TARIHI
‘Yaƙin Na Jehobah Ne’
A RAN 28 ga Janairu, 2010, ina Strasbourg, wani birni mai kyau sosai a ƙasar Faransa. Amma ba yawon buɗe ido ne ya kai ni wurin ba. Ina ɗaya daga cikin lauyoyin da suka je kāre ꞌyancin Shaidun Jehobah a Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYanꞌadam. Gwamnatin Faransa ta ce tana bin Shaidun Jehobah bashin kuɗin haraji dala miliyan 89. Don haka, mun je don mu nuna cewa hakan ba gaskiya ba ne. Amma ba yawan kuɗin ba ne ya fi daminmu ba, abin da ya fi daminmu shi ne, kada a ɓata sunan Jehobah da mutanensa, kuma a bar su su yi ibadarsu a sake. Abin da ya faru a wurin ya tabbatar mana cewa ‘yaƙin na Jehobah ne.’ (1 Sam. 17:47) Bari in ba ku labarin.
A 1999, gwamnatin Faransa ta ce ofishinmu da ke ƙasar tana bukatar ta biya kuɗin haraji don gudummawar da ta karɓa daga shekara ta 1993 zuwa 1996. Da muka kai ƙara a kotuna da ke Faransa, sun yi watsi da bukatarmu. Sai muka ɗaukaka ƙara, amma har ila ba a biya bukatarmu ba. Ƙari ga haka, gwamnatin ta ɗauki dala miliyan 6,300,000 daga asusun bankin reshen ofishinmu. Damar da ta rage mana kawai ita ce mu kai ƙara Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYanꞌadam, kuma abin da muka yi ke nan. Amma kafin Kotun ta saurare mu, ta ce mu haɗu da wasu lauyoyin gwamnatin Faransa tare da wata wakiliyar Kotun don a ga ko za a iya sasanta mu.
Mun yi tsammanin cewa wakiliyar za ta ce mana mu ba wa gwamnatin Faransa wasu kuɗaɗe a cikin kuɗin. Amma mun gano cewa idan muka ba wa gwamnatin wani abu, hakan zai saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. ꞌYanꞌuwa sun ba da gudummawar ne domin su tallafa wa aikin da ƙungiyarmu ke yi, don haka bai kamata a ba wa gwamnati gudummawarsu ba. (Mat. 22:21) Duk da haka, mun halarci taron don mu nuna cewa mun daraja Kotun.
Ni da wasu lauyoyi a gaban Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYanꞌadam, a 2010
Mun taru a wani babban ɗaki na Kotun da ya haɗu sosai. Nan da nan, wakiliyar Kotun ta ce, zai dace Shaidun Jehobah su biya wasu kuɗaɗen haraji da ƙasar Faransa ta ce su bayar. Sai muka tambaye ta, “Kin san cewa gwamnatin Faransa ta riga ta karɓi dalla miliyan 6,300,000 daga asusun bankinmu?”
Mun ga cewa abin ya ba ta mamaki sosai. Da lauyoyin gwamnatin Faransa sun tabbatar cewa sun yi hakan, sai ta canja yadda take bi da batun. Ta ɓata rai, kuma ta yi musu faɗa, sai ta kammala taron a tāke. Na gano cewa Jehobah ne ya canja kome da kome don mu yi nasara. Mun yi farin ciki sosai da muka bar wurin, kuma abin da ya faru ya ba mu mamaki ba kaɗan ba.
A ran 30 ga Yuni, 2011, Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYanꞌadam ya wanke sunanmu daga zargi. Ya ce ba ma bukatar mu biya kuɗin haraji, kuma ya ce wa gwamnatin ta mayar mana da kuɗinmu har da ƙari! Abin da ya faru yana kan taimakon mu a ƙasar Faransa har wa yau. Tambayar nan da ba mu ma shirya yin sa ba, ta zama kamar dutsen da ya kashe Goliyat, kuma ta taimaka mana mu yi nasara. Amma mene ne ainihin abin da ya sa muka yi nasara? Kamar yadda Dauda ya gaya wa Goliyat, ‘yaƙin na Jehobah ne.’—1 Sam. 17:45-47.
Ba a wannan ƙaro ne kawai muka yi nasara a kotu ba. Duk da cewa, gwamnati masu iko sosai tare da addinai suna tsananta mana, mun samu nasarori 1,225 a manyan kotu na ƙasashe 70, da kotuna na ƙasa da ƙasa. Nasarorin nan suna kāre ꞌyancinmu, kamar ꞌyancin da muke da shi na gudanar da ayyukan ibadarmu, da yin waꞌazi a wuraren da akwai jamaꞌa, da ƙin yin bukukuwa da ke ɗaukaka ƙasa, da kuma ƙin karɓan jini.
Bari in gaya muku abin da ya kai ni kāre ꞌyancinmu a Turai, duk da cewa ina hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah da ke New York, a ƙasar Amurka.
IYAYENA SUN KOYA MINI YADDA ZAN YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Mahaifina mai suna George da mahaifiyata mai suna Lucille, sun sauƙe karatu a aji na 12 na makarantar Gilead, kuma suna hidima a ƙasar Itiyofiya saꞌad da aka haife ni a 1956. Sun ba ni suna Philip, domin in zama takwarar Filibus mai waꞌazi da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. (A. M. 21:8) Shekara ɗaya bayan hakan, gwamnati ta hana aikinmu a ƙasar. Duk da cewa ni ɗan yaro ne, na tuna cewa muna ibada a ɓoye ne. A lokacin, hakan ya burge ni! Amma abin baƙin cikin shi ne, hukumomi sun kore mu daga ƙasar a 1960.
Lokacin da Ɗanꞌuwa Nathan H. Knorr (a can gefen hagu) ya ziyarce mu a Addis Ababa a ƙasar Itiyofiya, a 1959
Sai muka ƙaura zuwa Wichita, da ke birnin Kansas, a ƙasar Amurka. Amma iyayena ba su daina waꞌazi da ƙwazo kamar yadda suka yi a ƙasar waje ba. Sun koya wa ni da yayata, Judy, da ƙanina, Leslie, yadda za mu ƙaunaci Jehobah kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Kuma an haife mu duka a ƙasar Itiyofiya ne. Na yi baftisma ina shekara 13. Shekaru uku bayan hakan, iyalinmu sun ƙaura zuwa Arequipa a ƙasar Peru, domin ana bukatar masu shela a wurin.
A 1974 saꞌad da nake shekara 18, ofishinmu na Peru sun tura ni da wasu ꞌyanꞌuwa huɗu mu je mu yi hidimar majagaba na musamman. Wurin da aka tura mu, ba a taɓa yin waꞌazi a wurin ba, sunan wurin Central Andes Mountains ne. Mun yi wa mutane waꞌazi har da waɗanda ke yaren Quechua da Aymara. Muna tafiya a cikin wata mota da ke kama da akwati, kuma a ciki ne muke kwana. Nakan yi farin ciki sosai idan na tuna da yadda muka nuna wa mutanen garin alkawuran da Jehobah ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki, da suka nuna cewa nan ba da daɗewa ba zai kawar da talauci, da cututtuka, da kuma mutuwa. (R. Yar. 21:3, 4) Kuma mutane da yawa a wurin sun soma bauta wa Jehobah.
Motar tafi da gidanka a 1974
NA SOMA HIDIMA A HEDKWATARMU
A lokacin da Albert Schroeder, mamban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ziyarci ƙasar Peru a 1977, ya ƙarfafa ni in cika fom na yin hidima a hedkwatarmu. Kuma na yi hakan. Nan ba da daɗewa ba, a ran 17 ga Yuni, 1977, na soma hidima a Bethel na Brooklyn. Na yi shekaru huɗu ina aiki a sashen share-share da gyare-gyare.
