SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Ka Yi Amfani da Madubin da Kyau
Yakub ya ƙwatanta Littafi Mai Tsarki da madubin da yake sa mu san ainihin yadda muke. (Yak. 1:22-25) Ta yaya za mu yi amfani da wannan madubi, wato Littafi Mai Tsarki da kyau?
Ka karanta shi a hankali. Idan muka kalli madubi da gaggawa, zai yiwu cewa ba za mu ga wasu abubuwan da ya kamata mu gyara ba. Haka ma, idan muna karanta Littafi Mai Tsarki da gaggawa, ba za mu ga abubuwan da ya kamata mu gyara a rayuwarmu ba. Saboda haka, muna bukatar mu karanta shi a hankali.
Ka mai da hankali ga kanka ba wasu ba. Idan muna kallon kanmu a madubi, za mu iya ganin wasu da suke bayanmu. Kuma za mu iya mai da hankali ga abin da bai da kyau a jikinsu. Haka ma, za mu iya karanta Littafi Mai Tsarki kuma mu riƙa ganin kamar wani ne ya kamata ya bi umurnin da ke wurin. Amma idan muka yi hakan, ba za mu iya yin gyaran da muke bukata mu yi ba.
Ka kasance da raꞌayin da ya dace. Idan ka kalli madubi kuma abin da kake gani kawai abubuwa marar kyau ne game da kanka, hakan zai sa ka yi sanyin gwiwa. Don haka, idan kana karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka ga wuraren da kake bukatar ka yi gyara, zai yi kyau ka kasance da raꞌayin da ya dace kuma kada ka ga kamar ya kamata ka yi fiye da abin da Jehobah yake so ka yi.—Zab. 103:14.