TALIFIN NAZARI NA 37
WAƘA TA 114 Ku Kasance Masu “Haƙuri”
Abin da Za Ka Yi Idan Ka Ga Ana Rashin Adalci
“Ya sa zuciya ga shariꞌar gaskiya, sai ga zalunci.”—ISHA. 5:7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da Yesu ya yi saꞌad da ya ga ana yi ma wasu rashin adalci, za mu kuma ga yadda za mu yi koyi da shi.
1-2. Mene ne mutane da yawa suke yi idan suka ga ana rashin adalci ko ana wulaƙanta mutane, kuma wane irin tunani ne hakan zai iya sa mu yi?
A YAU, ana yi wa mutane da yawa rashin adalci. Ana yi musu hakan ne domin su talakawa ne, ko don inda suka fito, ko don kamanninsu, da dai sauransu. Wasu kuma suna shan wahala domin ꞌyan kasuwa masu kuɗi da shugabannin gwamnati sun damu ne kawai da yadda za su samu kuɗi. Irin waɗannan abubuwan suna iya jefa mu ko waɗanda muka sani cikin wahala.
2 Mutane da yawa suna fushi domin an wulaƙanta su ko kuma wasu mutane. Babu wanda ba ya son zaman lafiya, kuma ba wanda ba ya son a daraja shi. Wasu suna ƙoƙarin magance rashin adalci ko wulaƙancin da suke gani a duniya. Suna yin hakan ta wurin yin zanga-zanga, ko goyon bayan ꞌyan siyasa da suka yi alkawari cewa za su yaƙi rashin adalci. Amma, an koya mana cewa mu “ba na duniya ba ne,” da kuma cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance rashin adalcin da muke gani a yau. (Yoh. 17:16) Duk da haka, idan muka ga ana wulaƙanta mutane muna baƙin ciki, har ma ranmu ya ɓace. Kuma hakan zai iya sa mu yi tunani mu ce: ‘Me ya kamata in yi? Akwai abin da zan iya yi a yanzu don rashin adalcin da ake yi?’ Don mu iya amsa tambayoyin nan, bari mu ga yadda Jehobah da Yesu suke ji game da rashin adalcin da ake yi.
JEHOBAH DA YESU SUN TSANI RASHIN ADALCI
3. Me ya sa mukan damu idan aka yi mana rashin adalci? (Ishaya 5:7)
3 Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana dalilin da ya sa mukan damu idan aka yi mana rashin adalci, ko kuma aka yi wa wasu. Hakan yana faruwa ne domin Jehobah ya halicce mu yadda za mu yi koyi da shi. Kuma shi mai “adalci da gaskiya” ne. (Zab. 33:5; Far. 1:26) Ba ya wulaƙanta kowa, kuma ba ya son wani ma ya wulaƙanta kowa! (M. Sha. 32:3, 4; Mik. 6:8; Zak. 7:9) Alal misali, a lokacin annabi Ishaya, Jehobah ya ji “kukan wahala” da Israꞌilawa suka yi don wulaƙancin da suka sha daga wurin ꞌyanꞌuwansu. (Karanta Ishaya 5:7.) Jehobah ya hukunta waɗanda suka ƙi su bi abin da ya faɗa kuma suka ci-gaba da wulaƙanta mutane.—Isha. 5:5, 13.
4. Yaya Yesu yake ji idan aka yi ma wani rashin adalci? (Ka kuma duba hoton.)
4 Kamar Jehobah, Yesu yana son adalci kuma ya tsani rashin adalci. Akwai ranar da Yesu ya ga wani mutum mai shanyayyen hannu. Ya tausaya masa, kuma ya warkar da shi. Amma da shugabannin addinin Yahudawa suka ga hakan, sai ransu ya ɓace sosai. Abin da ya fi damun su shi ne, a ganinsu Yesu yana karya dokar ranar Assabaci. Ba su ma damu da cewa mutumin ya warke, kuma ya daina shan wahala ba. Yaya Yesu ya ji don halin nan da suka nuna? Ya yi “baƙin ciki domin taurin zuciyarsu.”—Mar. 3:1-6.
Shugabannin addinin Yahudawa a zamanin Yesu ba sa tausaya wa mutane, amma Yesu ya ƙaunaci mutane kuma ya taimaka musu (Ka duba sakin layi na 4)
5. Me ya sa ya kamata mu yi hattara idan muna fushi don rashin adalcin da muke gani?
5 Jehobah da Yesu ba sa jin daɗi idan suka ga ana yi wa mutane rashin adalci. Saboda haka, ba laifi ba ne idan mu ma ba mu ji daɗi ba. (Afis. 4:26) Amma, wajibi ne mu yi hattara kuma mu tuna cewa ba za mu iya dakatar da wahalar da mutane suke sha ba. Ban da haka ma, idan mun ci-gaba da yin fushi na dogon lokaci, hakan zai iya jawo mana rashin lafiya, ko kuma mu soma baƙin ciki mai tsanani. (Zab. 37:1, 8; Yak. 1:20) To, me ya kamata mu yi idan ana wulaƙanta mu, ko kuma ana wulaƙanta wasu? Misalin Yesu zai taimaka mana sosai.
YADDA YESU YA BI DA RASHIN ADALCI
6. Waɗanne rashin adalci ne ake yi wa mutane a lokacin da Yesu yake duniya? (Ka kuma duba hoton.)
6 Saꞌad da Yesu yake duniya, ya ga yadda ake yi wa mutane da yawa rashin adalci. Ya ga yadda shugabannin addinai suke wulaƙanta talakawa. (Mat. 23:2-4) Ya kuma ga yadda hukumomin Roma suke wulaƙanta mutane. Yahudawa da yawa sun yi ƙoƙari su ga sun samu ꞌyanci daga ƙarƙashin mulkin Roma. Wasu ma sun kafa ƙungiyoyi don su yaƙi Romawa. Amma, Yesu bai kafa ko ya goyi bayan irin waɗannan ƙungiyoyin ba. Saꞌad da ya ji cewa mutane suna so su zo su naɗa shi sarki, ya bar wurin.—Yoh. 6:15.
Saꞌad da mutane suka so su naɗa Yesu ya zama sarki, ya bar wurin (Ka duba sakin layi na 6)
7-8. Me ya sa Yesu bai yi ƙoƙarin kawo ƙarshen rashin adalci lokacin da yake duniya ba? (Yohanna 18:36)
7 A lokacin da Yesu yake duniya, bai saka hannu a harkokin siyasa da niyyar cewa hakan zai magance rashin adalcin da yake gani ba. Me ya sa? Ya san cewa ba ɗanadam da yake da iko, ko ya cancanci ya yi mulki bisa mutane. (Zab. 146:3; Irm. 10:23) Ban da haka ma, ba za su iya cire ainihin dalilin da ya sa mutane suke fama da rashin adalci ba. Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar. Shi mugu ne sosai, kuma mutane da yawa suna koyi da shi. (Yoh. 8:44; Afis. 2:2) Ƙari ga haka, ko mutanen kirki ma ba za su iya magance matsalolin da ake fama da su a duniya ba, domin a wasu lokuta ajizanci yakan sa su ma su yi rashin adalci.—M. Wa. 7:20.
8 Yesu ya san cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya cire ainihin abin da ke jawo rashin adalci. Shi ya sa a lokacin, ya yi iya ƙoƙarinsa “yana waꞌazi da shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah.” (Luk. 8:1) Ta hakan, ya ƙarfafa mutanen da suke so su ga ƙarshen rashin adalci da ake fama da shi. (Mat. 5:6; Luk. 18:7, 8) Babu mulkin ɗanadam da zai iya yin waɗannan abubuwan, Mulkin Allah ne kaɗai zai iya yin hakan domin Mulkin ba irin na wannan duniyar ba ne.—Karanta Yohanna 18:36.
KA YI KOYI DA YESU IDAN KA GA RASHIN ADALCI
9. Me ya tabbatar maka cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshen rashin adalci?
9 Muna rayuwa a kwanakin ƙarshe na wannan duniyar. Saboda haka, mutane suna shan wahala sosai fiye da yadda yake a lokacin da Yesu yake duniya. Amma, kamar yadda yake a lokacin, Shaiɗan da mugayen mutane ne suke jawo wahalolin da ake sha. (2 Tim. 3:1-5, 13; R. Yar. 12:12) Kamar Yesu, mun san cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai kowa ƙarshen ainihin abin da ke jawo rashin adalci, wato, Shaiɗan da dukan mugayen mutane. Da yake muna goyon bayan Mulkin Allah, ba ma zanga-zanga, ko kuma mu goyi bayan wata gwamnati da niyyar cewa ita ce za ta kawo ƙarshen rashin adalci. Ka yi laꞌakari da labarin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Stacy.a Kafin ta soma bauta wa Jehobah, tana yawan fita zanga-zanga da ake yi don rashin adalci. Amma ta soma shakka ko abin da take yi daidai ne. Ta ce: “Idan mun fita zanga-zanga, nakan yi tunani in ce, ‘anya ba ɓata lokacina kawai nake yi ba?’ Amma yanzu, ina da tabbaci cewa Mulkin Allah ne zai kawo ƙarshen dukan matsalolinmu. Na san cewa Jehobah zai iya taimaka wa duk wanda aka yi wa rashin adalci, amma ni ba zan iya ba.”—Zab. 72:1, 4.
10. Bisa ga Matiyu 5:43-48, me ya sa ba ma ƙoƙarin canja dokoki ko sauya gwamnati? (Ka kuma duba hoton.)
10 Mutane da yawa a yau suna shigan ƙungiyoyi da suke ƙoƙarin sauya gwamnati. Amma da shigewar lokaci, da yawa daga cikinsu sukan soma fushi sosai, har ma su daina bin doka ko kuma su ji wa mutane rauni. Kuma hakan bai jitu da abin da Yesu ya koya mana ba. (Afis. 4:31) Wani ɗanꞌuwa mai suna Jeffrey ya ce: “Idan mutane suna zanga-zanga, kafin a ce kwabo, yanayin zai iya lalacewa har a soma faɗa da sace-sace.” Amma, Yesu ya koya mana cewa mu riƙa ƙaunar dukan mutane har da waɗanda ba sa yarda da mu, ko suna tsananta mana. (Karanta Matiyu 5:43-48.) A matsayinmu na Kiristoci, muna iya ƙoƙarinmu mu guji duk wani abin da bai jitu da abin da Yesu ya koya mana ba.
Muna bukatar ƙarfin zuciya don kada mu sa hannu a harkokin duniyar nan (Ka duba sakin layi na 10)
11. Me ya sa zai iya yi mana wuya a wasu lokuta mu yi koyi da Yesu?
11 Ko da yake mun san cewa Mulkin Allah zai kawo ƙarshen rashin adalci kwata-kwata, zai iya yi mana wuya mu bi misalin Yesu idan mu da kanmu ne aka yi wa rashin adalcin. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Janiya ke nan saꞌad da wasu suka wulaƙanta ta don launin fatarta. Ta ce: “Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai, na yi fushi, kuma na so a hukunta waɗanda suka wulaƙanta ni. Na soma tunanin yadda zan goyi bayan wasu masu zanga-zangar adawa da wariyar launin fata. Kuma na ga kamar yin hakan hanya ce mai kyau na nuna ɓacin raina.” Amma da shigewar lokaci, Janiya ta ga cewa tana bukatar ta canja raꞌayinta. Ta daɗa da cewa: “Na ga cewa maimakon in dogara ga Jehobah, na soma dogara ga mutane, da abin da suke faɗa. Don haka, sai na daina maꞌamala da ƙungiyar.” Ko da yake ba ma jin daɗi idan aka yi mana ko wasu rashin adalci, muna bukatar mu kame kanmu don kar mu yi fushi fiye da kima. Kuma a kowane lokaci mu kasance ba na duniya ba.—Yoh. 15:19.
12. Me ya sa ya kamata mu yi laꞌakari da abubuwan da muke karantawa, ko saurarawa, ko kuma kallo?
12 Me zai taimaka mana mu kame kanmu idan muka ga ana rashin adalci? Wani abin da zai taimaka mana shi ne yin laꞌakari da abubuwan da muke karantawa, da saurara, da kuma kallo. Ana ba da wasu labarai a dandalin sada zumunta yadda za su ba wa mutane mamaki kuma su so su yi wa gwamnati tawaye. A yawancin lokuta, ƙafafun yaɗa labarai suna yaɗa raꞌayinsu ne kawai maimakon ainihin abin da ya faru. Amma tambayar ita ce, ko da abin da suke faɗa gaskiya ne, mai da hankali a kai zai taimaka mana kuwa? Idan muna yawan sauraron ko kallon irin waɗannan labaran, hakan zai iya tayar mana da hankali, ya sa mu baƙin ciki ko kuma fushi. (K. Mag. 24:10) Ban da haka ma, za mu daina mai da hankali ga ainihin abin da zai kawo ƙarshen matsalolin nan, wato, Mulkin Allah.
13. Ta yaya karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana zai taimaka mana idan muka ga ana rashin adalci?
13 Karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, da yin tunani a kan abin da muka karanta, za su taimaka mana mu san abin da za mu yi idan muka ga ana rashin adalci. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Alia ta damu ainun saꞌad da ta ga yadda ake wulaƙanta mutane da ke yankinsu. Kuma ta ga kamar ba a hukunta waɗanda suke wulaƙanta su. Ta ce: “Na gane cewa ina bukatar in canja yadda nake tunani idan na gaskata cewa Jehobah ne zai iya magance waɗannan matsalolin. A lokacin ne na karanta Ayuba 34:22-29. Ayoyin sun tuna mini cewa Jehobah yana ganin komen da ke faruwa. Shi kaɗai ne ya san yadda zai kwato hakkin kowane mutum, kuma shi kaɗai ne zai iya magance dukan matsalolinmu.” Amma yayin da muke jiran Mulkin Allah ya zo ya magance dukan matsalolinmu, mene ne za mu iya yi yanzu?
MENE NE ZA MU IYA YI YANZU?
14. Wane abu ne za mu yi don kada mu ma mu soma yin rashin adalci? (Kolosiyawa 3:10, 11)
14 Ba za mu iya canja yadda wasu suke wulaƙanta mutane ba, amma za mu iya tabbata cewa mu da kanmu muna daraja mutane. Kamar yadda muka koya, zai dace mu bi misalin Yesu ta wajen ƙaunar mutane. Hakan zai sa mu yi wa kowa alheri har da waɗanda suke tsananta mana ko wulaƙanta mu. (Mat. 7:12; Rom. 12:17) Jehobah yana farin ciki idan muna yi wa kowa alheri kuma muna daraja su.—Karanta Kolosiyawa 3:10, 11.
15. Ta yaya gaya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu?
15 Hanya mafi muhimmanci da za mu iya taimaka wa mutane ita ce koya musu game da Jehobah. Me ya sa muka ce haka? Domin idan mutane suka koyi abubuwa game da Jehobah kuma suka so su faranta masa rai, hakan zai sa su yi canje-canje a rayuwarsu, su ƙaunaci mutane, kuma su yi musu alheri. (Isha. 11:6, 7, 9) Kafin wani mutum mai suna Jemal ya soma bauta wa Jehobah, ya shiga wata ƙungiyar tawaye da take faɗa da gwamnatin ƙasarsu. Ƙungiyar tana ganin cewa gwamnati tana tauya hakkinsu. Jemal ya ce: “Ba a canja mutane ƙarfi da yaji. Ba haka na canja raꞌayina ba. Gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki ne ta taimaka min.” Abin da Jemal ya koya ya taimaka masa ya daina faɗa da gwamnati. Saboda haka, idan muka koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, za mu taimaka musu su daina yin munanan abubuwan da ke kawo rashin adalci.
16. Me ya sa kake so ka gaya wa mutane game da Mulkin Allah?
16 Kamar Yesu, muna marmarin gaya wa mutane cewa Mulkin Allah ne kawai zai magance dukan matsalolin ꞌyanꞌadam. Hakan zai iya ƙarfafa mutanen da aka wulaƙanta. (Irm. 29:11) ꞌYarꞌuwa Stacy, da aka ambata ɗazu ta ce: “Da yake na san cewa Jehobah zai magance dukan matsalolin da muke fama da su, hakan yana kwantar mini da hankali idan aka wulaƙanta ni, ko na ga ana yi wa wasu wulaƙanci. Jehobah yana amfani da abin da ke Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa mutane.” Muna bukatar mu yi shiri don mu iya ƙarfafa mutane da alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki. Idan ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wahalar da muke sha da kyau, hakan zai sa ka ƙara gaskata da koyarwarsa. Kuma hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka gaya wa mutane dalilin da ya sa muke shan wahala, da kuma yadda Jehobah zai magance matsalolinmu a duk inda kake. Ko a wurin aiki ne ko a makaranta.b
17. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana idan ana wulaƙanta mu?
17 Mun san cewa za mu ci-gaba da fama da rashin adalci muddin Shaiɗan ne “mai mulkin duniyar nan.” Amma mun kuma san cewa abubuwa za su canja. Jehobah ya yi alkawari cewa zai taimaka mana yanzu, kuma zai halaka Shaiɗan da dukan mugaye. (Yoh. 12:31) A Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya mana dalilin da ya sa ake shan wahala sosai a yau, da kuma cewa ya damu da waɗanda ake wulaƙantawa. (Zab. 34:17-19) Ta wurin Ɗansa, Jehobah ya koya mana abin da za mu yi idan muka ga ana rashin adalci, da kuma yadda Mulkin Allah zai magance rashin adalci gabaki ɗaya. (2 Bit. 3:13) Saboda haka, bari mu ci-gaba da yin waꞌazi game da Mulkin Allah da ƙwazo, yayin da muke marmarin ganin lokacin da “gaskiya da adalci” za su cika koꞌina a duniya.—Isha. 9:7.
WAƘA TA 158 “Ba Zai Yi Latti Ba!”
a An canja wasu sunayen.
b Ka kuma duba ƙarin bayani na 1 batu na 24-27, a ƙasidar nan Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su.