Ranar aurenmu, a 1979
A watan Yuni 1978, na haɗu da Elizabeth Avallone a wani taro na ƙasa da ƙasa da aka yi a New Orleans, Louisiana. Iyayenta masu ibada ne sosai kamar nawa. A lokacin da muka haɗu, ta riga ta yi hidimar majagaba na shekara huɗu, kuma tana so ta yi amfani da rayuwarta ta ci gaba da hidima ta cikakken lokaci. Mun ci gaba da magana. A kwana a tashi, sai muka soma soyayya. Mun yi aure a ran 20 ga Oktoba, 1979, kuma mun soma hidima a Bethel tare.
ꞌYanꞌuwa da muka haɗu da su a ikilisiyarmu na farko, wato Brooklyn Spanish, sun ƙaunace mu sosai. Ban da ikilisiyar, mun kasance a ikilisiyoyi uku, kuma dukansu sun taimaka mana mu ci gaba da hidimarmu a Bethel. Muna godiya sosai don taimakonsu da kuma yadda abokanmu da ꞌyanꞌuwanmu suka taimaka mana wajen kula da iyayenmu da suka tsufa.
ꞌYanꞌuwa da ke hidima a Bethel da suke Ikilisiyar Brooklyn Spanish, a 1986
YADDA NA YI HIDIMA A SASHEN DA KE KULA DA SHARIꞌA
A watan Janairu 1982, an ce in yi hidima a Sashen da Ke Kula da Shariꞌa a Bethel, kuma hakan ya ba ni mamaki sosai. Bayan shekaru uku, an tura ni karatu a jamiꞌa don in zama lauya. Na koyi cewa nasarori da yawa da Shaidun Jehobah suka samu a kotu sun taimaka wa mutane da yawa a ƙasar Amurka da wasu ƙasashe su sami ꞌyancin yin abubuwa da dama. Mun tattauna game da nasarorin nan sosai a makaranta.
A 1986 saꞌad da nake shekara 30, na zama mai kula da Sashen Shariꞌa. Na yi farin ciki sosai da aka damƙa min wannan babban aiki duk da shekaruna, amma na ji tsoro don akwai abubuwa da yawa da ban sani ba.
Na zama lauya a 1988, amma ban san cewa makarantar da na yi ya soma shafan dangantakata da Jehobah ba. Makarantar jamiꞌa zai iya sa mutum ya so samun matsayi, kuma zai sa ya ji kamar ya fi mutanen da ba su je makaranta ba. Matata ce ta taimaka mini. Ta taimaka min in mai da hankali ga abubuwan da nake yi don in ƙarfafa dangantakata da Jehobah kafin in je makarantar. A kwana a tashi, na ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Abin da ya faru da ni ya koya min cewa ba samun ilimi ne ya fi muhimmanci a rayuwa ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu.
KĀRE LABARIN NAN MAI DAƊI WANDA NA TABBATAR DA SHI A KOTU
Bayan da na gama makaranta, sai na soma mai da hankali ga kula da batutuwan shariꞌa a Bethel, da kuma kāre ꞌyancin da muke da shi na yin waꞌazi. Na ji daɗin aikina sosai, amma ban same shi da sauƙi ba domin abubuwa suna canjawa da sauri a ƙungiyarmu. Alal misali, a dā muna sayar da takardunmu, amma daga 1991, an ce Sashen da Ke Kula da Shariꞌa ya taimaka wajen ba da umurni a kan yadda za a daina sayar da takardun. Kuma bayan haka, Shaidun Jehobah sun soma ba da takardunsu kyauta. Hakan ya sauƙaƙa ayyuka a Bethel da kuma a ikilisiyoyi, kuma ya sa mun daina samun matsalolin biyan haraji. Wasu sun ɗauka cewa wannan canjin zai sa ba za mu sami isasshen kuɗi don mu ci gaba da buga littattafai ba, kuma zai hana mutane da yawa bauta wa Jehobah. A maimakon haka, adadin mutanen da ke bauta wa Jehobah tun 1990 ya yi ninki ba ninki, kuma a yau mutane za su iya karanta littattafanmu ba tare da sun biya kome ba. Wannan ya koya min cewa, canje-canjen da ƙungiyarmu take yi na samun nasara ne domin Jehobah yana taimaka mana, kuma yana mana ja-goranci ta wurin bawa mai aminci.—Fit. 15:2; Mat. 24:45.
Ba don muna da ƙwararrun lauyoyi ne kawai ya sa muke yin nasara a kotu ba. A yawancin lokuta, halayen Shaidun Jehobah ne ke sa mu yi nasara. Na ga misalin hakan a 1998, lokacin da mambobi uku na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da matansu suka je taron yanki na musamman a Cuba. Yadda suka nuna alheri da ban girma ya tabbatar wa hukumomin gwamnati cewa babu ruwanmu da harkokin siyasa, ko da yake mun daɗe muna bayyana musu hakan, amma sun ƙi ji.
A wasu lokuta, a kotu ne kawai za mu iya ‘kāre labarin nan mai daɗi wanda mun tabbatar da shi’. (Filib. 1:7) Alal misali, mun ɗau shekaru da yawa muna ƙoƙari mu bayyana wa hukumomin Turai da na Koriya ta Kudu cewa su ba mu ꞌyancin yin aiki da ba na soja ba. Kuma hakan ya sa ꞌyanꞌuwa 18,000 a Turai, da 19,000 a Koriya ta Kudu sun je kurkuku, domin sun ƙi yin aikin soja.
A ƙarshe, ran 7 ga Yuli, 2011, Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYanꞌadam ya yanke hukuncin da ake kira Bayatyan v. Armenia cewa wajibi ne ƙasashen Turai su ba wa duk wanda ba ya so ya yi aikin soja don imaninsa wani aiki dabam. Kuma irin hukuncin da wata babban kotu a Koriya ta Kudu ta yanke ke nan ran 28 ga Yuni, 2018. Da a ce wasu ꞌyanꞌuwanmu ba su riƙe aminci ba, da ba mu yi nasara ba.
Sashen da Ke Kula da Shariꞌa a hedkwatarmu da kuma waɗanda suke ofisoshin reshenmu a faɗin duniya suna aiki tuƙuru wajen kāre ꞌyancinmu na ibada da kuma yin waꞌazi. Muna farin ciki cewa muna kāre ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da hukumomin gwamnati suna tsananta musu. Ko da ba mu yi nasara a kotu ba, mun san cewa muna ba da shaida ga gwamnoni da sarakuna da kuma alꞌummai. (Mat. 10:18) Alkalai, da wakilan gwamnati, da masu wasa labarai, da ma alꞌumma gabaki ɗaya, suna duba nassosin da muke sakawa a takardun da muke kaiwa kotu, da waɗanda muke amfani da su idan ana shariꞌa. Ta hakan, wasu masu zuciyar kirki sukan koyi abubuwa game da Shaidun Jehobah da abin da suka yi imani da shi. Har ma wasun su sun zama Shaidun Jehobah.
NA GODE MAKA, JEHOBAH!
A cikin shekaru 40 da suka wuce, na sami gatan yin aiki tare da ofisoshinmu a faɗin duniya, da zuwa manyan kotuna, da kuma haɗuwa da manyan hukumomin gwamnati. Ina ƙauna da kuma alfahari da ꞌyanꞌuwan da nake aiki da su a Sashen da Ke Kula da Shariꞌa a hedkwatarmu, da kuma na ofisoshinmu a faɗin duniya. Rayuwata na cike da albarku, kuma na cim ma abubuwa da yawa a ƙungiyar Jehobah.
Matata ta ƙaunace ni sosai kuma ta taimaka min na tsawon shekaru 45 da muke tare, a lokacin da muke jin daɗi da kuma lokacin da muke shan wahala. Ina alfahari da ita sosai domin ta yi hakan duk da cewa tana fama da wata cuta da ke ƙarya garkuwar jiki.
Mun gano cewa ba iyawarmu ne ke sa mu sami ƙarfi ko nasara ba. Kamar yadda Dauda ya ce, “Yahweh ne ƙarfin mutanensa.” (Zab. 28:8) Babu shakka, ‘yaƙin na Jehobah ne.’