TARIHI
Na Sami Gamsuwa don Hidimata ga Jehobah
A 1951, na je wani gari mai suna Rouyn, a yankin Quebec a ƙasar Kanada. Sai na je gidan da aka ba ni adireshinsa. Da na ƙwanƙwasa kofar, sai wani mai waꞌazi a ƙasar waje mai suna Marcel Filteaua ya buɗe kofa. Shekarunsa 23, kuma yana da tsayi sosai; Ni kuma shekaruna 16 kuma ban kai shi tsayi ba. Da na nuna masa wasiƙata na zama majagaba kuma ya karanta, ya yi mamaki. Sai ya ce min, “Anya mahaifiyarka ta san kana nan kuwa?”
IYALINMU
A 1934 aka haife ni, a wani gari mai suna Timmins da ake hakka maꞌadanai, a yankin Ontario, a Kanada. Kuma iyayena ꞌyan ƙasar Suwizalan ne da suka ƙaura zuwa Kanada. A wajen shekara ta 1939 ne mahaifiyata ta soma karanta Hasumiyar Tsaro da kuma zuwa taron Shaidun Jehobah. Idan za ta je taron, takan kai ni da ꞌyanꞌuwana. Kuma ba da daɗewa ba ita ma ta zama Mashaidiyar Jehobah.
Babanmu bai ji daɗin abin da ta yi ba. Amma mahaifiyarmu ta so gaskiyar da ta koya, kuma ta ce za ta ci-gaba da bauta wa Jehobah. Ba ta ja da baya ba har a lokacin da aka hana aikinmu a Kanada a shekara ta 1940. Amma ta ci-gaba da yi wa mahaifinmu alheri, tana daraja shi ko da me ya gaya mata. Halinta yana cikin abubuwan da suka sa ni da ꞌyanꞌuwana shida muka ce za mu bauta wa Jehobah. Godiya ga Jehobah, a-kwana-a-tashi babanmu ya daina tsananta mana, kuma ya soma kyautata mana.
NA SOMA YIN HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
A Agusta 1950, na je wani babban taro mai jigo, Theocracy’s Increase, da aka yi a birnin New York a Amurka. A taron, na haɗu da ꞌyanꞌuwa daga wurare da dama a faɗin duniya, kuma an yi ganawa da ꞌyanꞌuwa da suka je Makarantar Gilead. Labaransu sun sa na so in ƙara ƙwazo a hidimata ga Jehobah. Na ce ni ma sai na yi hidima ta cikakken lokaci. Ina dawowa gida, sai na sanar da rashen ofishinmu na Kanada cewa ina so in zama majagaba na kullum. Sai suka amsa min da cewa ya kamata in yi baftisma tukuna. Na yi baftisma a ran 1 ga Oktoba, 1950. Bayan wata ɗaya sai aka mai da ni majagaba na kullum, kuma aka tura ni yin hidima a wani gari mai suna Kapuskasing. Garin yana da nisa sosai daga inda nake.
Lokacin da nake hidima a Quebec
A 1951, an rubuta wasiƙa daga rashen ofishinmu don a ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da suka iya Faransanci su je yin hidima a yankin Quebec. Ana bukatar masu shela sosai a wurin, kuma Faransanci ne ake yi a yankin. Na iya Turanci da Faransanci. Don haka na yarda zan je, sai aka tura ni wani gari mai suna Rouyn. Ban san kowa a wurin ba. Adireshin inda Ɗanꞌuwa Marcel yake ne kawai nake da shi. Kamar yadda na ambata a farkon labarin nan, wurin na je. Ɗanꞌuwa Marcel ya karɓe ni hannu bibbiyu, kuma mun zama abokai sosai. Na yi shekaru huɗu ina jin daɗin hidimata a yankin Quebec, kuma daga baya an mai da ni majagaba na musamman.
ZUWA GILEAD DA YADDA NA BUKACI YIN HAƘURI
Saꞌad da nake Quebec, an gayyace ni zuwa aji na 26 na Makarantar Gilead a yankin South Lansing da ke New York. Na yi farin ciki sosai! Bayan da na sauke karatu a ranar 12 ga Fabrairu, 1956, sai aka tura ni yin hidima a ƙasar Ghana,b da ke Afirka. Amma na fara zuwa Kanada don in ɗan jira sai an gama haɗa min takardun barin ƙasa.
