ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI
Mu Riƙa Ƙarfafa Juna
Muna jin daɗi sosai idan muka zauna da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Amma don mu amfana sosai, muna bukatar mu yi wani abu, wato ƙarfafa juna. Littafi Mai Tsarki ya ce irin wannan ƙarfafawar “kyauta daga wurin Allah” ne. (Rom. 1:11, 12, NWT) Ta yaya za mu iya yin hakan?
Mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwa ta wurin abubuwan da muke faɗa. Alal misali, yayin da muke ba da kalami a taro, zai dace mu yi magana a kan abin da muka koya game da Jehobah, da Kalmarsa da kuma ꞌyanꞌuwanmu. Maimakon mu yi magana game da kanmu ko kuma raꞌayinmu. A duk lokacin da muke tare da ꞌyanꞌuwanmu, mu riƙa yin magana a kan abin da zai ƙarfafa bangaskiyarsu.
Ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa ta wurin abubuwan da kake yi da kuma shawarwarin da kake yankewa. Alal misali, wasu sun zaɓi su ci-gaba da yin hidima ta cikakken lokaci duk da cewa suna fama da matsaloli. Wasu kuma suna halartan taron tsakiyar mako babu fasawa duk da cewa suna gajiya sosai bayan aiki ko kuma suna fama da rashin lafiya mai tsanani.
Shin abubuwan da kake faɗa da kuma abubuwan da kake yi suna ƙarfafa ꞌyanꞌuwa? Kana mai da hankali a kan abubuwan da ꞌyanꞌuwa suke yi ko faɗa da za su ƙarfafa ka?