Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Nuwamba p. 31
  • Abin da Zai Taimaka Mana Mu Yi Nazari Kowane Mako

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Zai Taimaka Mana Mu Yi Nazari Kowane Mako
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ku Hana Kanku Samun Ɗalibai—Yadda Za Mu Yi Nazari da Mutane Ko da Muna da Hidimomi da Yawa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Tsarin Nazari don Kowa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Inganta Yadda Kake Nazari!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Nuwamba p. 31
Wata ꞌyarꞌuwa tana nazari, tana amfani da kwamfuta, da Littafi Mai Tsarki, da kuma karamar takarda don yin rubutu. A nazarinta, tana amfani da wani zane da ya bayyana mulkokin duniya da Daniyel ya annabta; zanen yana a Appendix B9 na juyin “New World Translation.”

Abin da Zai Taimaka Mana Mu Yi Nazari Kowane Mako

YANA yi maka wuya ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kowane mako, ko ka ji daɗin yin sa? Yana faruwa da dukanmu a wasu lokuta. Amma ka yi laꞌakari da wasu abubuwan da muke yi kowane lokaci, kamar wanka da sauransu. Ba kowane lokaci ne yake da sauƙi mutum ya yi wanka ba, amma idan mutum ya yi, yana jin daɗi! Haka ma yake da nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi ƙoƙari muka yi nazari, za mu ji daɗi sosai. (Afis. 5:26) Ga wasu shawarwari da za su iya taimakawa:

  • Ka zaɓi lokaci. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana cikin abubuwa da suka “fi muhimmanci” da bai kamata mu yi watsi da su ba. (Filib. 1:​10, NWT) Idan ba ka so ka riƙa mantawa da lokacin nazarinka, ka rubuta lokacin da ranar da ka zaɓa, kuma ka saka shi a inda za ka riƙa gani da wuri. Za ka iya sa alam a wayarka don ta tunasar da kai kafin lokacin nazarin.

  • Ka yi bisa ga yanayinka. Yaya kake so ka yi nazarin? Alal misali, za ka iya yin nazarin har na awa ɗaya? Ko za ka fi so ka riƙa yinsa kaɗan-kaɗan? Kai ne ka fi sanin wanda zai fi maka. Don haka, ka zaɓi abin da zai dace da yanayinka. Idan lokacin nazarinka ya yi kuma ka ji kamar ba ka so, ka yi ƙoƙari ka yi shi ko na minti goma kawai. Yin nazari na minti goma, ya fi babu. Ƙila bayan minti goman ma, za ka ji daɗinsa har ka ci-gaba.—Filib. 2:13.

  • Ka zaɓi batutuwan da za ka yi nazarinsu. Idan a lokacin da za ka yi nazari ne ka soma neman batutuwan da za ka yi nazarinsu, hakan ba zai sa ka yi “amfani da lokacinka” da kyau ba. (Afis. 5:16) Ka yi ƙoƙari ka rubuta jerin batutuwa da za ka so ka yi nazarinsu. Kuma idan ka sami wani batu da za ka so ka nemi ƙarin haske a kai, sai ka rubuta shi a cikin jerin batutuwan da kake da su. Bayan ka gama nazari ma, ƙila ka ga wasu batutuwa da za ka so ka yi nazari a kai. Su ma ka rubuta su.

  • Za ka iya yin canje-canje. Ka tsara yadda za ka iya yin canje-canje idan da bukata. Hakan zai sa ka iya canja tsawon lokacin da kake yin nazari, ko batutuwan da kake nazari a kai, ko kuma ranar da kake yi nazarin. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka riƙa yin nazarin kowane mako.

Idan muna nazari kowane mako, za mu amfana. Za mu kusaci Jehobah sosai, za mu kasance da hikima, kuma nazarin zai ƙarfafa mu.—Yosh. 1:8.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba