Ƙarin Bayani
a Farawa 2:10-14 ta ce: “Kogi kuma ya fito daga cikin Adnin domin ya shayadda gona; daga can kuma ya rabu, ya zama kawuna huɗu. Sunan na farin Pishon ne . . . Sunan kogi na biyu kuma Gihon ne . . . Sunan kogi na uku kuma Hiddekel ne [ko Tigris]: shi ne wanda ke gudu gaban Assyria. Kogi na huɗu kuma Euphrates ne.” Babu wanda ya san inda koguna biyu na farko suke.