TALIFIN NAZARI NA 28
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
Yadda Za Mu Nemi Shawara
“Hikima tana wurin mai neman shawara.”—K. MAG. 13:10.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da za mu yi don mu amfana sosai daga shawarar da aka ba mu.
1. Me zai taimaka mana mu yanke shawara mai kyau kuma mu yi nasara? (Karin Magana 13:10; 15:22)
DUKANMU muna so mu yanke shawarwari masu kyau. Kuma muna fatan cewa za mu yi nasara a kowace shawara da muka yanke. To, mene ne zai taimaka mana? Kalmar Allah ta nuna mana yadda za mu cim ma hakan.—Karanta Karin Magana 13:10; 15:22.
2. Wane alkawari ne Jehobah ya yi mana?
2 Gaskiyar ita ce, babu wanda zai ba mu shawara mafi kyau kamar Ubanmu Jehobah. Saboda haka, muna bukatar mu roƙe shi cikin adduꞌa ya ba mu hikima. Ya yi alkawarin taimaka mana. Ya ce: “Zan ba ka shawara, ba zan cire idona a kanka ba.” (Zab. 32:8) Hakan ya nuna cewa, Jehobah zai ba mu shawarar da muke bukata, kuma zai taimaka mana mu iya bin ta.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A wannan talifin, za mu ga yadda za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa tambayoyi huɗu: (1) Waɗanne halaye ne nake bukata don in amfana daga shawara da kyau? (2) Waye ne zai iya ba ni shawara mai kyau? (3) Ta yaya zan nuna cewa ina bukatar shawara da gaske? (4) Me ya sa zai dace in guji sa wasu su faɗa mini abin da zan yi?
WAƊANNE HALAYE NE MUKE BUKATA DON MU AMFANA DAGA SHAWARA?
4. Idan aka ba mu shawara, waɗanne halaye ne muke bukata don mu amfana daga shawarar?
4 Muna bukatar mu zama masu sanin kasawarmu da kuma sauƙin kai don mu amfana daga shawara mai kyau da aka ba mu. Zai dace mu tuna cewa, ba kome da kome ba ne muka sani. Saboda haka, a wasu lokuta, muna bukatar taimakon wasu don mu iya yanke shawarwari masu kyau. Idan ba mu san kasawarmu ba, kuma mu ba masu sauƙin kai ba ne, Jehobah ba zai iya taimaka mana ba. Kuma ba za mu ga amfanin kowace shawara da muka karanta a Littafi Mai Tsarki ba. (Mik. 6:8; 1 Bit. 5:5) Amma, idan mu masu sauƙin kai ne kuma mun san kasawarmu, za mu yi marmarin ji da kuma bin shawarwarin da muka samu daga Littafi Mai Tsarki.
5. Waɗanne abubuwa ne Sarki Dauda ya cim ma da za su iya sa ya zama mai fahariya?
5 Ka yi laꞌakari da abin da za mu koya daga labarin Sarki Dauda. Ko da yake ya cim ma abubuwa da yawa a rayuwarsa, hakan bai sa shi fahariya ba. Shekaru da yawa kafin ya zama sarki, mutane sun san shi a matsayin mawaƙi da ya ƙware. Har ma an gayyace shi ya zo ya riƙa yi wa sarki waƙa. (1 Sam. 16:18, 19) Bayan Jehobah ya naɗa Dauda sarki, ya ba shi ruhu mai tsarki kuma hakan ya sa ya zama jarumi. (1 Sam. 16:11-13) Mutane suna yaba masa don yadda yake nasara wajen kakkashe maƙiyansu, kamar lokacin da ya kashe gwarzon Filistiyawa mai suna Goliyat. (1 Sam. 17:37, 50; 18:7) Da Dauda mutum mai fahariya ne, da waɗannan abubuwan da ya cim ma sun sa shi ya ga kamar ba ya bukatar shawarar kowa. Amma Dauda mutum ne mai sauƙin kai.
