Ƙarin Bayani
a Alal misali, Yarabawa na Nijeriya suna da al’adar gaskata da ra’ayin sāke haifuwar kurwa. Saboda haka yayinda uwa ta yi rashin yaro, akan yi baƙinciki na ƙwarai amma na ƙaramar lokaci ne, gama kamar yadda ra’ayin Yarabawa ya sa shi fa: “Ruwa ne kawai ya zuba. Ƙwaryar bata fashe ba.” Bisa ga Yarabawa fa, ƙwaryar da ke ɗauke da ruwan, uwar, zata iya haife wani yaro kuma—watakila sāke haife mataccen. Shaidun Jehovah basu bin wasu al’adu masu tushi bisa camfi da ke fitowa daga ra’ayoyin ƙarya na rashin mutuwar kurwa da kuma na sāke haifa wanda ya mutu, waɗanda basu da tushe cikin Littafi Mai-Tsarki.—Mai-Wa’azi 9:5, 10; Ezekiel 18:4, 20.