Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwhf talifi na 8
  • Yadda Za Ka Zama Mai Hakuri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka Zama Mai Hakuri
  • Taimako don Iyali
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me ya sa kake bukatar ka zama mai hakuri?
  • Ta yaya za ka nuna cewa kana da hakuri?
  • Muna Bukatar Haƙuri a Hidimarmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ka Ci Gaba da Zama Mai Hakuri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Yi Koyi Da Haƙurin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Koyi Darasi Daga Haƙurin Jehobah Da Na Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Taimako don Iyali
ijwhf talifi na 8
Wani magidanci yana jiran matarsa da bacin rai ta gama sayan takalmi

TAIMAKO DON IYALI| AURE

Yadda Za Ka Zama Mai Hakuri

Wani mai suna John ya ce: “A kowace rana, batutuwa na iya tasowa da za su gwada ko mata da miji masu hakuri ne. Kafin ka yi aure watakila kana ganin cewa hakuri ba hali ne mai muhimmanci ba, amma wannan hali yana da muhimmanci sosai idan kana so ka yi nasara a aure.”

  • Me ya sa kake bukatar ka zama mai hakuri?

  • Ta yaya za ka nuna cewa kana da hakuri?

  • “Hakuri yana da muhimmanci”

Me ya sa kake bukatar ka zama mai hakuri?

  • Aure zai sa ku san kasawar juna sosai.

    Wata mai suna Jessena ta ce: “Bayan kun yi aure, za ku saba da juna, kuma hakan zai sa ya yi muku sauki ku soma mai da hankali ga halayen juna da ba ku so. Sa’ad da hakan ya faru, yana iya yi muku sauki ku soma fushi.”

  • Idan ba ka da hakuri, kana iya yin magana da garaje.

    Wani mai suna Carmen ya ce: “Nakan fadi abin da ke damuna da gaggawa, kuma hakan yana sa in fadi abin da bai kamata ba. Da a ce ina da hakuri sosai, da zan iya bin batun da kyau ba tare da yin wata magana ba.”

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kauna tana da hakuri da kirki.” (1 Korintiyawa 13:4) Ya kamata mutane biyu da ke kaunar juna su kasance da hakuri. Amma, ba hakan take a kowane lokaci ba. John da muka ambata dazu, ya ce: “Yana da sauki mutum ya zama marar hakuri.”

Ta yaya za ka nuna cewa kana da hakuri?

  • Sa’ad da wani yanayi ya bukaci ka nuna hakuri.

    Misali: Sa’ad da matarka ko mijinki ya yi miki bakar magana. Kina iya yin tunanin ramawa.

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kada ka zama mai saurin fushi, gama wawa ne mai cike da fushi.”​—Mai-Wa’azi 7:9.

    Yadda za ka nuna kana da hakuri: Ka dakata. Kafin ka ba wa matarka ko mijinki amsa don abin da ya ce, ki yi tunanin cewa ba don ya bata miki rai ne ya sa ya magana haka ba. Wani littafi mai suna Fighting for Your Marriage ya ce: “Yawancinmu mukan mayar da martani bisa abin da muke tunani matarmu ko mijinmu yake nufi ba tare da jin asalin abin da yake fada ba.”

    Kamar yadda ake saka itace a wuta, wani magidanci yana mayar da martani ga matarsa da ta bata masa rai; kamar wutan da ya kusan mutuwa, wani magidanci ya kame kansa sa’ad a matarsa ta bata masa rai

    Hakika, ko da matarka ko mijinki yana so ya bata miki rai ne, kasancewa mai hakuri da kuma guje wa ramako zai iya sa batun ya yi sanyi maimakon zafi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda babu itace, wuta takan mutu.”​—Karin Magana 26:20.

    Wani mai suna Ethan ya ce: “A duk lokacin da ka soma ganin matarka kamar abokiyar hamayya ce, ka dakata kuma ka yi tunani a kan abin da ya sa kake kaunar ta kuma ka yi kokarin yi mata wani abu mai kyau.”

    Ka yi tunanin wannan:

    • Mene ne za ka yi idan matarka ko mijinki ya yi ko ya fadi abin da ya bata miki rai?

    • Ta yaya za ka nuna hakuri sosai idan hakan ya sake faruwa?

  • Sa’ad da wata matsala ta ci gaba da gwada hakurinka.

    Misali: Matarka ko mijinki yana yawan makara kuma hakan yana sa ki jiran shi da fushi.

    Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Kuna ta yin hakuri da juna. Idan kuma wani a cikinku ya yi wa wani laifi, ku gafarta masa.”​—Kolosiyawa 3:13.

    Yadda za ka nuna hakuri: Ka yi kokarin saka bukatun aurenku a kan gaba fiye da bukatun ka. Ka yi wa kanka wannan tambayar, ‘Shin wannan batun zai taimaka wa aurenmu ne ko kuma lalace ta ne?’ Ka kuma tuna cewa, “dukanmu mukan yi kuskure da yawa.” (Yakub 3:2) Hakan na nufin cewa kana da abubuwa da ya kamata ka yi gyara akan su.

    Wata mai suna Nia ta ce: “A wasu lokuta, yana mini sauki in yi hakuri da abokaina fiye da mijina. A ganina, da yake mun saba da juna sosai, hakan ya sa na san kasawarsa. Amma hakuri hanya ce na nuna kauna, kuma alama ne cewa ina daraja shi. Don haka, halin nan yana da muhimmanci a aurenmu.”

    Ka yi tunanin wannan:

    • Kana yin hakuri sa’ad da matarka ko mijinki ya yi laifi?

    • Ta yaya za ka nuna hakuri sosai a nan gaba?

“Hakuri yana da muhimmanci”

Jessena tare da mijinta Hayden

Jessena da mijinta Hayden sun ce: “Zama masu hakuri yana da muhimmanci don a yi nasara a aure. Mata da miji ajizai ne, don haka, dole ne a samu matsaloli dabam-dabam. Kuma da yake halayensu ya bambanta hakan ma na iya sa fushi. Idan ba mu zama masu hakuri ba, irin wadannan matsaloli suna iya bata aurenmu a sannu-a-hankali.”

Bita: Yadda Za Ka Zama Mai Hakuri

Sa’ad da wani yanayi ya bukaci ka nuna hakuri

Kafin ka ba wa matarka ko mijinki amsa don abin da ya ce, ki yi tunanin cewa ba don ya bata miki rai ne ya sa ya yi magana haka ba.

Sa’ad da wani matsala ya ci gaba da gwada hakurinka

Ka saka bukatun aurenku a kan gaba fiye da bukatunka. Ka tuna cewa kai ma kana da halayen da ya kamata ka kawar da su.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba