya sa aka cire su. Ko da ya daɗe sosai da aka cire mutum, ko bai daɗe sosai ba, dattawa za su yi ƙoƙari su nemi inda yake kuma su ziyarce shi. Idan suka ziyarce shi kuma ya karɓe su, dattawan za su yi adduꞌa tare da shi kuma su roƙe shi ya komo ga Jehobah. Idan mutum ya yi shekaru da yawa da barin ikilisiya, bangaskiyarsa za ta yi sanyi sosai. Idan mutumin yana so ya dawo cikin ikilisiya, dattawa za su iya shirya yadda za a yi nazari da shi, ko ba a riga an sanar da cewa an dawo da shi ba. Amma dattawa ne kaɗai za su riƙa zaɓan waɗanda za su yi nazari da irin mutanen nan.
11 Dattawa za su nuna cewa suna tausaya wa waɗanda suka bar Jehobah ta wurin ziyartarsu da kuma taimaka musu su san cewa za su iya komowa. Halin Jehobah suke bi. Idan wanda ya yi zunubin ya tuba kuma ya canja halinsa, za a dawo da shi ba tare da ɓata lokaci ba.—2 Kor. 2:6-8.
12. (a) A waɗanne lokuta ne dattawa suke bukatar su lura sosai kafin su dawo da mutum cikin ikilisiya? (b) Me ya sa bai kamata mu ɗauka cewa Jehobah ba zai taɓa gafarta wa wasu don irin zunubin da suka yi ba? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
12 Akwai lokutan da dattawa suke bukata su lura sosai kafin su dawo da mutum cikin ikilisiya. Alal misali, idan an kama mutumin ne da cin zarafin yaro, ko idan ɗan ridda ne, ko ya yi wayo don ya kashe aurensa. Dole dattawa su tabbata cewa ya tuba da gaske. (Mal. 2:14; 2 Tim. 3:6) Domin hakkinsu ne su kāre ꞌyanꞌuwan da ke ikilisiya. Duk da haka, mu tuna cewa idan har mutum ya tuba da gaske kuma ya canja halinsa, Jehobah zai karɓe shi. Don haka, kada dattawa su soma ganin kamar Jehobah ba zai taɓa gafarta wa wasu don irin zunubin da suka yi ba.c—1 Bit. 2:10.
YADDA KOWA A IKILISIYA ZAI TAIMAKA
13. Yadda za mu bi da wanda aka yi masa horo, da wanda aka cire shi daga ikilisiya ɗaya ne? Ka bayyana.
13 Kamar yadda muka tattauna a talifi da ya gabata, a wasu lokuta, akan yi sanarwa cewa an yi wa mutum horo. Idan hakan ya faru, za mu ci-gaba da yin tarayya da mutumin don mun san cewa ya tuba kuma ya canja halinsa. (1 Tim. 5:20) Har ila shi ɗanꞌuwa ne a ikilisiya kuma yana bukatar mu riƙa yin abubuwa tare da shi don mu ƙarfafa juna. (Ibran. 10:24, 25) Amma ba haka yake da mutumin da aka cire daga ikilisiya ba. Idan hakan ya faru, za mu daina “haɗa kai” da mutumin, “ko ci abinci tare da” shi ma ba za mu yi ba.—1 Kor. 5:11.
14. Ta yaya kowane Kirista zai bi abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki, idan ya zo ga wanda aka cire shi daga ikilisiya? (Ka kuma duba hoton.)
14 Hakan yana nufin cewa ba za mu sake kula wanda aka cire shi daga ikilisiya ba ne? Ba lallai ba. Ba za mu yi tarayya da shi ba. Amma a batun gayyatar sa zuwa taro, kowane Kirista ya yi abin da zuciyarsa ta ba shi, bisa ga abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki. Wataƙila mutumin danginmu ne ko abokinmu a dā. Idan ya zo taro kuma fa? A dā ba ma gai da su. Amma yanzu, kowane Kirista ne zai zaɓi abin da zai yi bisa ga abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki. Idan mutum ya so, zai iya ya ɗan gaishe shi, ko ya marabce shi. Amma ba za mu shiga yin wani dogon zance da shi, ko mu shiga yin wasu abubuwa da shi ba.
A batun gayyatar wanda aka cire daga ikilisiya zuwa taro ko yin ɗan gaisuwa da shi idan ya zo taro, kowane Kirista ne zai zaɓi abin da zai yi bisa ga abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 14)
15. Su wa ake magana a kai a 2 Yohanna 9-11? (Ka kuma duba akwatin nan, “Zunubin da Yohanna da Bulus Suka Yi Magana a kai Iri Ɗaya Ne?”)
15 Ƙila wasu su ce, ‘Ba Littafi Mai Tsarki ya ce duk wanda ya gai da irin wannan mutum, yana haɗa kai da mutumin cikin mugun aikinsa ke nan ba?’ (Karanta 2 Yohanna 9-11.) Wannan nassin yana magana ne game da ꞌyan ridda da waɗanda suke goyon bayan yin zunubi. (R. Yar. 2:20) Shi ya sa idan wanda aka cire daga ikilisiya ɗan ridda ne ko yana goyon bayan yin zunubi, dattawa ba za su ziyarce shi ba. Amma har ila irin wannan mutumin zai iya tuba. Sai dai muddin bai tuba ba, ba za mu gaishe shi ko gayyace shi ya zo taronmu ba.
MU ZAMA MASU TAUSAYI DA JINƘAI KAMAR JEHOBAH
16-17. (a) Mene ne Jehobah yake so masu zunubi su yi? (Ezekiyel 18:32) (b) Ta yaya dattawa za su nuna cewa suna yin aiki da Jehobah?
16 Me muka koya a jerin talifofin nan? Mun koyi cewa Jehobah ba ya so wani ya halaka! (Karanta Ezekiyel 18:32.) Yana so masu zunubi su shirya da shi kuma su zama abokansa. (2 Kor. 5:20) Shi ya sa a-ko-da-yaushe yana kira ga bayinsa da suka bar shi su tuba kuma su komo gare shi. Babban gata ne Jehobah ya ba wa dattawa da ya ce su yi aiki tare da shi wajen taimaka wa masu zunubi su tuba.—Rom. 2:4; 1 Kor. 3:9.
17 Ana farin ciki sosai a sama idan mai zunubi ya tuba! Ubanmu na sama, wato Jehobah, yana farin ciki sosai idan bawansa ya dawo cikin ikilisiya. Ba shakka yin tunani mai zurfi a kan yawan tausayin Jehobah, da jinƙansa, da kuma alherinsa, zai sa mu ƙara ƙaunar sa.—Luk. 1:78.
WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna
a A talifin nan, za mu dinga magana kamar wanda ya yi zunubin namiji ne. Amma idan mace ma ta yi zunubi, haka za a yi da ita.
b Yanzu ba ma ce an yi wa mutum yankan zumunci. Bisa ga abin da manzo Bulus ya ce a 1 Korintiyawa 5:13, za mu riƙa cewa an cire mutumin daga ikilisiya.
c Littafi Mai Tsarki ya ce akwai wasu da ba za a taɓa yafe musu ba. Irin mutanen nan sun riga sun ƙudura a zuciyarsu cewa abin da Allah ba ya so ne za su riƙa yi. Jehobah da Yesu ne kaɗai za su iya cewa ba za a yafe wa mutum ba.—Mar. 3:29; Ibran. 10:26, 27.