Ƙarin Bayani
c A Matta 23:4, an yi amfani da wannan kalmar wajen kwatanta “kaya masu-nauyi,” wato, yawan dokoki da kuma al’adun mutane da marubuta da Farisiyawa suka ɗaura a kan mutane. Wannan kalmar kuma an fassara ta “zafin hali” a Ayukan Manzanni 20:29, 30 kuma tana nuni ne ga ’yan ridda masu zafin hali waɗanda za su yi “karkatattun zantattuka” domin su yaudari mutane.