6. Ta yaya muka san cewa Dauda yana karɓan shawara hannu bibbiyu? (Ka kuma duba hoton.)
6 Bayan an naɗa Dauda sarki, ya zaɓi abokan da za su riƙa ba shi shawara. (1 Tar. 27:32-34) Wannan ba abin mamaki ba ne, domin tun kafin ya zama sarki, yana karɓan shawarwari masu kyau da aka ba shi. Ba maza kawai ne suke ba shi shawara ya karɓa ba, har da mata ma. Alal misali, ya karɓi shawarar wata mata mai suna Abigail. Ita matar Nabal ce, mutum mai girman kai, marar godiya, kuma ba ya daraja mutane. Dauda cikin sauƙin kai ya bi shawarar da ta ba shi, kuma hakan ya sa bai yi babban kuskure ba.—1 Sam. 25:2, 3, 21-25, 32-34.
Sarki Dauda ya bi shawarar da Abigail ta ba shi (Ka duba sakin layi na 6)
7. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarin Dauda? (Mai-Waꞌazi 4:13) (Ka kuma duba hotunan.)
7 Za mu iya koyan wasu darussa daga labarin Dauda. Alal misali, idan muna da wata baiwa, ko kuma mu ne muke yi wa wasu ja-goranci, ba zai dace mu ɗauka cewa mun san kome da kome ba. Ko kuma cewa ba ma bukatar shawarar kowa. Kamar Dauda, zai dace mu karɓi shawarwari masu kyau, ko da waye ne ya ba mu. (Karanta Mai-Waꞌazi 4:13.) Idan muka yi hakan, za mu guji yin kuskuren da zai jawo wa mu da ꞌyanꞌuwanmu baƙin ciki.
Zai dace mu kasance da niyyar karɓan shawara mai kyau, ko da waye ne ya ba mu (Ka duba sakin layi na 7)c
WAYE NE ZAI IYA BA MU SHAWARA MAI KYAU?
8. Me ya sa Jonathan ya cancanci ba wa Dauda shawara mai kyau?
8 Akwai wani abu kuma da za mu iya koya daga labarin Dauda. Ya nemi shawara daga waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Jehobah. Amma ba shi ke nan ba. Mutanen da ya nemi shawara daga wurinsu sun fahimci yanayin da yake ciki da kyau. Alal misali, saꞌad da ya bukaci ya san ko zai iya yin sulhu da Sarki Shawulu, ya nemi shawara daga wurin Jonathan, ɗan Shawulu. Me ya sa Jonathan ya cancanci ba wa Dauda shawara mai kyau? Domin yana da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma ya san Shawulu da kyau. (1 Sam. 20:9-13) To, mene ne hakan ya koya mana?
9. Su waye ne za mu iya tuntuɓa don samun shawara mai kyau? Ka ba da misali. (Karin Magana 13:20)
9 Idan muna bukatar shawara, zai dace mu tuntuɓi waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma sun fahimci yanayin da muke ciki da kyau.a (Karanta Karin Magana 13:20.) Alal misali, a ce wani ɗanꞌuwa yana neman wadda zai aura, waye ne zai iya ba shi shawara mai kyau? Abokinsa da bai yi aure ba zai iya ba shi shawara mai kyau, idan ya yi hakan bisa ga ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Amma, ɗanꞌuwan zai fi amfana idan ya nemi shawara daga maꞌaurata da suka manyanta, waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah tare, kuma sun san shi da kyau. Ba kawai yadda zai bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su gaya masa ba, za su gaya masa yadda su ma da kansu suka amfana don yin hakan.
10. Mene ne za mu tattauna yanzu?
10 Mun ga halaye biyu da muke bukatar mu kasance da su don samun shawarwari masu kyau. Mun kuma ga waɗanda za su iya ba mu irin shawarwarin nan. Yanzu bari mu ga yadda za mu nuna cewa muna bukatar shawara da gaske, da kuma dalilin da ya sa zai dace mu guji sa wasu su faɗa mana abin da za mu yi.
TA YAYA ZA MU NUNA CEWA MUNA BUKATAR SHAWARA DA GASKE?
11-12. (a) Wane hali ne ya kamata mu guje wa? (b) Mene ne Sarki Rehoboam ya yi lokacin da ya bukaci ya yanke shawara mai muhimmanci?
