Babban taron da aka yi a Indianapolis, da ke Indiana, a 1925
1925—Shekaru Ɗari da Suka Shige
HASUMIYAR TSARO ta 1 ga Janairu, 1925 ta ce: “Muna ganin wani abu mai muhimmanci zai faru a wannan shekarar. Amma kada mu mai da hankali sosai a kan abin da zai iya faruwa. Domin yin hakan zai janye hankalinmu har mu daina yin aikin da Jehobah yake so mu yi.” Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke tsammani zai faru a 1925? Kuma ta yaya suka ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo duk da cewa abin da suke tsammani bai faru ba?
SUN YI TA JIRA
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun ɗauka cewa duniya za ta zama Aljanna a 1925. Me ya sa? Ɗanꞌuwa Albert Schroeder, wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya ce: “A lokacin mun ɗauka cewa shafaffu za su tafi sama a 1925. Kuma za a tā da wasu bayin Allah masu aminci kamar su Ibrahim, da Dauda da dai sauransu, don su yi ja-goranci a duniya.” Da abubuwan da ꞌyanꞌuwa suke tsammani za su faru ba su faru ba, hakan ya sa wasu sanyin gwiwa.—K. Mag. 13:12.
Yawancin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo, kuma sun gano cewa yin waꞌazi game da Jehobah shi ne abu mafi muhimmanci a gare su. Bari mu ga yadda suka yi amfani da rediyo kuma suka yi wa mutane da yawa waꞌazi.
AN ƘARA GINA GIDAJEN REDIYO
A 1924, mutane da yawa sun saurari gidan rediyonmu na WBBR. Don haka, a 1925, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun gina wani gidan rediyo a kusa da Chicago, Illinois. Sunan gidan rediyon shi ne WORD. Ɗanꞌuwa Ralph Leffler, wanda ya taimaka wajen gina gidan rediyon ya ce: “Da yamma idan ana sanyi mutane a wurare da yawa masu nisa suna saurarar tasharmu.” Alal misali, wani iyali da ke zama a birnin Alaska da ke da nisan fiye da kilomita 5,000 daga gidan rediyon, sun saurari shiri na farko da aka yi. Bayan sun saurari shirin, sun rubuta wasiƙa suna godiya ga masu aiki a gidan rediyon. Sun ce shirin ya ƙarfafa su, kuma ya daɗa taimaka musu su san Allah da Littafi Mai Tsarki.
Hagu: Manyan eriyoyi na gidan rediyon WORD da ke Batavia, Illinois
Dama: Ralph Leffler saꞌad da yake aiki a cikin gidan rediyon
Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1925, ta bayyana abin da ya sa mutane da yawa suke iya kama tashar daga wurare masu nisa. Ta ce: “Gidan rediyon tana cikin ɗaya daga cikin gidajen rediyo mafi ƙarfi a ƙasar Amurka. Mutane suna iya kama tashar a koꞌina a ƙasar Amurka, da Cuba, har ma da arewacin Alaska. Mutane da yawa da ba a taɓa yi musu waꞌazi ba sun so su koyi gaskiya don abin da suka ji daga gidan rediyon nan.”
George Naish
A daidai wannan lokacin kuma, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun so su kafa wani gidan rediyo don yin waꞌazi a Kanada. A 1924, an gina gidan rediyo mai suna CHUC a Saskatoon, da ke Saskatchewan. Yana cikin gidan rediyo na addini na farko-farkon da aka buɗe a Kanada. A 1925, sun bukaci su ƙaura zuwa babban wuri. Sai suka ƙaurar da gidan rediyon zuwa wani wuri da suka saya a Saskatoon. Sai suka gyara wurin don ya tsufa.
Sanadiyyar gidan rediyon nan, mutane da yawa da suke zama a ƙananan garurruka da kuma ƙauyuka a Saskatchewan sun sami damar jin waꞌazinmu a karo na farko. Alal misali, a wani gari, wata mata mai suna Graham ta rubuto wasiƙa ta ce a turo mata littattafanmu bayan da ta saurari wani shiri a rediyo. Ɗanꞌuwa George Naish ya ce: “Saƙonta ya nuna cewa tana bukatar littattafan da gaggawa. Hakan ya sa muka tura mata Studies in the Scriptures gabaki ɗaya.” Ba da daɗewa ba, matar ta soma yin waꞌazi har zuwa wurare masu nisa.
MUN KOYI WANI ABU MAI MUHIMMANCI
Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1925, yana ɗauke da wani talifi mai muhimmanci mai jigo, “Birth of the Nation.” Me ya sa talifin yake da muhimmanci? Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun riga sun san cewa Shaiɗan ne yake mulki a kan aljannu, da addinan ƙarya da kuma ƙungiyoyin kasuwanci na duniyar nan. Amma a wannan talifin, “bawan nan mai aminci da hikima” ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa su fahimci cewa bayin Jehobah a sama da duniya suna da haɗin kai. Ba sa goyon bayan Shaiɗan da duniyarsa, amma suna goyon bayan Jehobah. (Mat. 24:45) Ƙari ga haka, bawan nan mai aminci da hikima ya bayyana cewa an kafa Mulkin Allah a sama a 1914. Kuma yaƙin da ta ɓarke a sama a shekarar ya sa an kori Shaiɗan da aljannunsa zuwa duniya kuma ba za su iya koma sama ba.—R. Yar. 12:7-9.
Ya yi ma wasu wuya su amince da wannan koyarwar. Don haka, talifin ya daɗa da cewa: “Idan akwai masu karanta Hasumiyar Tsaro da ba su yarda da abin da aka faɗa a nan ba, su yi haƙuri kuma su dogara ga Jehobah yayin da suke ci-gaba da bauta masa da aminci.”
Wani ɗanꞌuwa majagaba daga Birtaniya, mai suna Tom Eyre, ya faɗi yadda yawancin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ji game da wannan talifin, ya ce: “ꞌYanꞌuwa sun ji daɗin bayanin da aka yi game da Ruꞌuya ta Yohanna sura 12. Saꞌad da suka gane cewa an kafa Mulkin Allah a sama, hakan ya sa suka yi marmarin gaya wa mutane wannan labari mai daɗi. Kuma ya sa mun so mu ƙara ƙwazo a yin waꞌazi. Ƙari ga haka, ya taimaka mana mu ga cewa Jehobah zai yi abubuwa masu ban mamaki a nan gaba.”
ZAMA SHAIDUN JEHOBAH
A yau, Shaidun Jehobah suna yawan magana game da Ishaya 43:10 da ta ce: “Ni Yahweh na ce, . . . ku ne shaiduna, ku ne na zaɓa ku zama bayina.” Amma, kafin 1925, ba a yawan magana game da ayar nan a cikin littattafanmu. A 1925, an tattauna Ishaya 43:10 da 12 a Hasumiyar Tsaro guda 11!
A ƙarshen watan Agusta 1925, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi wani babban taro a Indianapolis, da ke Indiana. A tsarin ayyuka na taron, Ɗanꞌuwa Joseph F. Rutherford ya rubuta wani saƙo don ya marabci waɗanda suka zo taron. Ya ce: “Mun zo wannan taron ne don mu sami ƙarfi daga Ubangiji kuma mu koma mu yi waꞌazi a matsayin Shaidunsa.” A kwanaki takwas da aka yi ana gudanar da taron, an ƙarfafa waɗanda suka zo su yi amfani da kowace damar da suka samu su gaya wa mutane game da Jehobah.
A ranar Asabar, 29 ga Agusta, Ɗanꞌuwa Rutherford ya yi jawabi mai jigo “A Call to Action,” wato, “Su Ɗau Matakin Yin Waꞌazi.” A jawabin, ya nanata muhimmancin yin waꞌazi, ya ce: “Jehobah ya gaya wa bayinsa . . . : Ku ne shaiduna . . . cewa ni ne Allah. Bayan haka, sai ya umurce su cewa: ‘Ku ɗaga tuta domin mutane su san hanya.’ Mutanen da za su iya zama Shaidun Jehobah su ne waɗanda ya ba su ruhunsa domin su ne bayinsa.”—Isha. 43:12; 62:10.
Takarda mai jigo Message of Hope
Bayan Ɗanꞌuwa Rutherford ya gama jawabinsa, sai ya karanta musu wata takarda mai jigo “Message of Hope,” kuma dukan masu sauraro sun amince da abin da ya karanta. Takardar ta nuna cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai sa mu sami “salama, da wadata, da lafiya, da rai, da ꞌyanci, da kuma farin ciki na dindindin.” Daga baya, an fassara abin da ke takardar zuwa yaruka da yawa, kuma aka buga don a rarraba saꞌad da ake waꞌazi. An rarraba wajen miliyan 40.
Ko da yake Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su canja sunansu zuwa Shaidun Jehobah a wannan lokacin ba. Duk da haka, sun soma gane muhimmancin yin waꞌazi game da Jehobah a matsayin shaidunsa.
SUN SOMA KOMAWA ZIYARA
Yayin da adadin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki yake karuwa a faɗin duniya, an ƙarfafa su su riƙa komawa suna ziyartar waɗanda suka so waꞌazinmu. Bayan waꞌazi na musamman da aka yi don a rarraba takardar nan, Message of Hope, an gaya wa ꞌyanꞌuwa a cikin Bulletina cewa: “Ku koma ku ziyarci waɗanda kuka bar musu wannan takardar.”
Bulletin na Janairu 1925 na ɗauke da rahoton da wani ɗanꞌuwa da ke zama a birnin Plano, da ke Texas ya bayar. Ya ce: “Mun yi farin ciki sosai domin muna samun sakamako mai kyau idan muka koma wuraren da muka taɓa yin waꞌazi maimakon sabbin wurare. Akwai wani ƙaramin gari a yankinmu da aka yi waꞌazi sau biyar cikin shekaru goma da suka shige. . . . A kwanan nan, ꞌYarꞌuwa Hendrix da mahaifiyata sun sake yin waꞌazi a wurin kuma sun ba da littattafai fiye da yadda aka taɓa bayarwa.”
A ƙasar Panama, wani majagaba ya rubuto cewa: “Mutane da yawa da suka kore ni daga gidansu da farko, sukan canja raꞌayinsu idan na koma karo na biyu ko na uku. Yawancin abin da na yi wannan shekarar shi ne, komawa wurin mutanen da na yi musu waꞌazi a dā, kuma na ji daɗin tattaunawar da na yi da wasu daga cikinsu.”
ABIN DA ZA MU YI A NAN GABA
A ƙarshen shekara ta 1925, Ɗanꞌuwa Rutherford ya rubuta wa majagaba wasiƙa. A wasiƙar, ya gaya musu abin da aka cim ma a shekarar, da wanda za a yi a nan gaba. Ya ce: “A shekarar da ta shige, kun sami damar ƙarfafa mutane da yawa da suke baƙin ciki. Babu shakka hakan ya sa ku farin ciki sosai . . . A 1926, za ku sami damar yin waꞌazi game da Allah da kuma Mulkinsa, kuma ku sa mutane su san ainihin bayinsa. . . . Bari dukanmu mu haɗa muryoyinmu wajen yabon Allahnmu da kuma Sarkinmu.”
A ƙarshen shekara ta 1925, ꞌyanꞌuwan sun soma shirin yadda za su faɗaɗa Bethel da ke Brooklyn. A 1926, za su soma aikin gine-gine da ƙungiyarmu ba ta taɓa yi irin su ba.
Aikin gine-gine da aka yi a Adams Street, Brooklyn, New York, a 1926
a Yanzu shi ne ake kiran, Littafin Taro Don—Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu.