Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 27
  • Me Ya Sa Ba Ni da Abokai?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Ba Ni da Abokai?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wasa kwakwalwa a kan batun kadaici
  • Gaskiya game da abokantaka da kuma kadaici
  • Yadda za ka yi nasara
  • Jehobah Yana Tare da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 27
Wata matashiya da take fama da jin kadaici

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Ba Ni da Abokai?

Kana intane kana kallon hotunan wani fati da aka yi. Abokanka duka sun hallara kuma suna liyafa. Amma wani ba ya wurin. Wane ne wannan? Kai ne!

Hakan ya sa ka bakin ciki, sai ka tambayi kanka: ‘Me ya sa ba a gayyace ni ba?’

Kana ganin an yi ban da kai! Kamar dai dangantakarka da wasu duk ya rushe kamar rumfar kara. Kana bakin ciki don ka kadaita, sai ka tambayi kanka, ‘Me ya sa ba ni da abokai?’

  • Wasa kwakwalwa a kan batun kadaici

  • Bayani game da abokantaka da kuma kadaici

  • Yadda za ka yi nasara

  • Abin da tsararka suka ce

  • Yadda za ka shawo kan shakkar yin abokantaka

Wasa kwakwalwa a kan batun kadaici

Gaskiya ko Karya

  1. Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana da abokai da yawa.

  2. Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana shigar dandalin intane.

  3. Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana yawan aika sakonni da yawa ta wayar selula.

  4. Ba za ka taba jin kadaici ba idan kana taimaka wa mutane.

Amsar dukan wadannan kalamai hudu karya ce.

Me ya sa?

Gaskiya game da abokantaka da kuma kadaici

  • Idan mutum yana da abokai da yawa ba zai hana shi jin kadaici ba.

    Anne ta ce: “Na damu da abokai na sosai, amma wani lokaci ina ganin kamar ba su damu da ni. Abin da zai fi sa ka ji kadaici shi ne idan kana da abokai da yawa amma ba sa nuna suna kaunarka ko kuma cewa sun damu da kai ba.”

  • Shiga dandalin intane ba zai sa ka daina jin kadaici ba.

    Elaine ta ce: “Wasu mutane suna tara abokai yadda wasu ke tara kayan adon daki. Amma cika daki da kayan ado ba zai sa wani ya ji kana kaunarsa ba. Idan abokanka ba na kirki ba ne, ba bambancinsu da kayan adon daki.”

  • Yawan aika da sako a waya ba shi zai sa ka daina jin kadaici ba.

    Serena ta ce: “Wani lokaci idan kana jin kadaici sai ka rika duba wayarka kana tsammanin wani ya aika maka sako. Yanayin zai fi muni idan kana jin kadaici kuma babu wanda ya aika maka sako!”

  • Taimaka wa wasu ba ya nufin cewa ba za ka taba jin kadaici ba.

    Richard ya ce: “Nakan yi wa abokaina kyauta sosai amma na lura cewa ba su taba ba ni kyauta ba sam. Ko da yake ba na nadama cewa na yi musu kyauta amma ina mamakin cewa ba su taba yi mini alheri ba.”

Gaskiyar al’amarin: A takaice, kadaici yadda mutum yake tunaninsa ne. Wata matashiya mai suna Jeanette ta ce: “Halin mutum ne, ba koya ya yi ba.”

Me za ka iya yi idan kana ji kamar ba ka da abokai kuma kana jin kadaici?

Yadda za ka yi nasara

Wata matashiya da take da fargaba

Ka kasance da gabagadinka.

Jeanette ta ce: “Rashin tabbata da kanka ya iya sa mutumin jin kadaici. Yin abota ba shi da sauki idan kana yawan ji kamar ka fi wasu.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.” (Galatiyawa 5:14) Idan muna so mu more abokantaka mai kyau, dole ne mu so kanmu kuma mu kasance da saukin kai.​—Galatiyawa 6:3, 4.

Wani matashi da ke tausayin kansa

Ka guji yin shagwaba.

Erin ta ce: “Kadaici yana kama da kasa. Idan ka ci gaba da jin kadaici, zai zama maka da wuya ka bar halin. Idan ka kyale jin kadaici ya zama abin jikinka, za ka soma shagwaba kuma mutane za su rika guje maka.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kauna . . . ba ta bida ma kanta.” (1 Korintiyawa13:​4, 5) Gaskiyar ita ce, idan mun fi damuwa da kanmu kawai, ba za mu yi tunanin wasu ba kuma hakan zai sa mutane su guje mu. (2 Korintiyawa 12:15) Batun shi ne: Idan yadda wasu za su aikata ne zai sa ka yi nasara, to lallai ba za ka yi nasara ba! Irin furucin nan “Babu wanda yake kirana” da kuma “Babu wanda yake gayyata ta zuwa wani wuri” yana nufin cewa idan wasu ba su yi maka alheri ba, ba za ka yi farin ciki ba. Ba ka ganin cewa kana sa su ga cewa ka dogara ne gare su?

Wani matashi yana ki da sigari

Kada ka yi abokantaka da kowane irin mutum.

Brianne ya ce: “Wadanda suke jin kadaici suna so a nuna musu cewa ana son su ko da wanene yake yin hakan. Su dai a so su ne kawai. Wasu mutane za su nuna suna son ka amma daga baya su cuce ka. Lokacin ne za ka dada jin kadaici.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Misalai 13:20) Mayunwaci yakan ci duk abin da ya samu. Haka ma yake da wadanda suke neman abokai, za su iya neman abokai a inda bai dace ba. Har za su iya fadawa a hannun wadanda za su damfare su da jin cewa suna bukatar abokantaka.

A karshen: Babu wanda ba ya jin kadaici; wasu suna jin kadaici fiye da wasu. Kadaici yadda mutum yake ji ne kawai ko da yake yana shafan kowa. Sau da yawa, abin da muke tunaninsa ne ke sa mu jin kadaici, kuma za mu iya sarrafa tunaninmu.

Ka kasance da halin da ya dace game da wasu, kuma kada ka so kanka. Jeanette ta ce: “Ba kowa ba ne zai iya zama abokinka na kud da kud da dadewa, amma dai za ka iya samun mutane da sun damu da kai. Mutane sun fi son haka. Abin da zai taimake ka guje wa jin kadaici ke nan.”

Kana bukatar karin taimako ne? Ka karanta talifin nan “Yadda za ka shawo kan shakkar abokantaka.” Ka kuma sauko da wannan PDF mai jigo “Jure da Kadaici.”

ABIN DA TSARARKA SUKA CE

Vanessa

Vanessa ta ce: “Ka gaya wa wani yadda kake jin kadaici. Kada ka boye abin da ke damun ka. Watakila akwai wasu da ke da irin wannan matsalar. A wani lokaci, kana bukatar aboki ne kawai don ka sake.”

Taylor

Taylor ya ce: “Kada ka ga laifin wasu don kana jin kadaici. Kila a wani lokacin kai ne ka ware kanka daga mutane. Saboda haka, ka yi iyakar kokarinka don ka sake soma cudanya da mutane. Idan hakan bai taimaka ba, ka yi kokarin neman sababbin abokai, kila ma da wadanda ba ka taba kokarin yin abokantaka da su ba.”

Yadda za ka shawo kan shakkar yin abokantaka

Elaine ta ce: “Wata abokiyata tana fama da kadaici sosai. Ko da yake tana tare da mutane da suke kula da ita, amma har ila tana ganin babu wanda yake kaunarta ko da ya damu da ita. Tana lamunin cewa babu abin da yake damunta amma tana cikin matsala sosai. Kokarin da take yi don ta nuna cewa ba ta da matsala ya sa ba ta iya yin abokantaka ba. Duk mutanen da ta sadu da su suna yi mata ganin ba ruwana da kowa, kuma hakan ya hana ta samun abokai.

“Abokiyata tana tsoron cewa abokanta za su bata mata rai, saboda haka idan mutane sun so su yi abokantaka da ita sai ta musu ganin su munafukai ne abokantakar ba za ta dade ba. Tana jin kadaici domin mutane ba su fahimce ta ba kuma ta ki ta gaya wa kowa matsalarta.

“Abokiyata tana bukatar ta fahimci cewa yin tarayya yana sa mutane su so juna kuma ya sa mutane su san ta. Zai sa su so su yi abokantaka da ki ke bukata. Ina fata abokiyata za ta sami taimakon da take bukata don ta shawo kan tsoron yin abokantaka.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba