Yadda Yaƙi da Tashin Hankali Suke Shafan Dukanmu
“Tashin hankali yana ta ƙaruwa a faɗin duniya tun lokacin da aka yi Yaƙin Duniya na Biyu. Kuma mutane biliyan 2, wato mutum ɗaya cikin huɗu na mutanen da ke duniya ne suke zama a wuraren da ake tashin hankalin.”
Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed, 26 ga Janairu, 2023.
Yaƙi da tashin hankali za su iya ɓarkewa ba zato ba tsammani a wuraren da ake zaman lafiya. Ko mutanen da ba sa zama a wuraren da ake yaƙi ko tashin hankali ma, hakan zai iya shafan su. Bayan yaƙin, mummunan sakamakon za su iya shafan mutane na dogon lokaci. Ga wasu misalai:
Yaƙi yana jawo ƙarancin abinci. Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, “tashin hankali ne babban abin da ke jawo yunwa, domin kashi 70 na mutanen da suke fama da yunwa a faɗin duniya suna zama a wuraren da ake yaƙi da tashin hankali.”
Yaƙi yana jawo raunuka da matsalar ƙwaƙwalwa. Idan akwai alama za a yi yaƙi a wani wuri, mutane a yankin sukan ji tsoro sosai kuma sukan yi fama da tsananin damuwa. Mutanen da suke zama a wuraren da ake tashin hankali za su iya jin rauni. Ban da haka ma, za su iya fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Abin baƙin ciki shi ne, a yawancin lokaci, ba sa samun kulawar likitoci yadda suke bukata.
Yaƙi yana sa mutane su yi gudun hijira. Hukumar Kula da ꞌYan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zuwa Satumba 2023, mutane fiye da miliyan 114 a faɗin duniya ne aka tilasta musu su gudu su bar gidajensu. Kuma abubuwan da suka fi jawo hakan su ne yaƙi da tashin hankali.
Yaƙi yana jawo matsalar tattalin arziki. A yawancin lokaci, yaƙi yana jawo matsalolin tattalin arziki. Alal misali, abubuwa sukan yi tsada sosai fiye da yadda aka saba. Mutane za su iya shan wahala sosai domin gwamnati tana kashe kuɗaɗe da yawa a kan sojoji da sayan makamai, waɗanda ya kamata ta kashe a kan kiwon lafiya da ilimi. Kuma bayan yaƙin, sake gina wuraren da yaƙi ya lalatar yana cin kuɗaɗe da yawa.
Yaƙi yana ɓata mahalli. Mutane sukan sha wahala sosai saꞌad da aka ɓata mahallinsu. Gurɓataccen ruwa, da iska, da kuma ƙasa za su iya jawo rashin lafiya na dogon lokaci. Ko bayan yaƙin ma, nakiyoyin da aka binne a ƙasa za su iya ji wa mutane rauni ko su kashe su.
Babu shakka, yaƙi yana da muni sosai kuma yana sa mutane su sha wahala ba kaɗan ba.