Na zata ꞌyan makonni zan yi, amma abin ya ɗauki watanni bakwai. A lokacin na zauna a gidan wani ɗanꞌuwa mai suna Cripps. Yana da wata ꞌya mai suna Sheila, kuma mun soma fita zance. Ina shirin tambayarta ko za ta aure ni ke nan, sai aka kawo min bizan da nake jira. Da na gaya wa Sheila, sai muka yi adduꞌa, kuma muka yarda cewa zan tafi yin hidimata a Ghana. Amma za mu ci-gaba da yin magana ta wurin tura wa juna wasiƙu. Kuma muna fatan za mu yi aure. Yanke wannan shawarar bai yi mana sauƙi ba, amma a-kwana-a-tashi, mun ga cewa hakan ne ya fi.
Tafiyar ta ɗauke ni wata guda. Sai da na bi jirgin ƙasa, da jirgin ruwa, da jirgin sama kafin na isa birnin Accra, a ƙasar Ghana. A wurin an mai da ni mai kula da gunduma. Hidimar ta sa na yi tafiye-tafiye sosai a ƙasar Ghana, har da ƙasar Kwat Dibuwa (wanda a lokacin ake kira Ivory Coast) da kuma ƙasar Togo (Togoland). Yawancin lokaci ni kaɗai nake tafiya a motar rashen ofishinmu. Na ji daɗin aikin sosai!
A ƙarshen mako, nakan yi ayyuka da dama a taron daꞌira. Lokacin ba mu da Majamiꞌun Taro. Don haka, ꞌyanꞌuwa sukan yi amfani da gora da ganyen kwakwa su yi rumfa da zai kāre mu daga zafin rana. Kuma da yake ba mu da firiji, mukan ajiye dabbobi da ransu, saꞌan nan a yanka su lokacin da za a dafa ma waɗanda suka zo taron abinci.
Wasu abubuwan ban dariya sun faru a lokacin. Alal misali, akwai ran da wani mai waꞌazi a ƙasar waje mai suna Herb Jenningsc yake yin jawabi, sai kawai wata saniya ta gudu daga inda aka ɗora ta. Ta zo ta wuce da gudu tsakanin dakalin magana da inda mutane suke zama. Da Ɗanꞌuwa Herb ya gan ta, sai ya daina magana. Ita saniyar kuma ta rikice. Sai ꞌyanꞌuwa maza huɗu suka je suka kama saniyar suka kai ta inda aka ɗora ta dā. Jamaꞌa kuma suka kama ihu suna tafi.
Kafin ranar da za a yi taro, nakan bi ƙauyukan da ke kusa ina nuna fim ɗinmu mai suna, The New World Society in Action. Da yake da naꞌurar projector nake haska fim ɗin, nakan kafa sanduna biyu kuma in ɗora farin ƙyalle tsakaninsu, ko in ɗora ƙyallen tsakanin itatuwa biyu, sai in kunna fim ɗin. Mutanen ƙauyen suna jin daɗinsa sosai! Yawancinsu ba su taɓa kallon fim ba sai wannan. Idan suka ga inda ake yi wa mutane baftisma, sai su yi tafi sosai. Wannan fim ya sa mutane sun ga cewa Shaidun Jehobah suna da haɗin kai, kuma suna a koꞌina a duniya.
Mun yi aure a Ghana a 1959
Bayan da na yi shekaru biyu a Afirka, sai na je wani taron ƙasa-da-ƙasa da aka yi a birnin New York, a 1958. ꞌYarꞌuwa Sheila ma ta zo taron daga Quebec, inda take hidimar majagaba na musamman. Na yi farin ciki sosai da na gan ta. Kafin lokacin, muna magana da juna ta wasiƙu. Yanzu da muka sake haɗuwa, sai na tambaye ta ko za ta aure ni, kuma ta yarda. Bayan haka, sai na rubuta wasiƙa zuwa ga Ɗanꞌuwa Knorr,d na tambaye shi ko zai yiwu a kira ꞌYarꞌuwa Sheila Makarantar Gilead, kuma idan ta sauke karatu a turo ta Afirka inda nake. Ya yarda, kuma a-kwana-a-tashi, Sheila ta zo Ghana. Mun yi aure a ran 3 ga Oktoba, 1959, a birnin Accra. Hakika Jehobah ya albarkace mu don mun sa hidimarsa farko a rayuwarmu.
HIDIMARMU A KAMARU
Ina hidima a rashen ofishinmu a Kamaru
A 1961, an tura mu yin hidima a ƙasar Kamaru. An ce min in taimaka wajen kafa sabon rashen ofishi a wurin, don haka na sha aiki sosai. Da yake an mai da ni mai kula da ofishin, ina bukatar in koyi abubuwa da yawa. Ana nan, a shekara ta 1965 sai matata Sheila ta yi ciki. Ba mu taɓa tsammani cewa za mu zama iyaye ba, don haka abin bai zo mana da sauƙi ba. Sai muka soma shirin komawa Kanada. Amma kafin mu tafi, sai wani mugun abu ya faru.
Cikin ya zube. Kuma likita ya gaya mana cewa ɗa namiji ne. Abin ya fi shekaru 50 yanzu, amma yana daminmu har wa yau. Ko da yake mun yi bakin ciki sosai don abin da ya faru, mun ci-gaba da yin hidimarmu, don muna son hidimar.
Ni da matata Sheila a Kamaru a 1965
Ana yawan tsananta wa ꞌyanꞌuwa a ƙasar Kamaru don yadda ba sa shiga harkokin siyasa, musamman lokacin zaɓen shugaban ƙasa. Mun yi ta alla-alla kar a hana aikinmu a ƙasar, amma abin da ya faru ke nan a ran 13 ga Mayu, 1970. Gwamnati ta kwace sabon rashen ofishinmu da aka yi wata biyar kawai da buɗewa. Kafin mako ɗaya, an kori dukan masu waꞌazi a ƙasar waje daga ƙasar, har da ni da Sheila. Ba mu so mu bar ꞌyanꞌuwan ba don muna ƙaunar su sosai, kuma mun yi ta damuwa a kan abin da zai iya faruwa da su.
Mun koma yin hidima a ofishinmu da ke Faransa, kuma mun yi wata shida a wurin. Lokacin da nake Faransa, na ci-gaba da yin iya ƙoƙarina in taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu da ke Kamaru. Sai a watan Disamba, aka ce mu je yin hidima a Najeriya. Kuma a lokacin ofishinmu da ke Najeriya ne yake kula da aikin waꞌazinmu a Kamaru. Da muka je Najeriya, ꞌyanꞌuwa sun karɓe mu hannu bibbiyu. Mun yi shekaru da dama muna hidima a wurin, kuma mun ji daɗinsa.
MUN YANKE SHAWARA MAI WUYA
A 1973 mun bukaci mu yanke wata shawara mai wuya sosai. Lokacin Sheila tana fama da rashin lafiya. Da muka je wani babban taro a New York, sai ta fashe da kuka ta ce: “Gaskiya ba zan iya ci-gaba da wannan hidimar ba! Yawancin lokaci ina rashin lafiya kuma hakan yana sa ni yawan gajiya.” Mun yi fiye da shekaru 14 muna hidima tare a Yammacin Afirka, kuma ina alfahari da ita don ƙoƙarin da take yi. Amma yanzu dole mu yi wasu canje-canje. Bayan da muka tattauna kuma muka yi adduꞌa sosai game da batun, sai muka yanke shawarar komawa ƙasar Kanada. Mun san cewa a wurin za ta sami jinya mai inganci. Barin hidimar waꞌazi a ƙasar waje da hidima ta cikakken lokaci ne shawara mafi wuya da muka taɓa yankewa.
Da muka koma Kanada, sai wani abokina mai sayar da motoci a arewacin yankin Toronto, ya ɗauke ni aiki. Sai muka kama hayar gida kuma muka sayo kayan ɗaki. Ba sabbi muka saya ba, amma hakan ya taimaka mana mu ci-gaba da rayuwarmu ba tare da cin bashi ba. Burinmu shi ne mu yi rayuwa mai sauƙi, da fatan cewa wata rana za mu sake koma yin hidima ta cikakken lokaci. Ba da daɗewa ba, abin da muke fata ya faru, kuma mun yi mamaki sosai!
Ga yadda ya faru. Na soma zuwa taimakawa a inda ake gina Majamiꞌar Taro, a wani gari mai suna Norval. Ina zuwa kowane ran Asabar. Daga baya, sai aka mai da ni mai kula da Majamiꞌar Taron. A lokacin, matata Sheila ta soma samun sauƙi, kuma mun ga cewa za mu iya yin aikin nan. Don haka mun koma zama a Majamiꞌar Taron a watan Yuni 1974. Mun yi farin ciki sosai da muka sake soma hidima ta cikakken lokaci!
Wani abin farin cikin shi ne, Sheila ta ci-gaba da samun sauƙi. Bayan shekaru biyu, sai aka ce mu soma yin hidimar mai kula da daꞌira, kuma mun yarda. Daꞌirarmu tana wani yanki mai suna Manitoba a Kanada, kuma ana sanyi sosai a wurin. Amma ƙaunar da ꞌyanꞌuwa suka nuna mana ta sa ba mu mai da hankali ga sanyin ba. Abubuwan nan sun sa mun ga cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne mu ci-gaba da bauta ma Jehobah, ko da a ina ne muke.
NA KOYI WANI DARASI MAI MUHIMMANCI
Bayan da muka yi shekaru muna hidimar masu kula da daꞌira, sai a 1978 aka ce mu soma yin hidima a Bethel da ke nan Kanada. Da muka je, bai daɗe ba sai na koyi wani darasi mai muhimmanci sosai. An ba ni jawabi mai tsawon awa ɗaya da rabi a wani taro na musamman da aka yi a birnin Montreal. Kuma jawabin da Faransanci ne. Abin baƙin cikin shi ne, masu sauraro basu ji daɗin jawabin sosai ba. Daga baya, wani ɗanꞌuwa daga Sashen Kula da Hidima ya ba ni shawara game da hakan. A gaskiya, da a ce na yarda cewa abin da ya faɗa gaskiya ne, da ya fi, don ni ba mai iya ba da jawabi sosai ba ne. Amma ban amince da shawarar da ya ba ni ba. Na yi fushi da ɗanꞌuwan don na ga kamar kushe ni kawai ya yi, maimakon ya ce na ɗan yi ƙoƙari. Kuskuren da na yi shi ne, maimakon in mai da hankali ga abin da ɗanꞌuwan yake gaya min, na mai da hankali ga yadda ya yi maganar, da kuma raꞌayina game da ɗanꞌuwan.
Na koyi wani darasi mai muhimmanci bayan da na yi wani jawabi da Faransanci
Bayan ꞌyan kwanaki, sai wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu ya yi min magana game da batun. Na yarda cewa yadda na amsa wa ɗanꞌuwan bai dace ba, kuma na yi nadama. Bayan haka, sai na koma wurin ɗanꞌuwan da ya ba ni shawarar, na ba shi haƙuri, kuma nan-da-nan ya yafe min. Abin da ya faru ya koya min muhimmancin zama mai sauƙin kai. Ba zan taɓa manta da wannan darasin ba. (K. Mag. 16:18) Na yi adduꞌa sau da yawa game da batun, kuma na ce ba zan sake ƙin shawara ba.
Yanzu na fi shekaru 40 ina hidima a Bethel da ke Kanada. Kuma tun daga 1985, an ba ni damar yin hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu. A watan Fabrairu 2021, matata abin ƙaunata, ta rasu. Ina kewarta sosai. Ban da haka ma, ina fama da nawa rashin lafiya. Amma ayyuka da yawa da nake yi a hidimata ga Jehobah suna sa ni farin ciki sosai, har ‘ba na cika damuwa.’ (M. Wa. 5:20) Ko da yake na gamu da matsaloli iri-iri a rayuwata, farin cikin da na yi ya fi matsalolin da na fuskanta. Cikin shekaru 70 da na yi ina hidima ta cikakken lokaci, Jehobah ya yi min albarka sosai don na sa yin nufinsa farko a rayuwata. Fatana shi ne, ꞌyanꞌuwanmu matasa, maza da mata, su sa yin nufin Jehobah farko a rayuwarsu. Na tabbata cewa idan suka yi hakan, za su yi farin ciki da rayuwa mai gamsarwa. Na san bautar Jehobah ce kaɗai za ta iya sa mutum yi farin ciki kuma ya yi rayuwa mai gamsarwa.
a Ka karanta tarihin Ɗanꞌuwa Marcel Filteau, a talifi mai jigo, “Jehovah Is My Refuge and Strength,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2000.
b A 1957 ne aka soma kiran ƙasar da suna Ghana. Kafin nan, Gold Coast ake kiranta.
c Ka karanta labarin Ɗanꞌuwa Herbert Jennings a talifi mai jigo, “You Do Not Know What Your Life Will Be Tomorrow,” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 2000.
d A lokacin, Ɗanꞌuwa Nathan H. Knorr ne yake ja-gorantar aikinmu.