Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 55
  • Sunayen Su Waye ne ke Rubuce Cikin “Littafin Rai”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sunayen Su Waye ne ke Rubuce Cikin “Littafin Rai”?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • An Rubuta Sunanka a Cikin “Littafin Rai”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 55

Sunayen Su Waye ne ke Rubuce Cikin “Littafin Rai”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

“Littafin rai,” da ake kira “littafin tunawa,” yana dauke da sunayen mutanen da za su sami rai na har abada. (Ru’ya ta Yohanna 3:5; 20:12; Malakai 3:16) Allah yana zaban sunayen nan dangane da yadda mutumin ya kasance da aminci a gare shi ne.​—Yohanna 3:16; 1 Yohanna 5:3.

Allah yana tune da kowanne bawansa da ya kasance da aminci, kamar yana rubuta sunayensu ne cikin wani littafi, tun “kahuwar duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 17:8) Mutum na farko mai aminci da sunansa ke cikin littafin rai shi ne Habila. (Ibraniyawa 11:4) Littafin rai, ba kawai yana dauke da sunayen masu aminci ba, amma yana nuna mana cewa Jehobah Allah ne mai kauna wanda “ya san wadanda ke nasa.”​—2 Timotawus 2:19; 1 Yohanna 4:8.

Shin za a iya share sunaye daga “littafin rai”?

Hakika. Ga abin da Allah ya ce wa masu rashin biyayya a Isra’ila ta dā: “Wanda ya yi zunubi gareni duka, shi ne zan shafe daga cikin littafina.” (Fitowa 32:33) Amma idan muka kasance da aminci za a bar sunayenmu cikin “littafin rai.”​—Ru’ya ta Yohanna 20:12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba