KU ZAUNA A SHIRYE!
Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Addini da Yakin Yukiren?
Ka yi la’akari da wasu abubuwan da manyan limaman addini suka fada game da yakin da ake yi a Yukiren:
A ranar 7 ga Maris, 2022, jaridar EUobserver ta ce: “Wani shugaban Cocin Orthodox na Rasha da ake kira Patriarch Kirill bai ce kome game da harin da Rasha ta kai wa kasar Yukiren ba. . . . Cocinsa ta ci gaba da yada labaran karya game da kasar Yukiren kuma shugaba Putin yana amfani da wadannan labaran don ya ba da hujja cewa harin da ya kai wa Yukiren daidai ne.”
A ranar 8 ga Maris, 2022, jaridar AP News ta ce: “Patriarch Kirill . . . ya bayyana cewa harin da Rasha ta kai wa Yukiren ya dace domin tana yakan zunubi ne.”
A ranar 16 ga Maris, 2022, jaridar Jerusalem Post ta ce, “Shugaban Cocin Orthodox na Yukiren da ake kira Metropolitan Epiphanius I na birnin Kyiv ya sa wa mutanensa albarka ‘su je su yaki ’yan Rasha da suka kawo musu hari’ . . . kuma [ya] ce kashe sojojin Rasha ba zunubi ba ne.”
A ranar 24 ga Fabrairu, 2022, kungiyar UCCROa ta ce: “A matsayinmu na [Ukrainian Council of Churches and Religious Organizations (UCCRO)] muna goyon bayan sojojin Yukiren da dukan wandanda suke taimaka mana a yakin, muna sa musu albarka domin yadda suke kokarin kāre mu daga makiyanmu kuma muna addu’a a madadinsu.”
Mene ne ra’ayinka? Kana ganin ya kamata addinan da suke da’awar cewa su mabiyan Yesu ne su karfafa membobinsu su je yaki? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?
Tarihin yadda shugabannin addinai suke goyon bayan yaki
Tarihi ya nuna cewa shugabannin addinai suna yawan amincewa a je yaki ko yana da kyau a yi yaki ko kuma ya kamata a yi yaki, duk da cewa suna yi kamar suna son zaman lafiya. Shaidun Jehobah sun yi shekaru da yawa suna taimaka wa mutane su ga cewa abin da suke yi munafurci ne. Ga wasu misalai daga littattafanmu.
Talifin nan, “The Crusades—A ‘Tragic Illusion’ ” ya nuna cewa Cocin Roman Katolika ne suka sa a yi kisan kare dangi kuma suka ce hakan ibada ce ga Allah da kuma Kristi.
Talifin nan, “The Catholic Church in Africa” ya nuna misalan yadda shugabannin addinai sun kasa hana mutane yakin kabilanci, har da yakin kare dangi.
Talifofin nan, “Is Religion to Blame?,” da “Religion’s Role in Man’s Wars,” da kuma “Religion Takes Sides” sun bayyana cewa a yawancin yakin da ake yi, limaman Kotolika da na Orthodox da kuma na Farostatan ne suke goyon bayan bangare biyu da suke yaki da juna.
Ya kamata Kiristoci su goyi bayan yaki?
Abin da Yesu ya koyar: “Ka kaunaci makwabcinka kamar yadda kake kaunar kanka.” (Matiyu 22:39) “Ku kaunaci wadanda ba sa kaunarku.”—Matiyu 5:44-47.
Ka lura da wannan: Zai dace addinin da ke da’awar yin biyayya ga dokar Yesu game kauna ta karfafa membobinta su je yaki su kashe mutane? Don ka ga amsar tambayar nan, ka karanta talifofin nan, “True Christians and War” da kuma “Is It Possible to Love One’s Enemies?”
Abin da Yesu ya ce: “Mulkina ba iri na duniya ba ne. Da mulkina iri na wannan duniya ne, da masu yi mini hidima za su yi yaki domin kada a bashe ni.” (Yohanna 18:36) “Duk wanda ya dauki takobi, takobi ne zai kashe shi.”—Matiyu 26:47-52.
Ka lura da wannan: Idan Kiristoci ba su yi yaki don kāre Yesu ba, zai dace su yi yaki don wani dalili? Ka karanta talifin nan, “Is War Compatible With Christianity?” don ka ga yadda Kiristoci na farko suka bi misalin Yesu da koyarwarsa da dukan zuciyarsu.
Me zai faru da addinan da ke karfafa yin yaki?
Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah yana tir da addinan da suke da’awar cewa suna wakiltar Yesu amma ba sa bin koyarwarsa.—Matiyu 7:21-23; Titus 1:16.
Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya nuna cewa Allah zai tambayi alhakin “jinin dukan wadanda aka kashe a duniya” daga hannun addinan nan. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:21, 24) Don ka san dalilin da ya sa zai yi hakan, karanta talifin nan, “Mece ce Babila Babba?”
Yesu ya ce dukan addinan da Allah ya yi tir da su za a hallaka su don munanan ayyukansu. Za a hallaka su kamar yadda ake yi wa itace marar kyau da ke ba da ’ya’ya marasa kyau, ana “sare shi a jefar a cikin wuta.” (Matiyu 7:15-20) Don ka ga yadda hakan zai faru, ka karanta “The End of False Religion Is Near!”
Inda aka dauko hotuna, hagu zuwa dama: Photo by Sefa Karacan/Anadolu Agency/Getty Images; Maxym Marusenko/NurPhoto via Getty Images
a Kungiyar UCCRO, ko Ukrainian Council of Churches and Religious Organizations, na kunshe da coci guda 15 da suke wakiltar cocin Orthodox da cocin Greek Katolika da cocin Roman Katolika da cocin Farostatan da cocin Evangelical da addinin Yahudawa da kuma Musulmai.