11 A wasu lokuta, mutum yakan yi kamar yana neman shawara, alhali, yana neman goyon bayan shawarar da ya riga ya yanke ne. Irin wannan mutum, ba shawara yake nema da gaske ba. Saboda haka, zai dace ya koyi darasi daga abin da ya faru da Sarki Rehoboam.
12 Bayan mutuwar Sarki Sulemanu, ɗansa Rehoboam ne ya gaje shi. A lokacin sarautar Sulemanu, alꞌummar sun ji daɗi sosai, amma sun ga kamar ya sa su aiki da yawa. Don haka, sun roƙi Rehoboam ya rage musu aiki. Rehoboam ya gaya musu cewa su ɗan ba shi lokaci ya yi tunani. Da farko, ya nemi shawara daga wurin tsofaffi da suka taimaki Sulemanu. (1 Sar. 12:2-7) Amma, ya yi banza da shawarar da suka ba shi. Me ya sa ya yi hakan? Mai yiwuwa ya riga ya yanke shawara a kan abin da zai yi. Kuma goyon bayan su ne kawai yake so ya samu. Idan haka ne, ya sami abin da yake nema daga wurin tsaransa. (1 Sar. 12:8-14) Rehoboam ya gaya wa mutanen abin da abokansa suka gaya masa. Hakan ya sa mutane da yawa suka yi tawaye, kuma daga lokacin, Rehoboam ya yi ta fama da matsaloli.—1 Sar. 12:16-19.
13. Ta yaya za mu nuna cewa muna bukatar shawara da gaske?
13 Mene ne za mu iya koya daga abin da ya faru da Rehoboam? Idan muka nemi shawara, zai dace mu nuna cewa muna bukatar shawarar da gaske. Ta yaya za mu yi hakan? Zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin bayan na nemi shawara, ina banza da ita idan ba ta jitu da abin da nake so ba?’
14. Me muke bukatar mu tuna idan aka ba mu shawara? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)
14 Alal misali, a ce wani ɗanꞌuwa ya sami damar yin aiki a wani wuri da za a biya shi albashi mai tsoka. Sai ya nemi shawara daga wurin wani dattijo kafin ya karɓi aikin. Ɗanꞌuwan ya gaya wa dattijon cewa, aikin zai sa ya bar iyalinsa na dogon lokaci. Kuma dattijon ya tuna masa da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa taimaka wa iyalinsa ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah ne ya fi muhimmanci. (Afis. 6:4; 1 Tim. 5:8) A ce ɗanꞌuwan ya ƙi amincewa da abin da dattijon ya faɗa, kuma ya ci gaba da tambayar wasu ꞌyanꞌuwa raꞌayinsu game da batun. Har wani ya gaya masa cewa zai iya karɓan aikin. Shin, wannan ɗanꞌuwan yana neman shawara da gaske ne, ko kawai yana neman waɗanda za su goyi bayan shawarar da ya riga ya yanke? Zai dace mu tuna cewa, zuciyarmu za ta iya ruɗin mu. (Irm. 17:9) A wasu lokuta, shawarar da muke ganin ta yi wani iri, ita ce shawarar da muka fi bukata.
Shawara ne muke nema da gaske, ko muna neman wanda zai goyi bayanmu ne kawai? (Ka duba sakin layi na 14)
SHIN, ZAI DACE MU SA WASU SU FAƊA MANA ABIN DA ZA MU YI?
15. Mene ne muke bukatar mu guje wa, kuma me ya sa?
15 Jehobah yana so kowannenmu ya riƙa yanke wa kansa shawara. (Gal. 6:4, 5) Kamar yadda muka tattauna, Littafi Mai Tsarki, da Kiristocin da suka manyanta, za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Amma, ba zai dace mu sa wasu su gaya mana abin da za mu yi ba. Wasu za su iya tambayar wani kai tsaye cewa, “Idan kai ne, me za ka yi a yanayin nan?” Wasu kuma za su bi raꞌayin wasu ba tare da sun yi tunani a kai ba.
16. Wace shawara ce ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar da ke Korinti suke bukatar su yanke game da nama? (1 Korintiyawa 8:7; 10:25, 26)
16 Bari mu yi laꞌakari da abin da ya faru da ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar da ke Korinti a ƙarni na farko. A lokacin, akan sayar da naman da mai yiwuwa an miƙa wa gumaka. Saboda haka, sun bukaci su yanke shawara ko za su ci ko aꞌa. Game da wannan batun, Bulus ya gaya musu cewa: “Mun sani cewa, a duk duniyar nan, gunki ba a bakin kome yake ba, mun kuma san cewa Allah ɗaya ne, babu wani.” (1 Kor. 8:4) Wannan abin da Bulus ya faɗa, ya sa wasu suka yanke shawara cewa, za su iya cin naman da suka saya a kasuwa da mai yiwuwa an miƙa wa gumaka. Wasu kuma sun yanke shawara cewa ba za su iya ci ba, don kada zuciyarsu ta dame su. (Karanta 1 Korintiyawa 8:7; 10:25, 26.) A irin wannan yanayin, kowane mutum ne zai zaɓi abin da zai yi. Bulus bai gaya musu su yanke wa wasu shawarar ba, ko kuma su bi abin da wasu suke yi kawai ba. Kowane mutum ne “zai ba da lissafin rayuwarsa ga Allah.”—Rom. 14:10-12.
17. Me zai iya faruwa idan muka bi abin da wasu suka zaɓa ido a rufe? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)
17 Ta yaya irin wannan abin zai iya faruwa a yau? Bari mu yi laꞌakari da batun amfani da sinadaran jini. Kowanne Kirista ne zai yanke shawara ko zai yi amfani da sinadaran ko aꞌa.b Mai yiwuwa, zai iya yi mana wuya mu fahimci yadda aka ɗauko sinadaran nan, da kuma yadda ake amfani da su. Duk da haka, mu da kanmu ne za mu zaɓa abin da za mu yi. (Rom. 14:4) Idan muka bi abin da wasu suka zaɓa ba tare da yin tunani ba, hakan ba zai nuna cewa muna da hikima ba. Amma za mu zama masu hikima idan muka yanke shawarwari bisa ga ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. (Ibran. 5:14) To, a wane lokaci ne muke bukatar mu nemi shawara daga wurin ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ta manyanta? Za mu yi hakan ne bayan mun yi bincike da kanmu, amma har ila, ba mu gane da kyau yadda ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana a yanayin da muke ciki ba.
Zai dace mu nemi shawara bayan mun yi namu bincike (Ka duba sakin layi na 17)
MU CI GABA DA NEMAN SHAWARA
18. Mene ne Jehobah ya ba mu?
18 Yanke shawarwari da kanmu, babban gata ne daga wurin Jehobah. Ya ba mu Littafi Mai Tsarki, kuma ya ba mu abokai da za su taimaka mana mu san yadda za mu yi amfani da ƙaꞌidodin da ke ciki. Ta hakan, Jehobah ya nuna cewa shi Uba ne da yake ƙaunar mu sosai. (K. Mag. 3:21-23) Me za mu yi don mu nuna masa cewa muna godiya?
19. Me za mu yi don mu ci gaba da sa Jehobah farin ciki?
19 Idan yara suka yi girma, suna bauta wa Jehobah, kuma suna taimaka wa mutane, iyayensu suna farin ciki sosai. Haka ma, Jehobah yana farin ciki sosai idan muka zama Kiristocin da suka manyanta, muna neman shawara daga wurin ꞌyanꞌuwanmu, kuma muna yanke shawarwari da suka nuna cewa muna ƙaunar sa.
WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama
a A wasu lokuta, Kirista zai iya neman shawara daga wurin waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Kamar a batun kuɗi, da kiwon lafiya, da kuma wasu batutuwa.
b Don samun ƙarin bayani game da wannan batun, ka duba littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, darasi na 39 batu na 5 da kuma sashen “Ka Bincika.”
c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo yana yi wa wani dattijo magana don abin da ya yi a taron dattawa.