Ƙarin Bayani
a Sarkin ya daɗa wa Yahudawa rana ɗaya don su gamar da magabtansu. (Esther 9:12-14) Har yau, Yahudawa sukan yi biki a kowane watan Adar da ya yi daidai da ƙarshen watan Fabrairu zuwa farkon watan Maris, don su tuna da nasarar da suka yi. Ana kiran bikin Purim wato jam’in Pur da ke nufin ƙuri’ar da Haman ya jefa don ya halaka Isra’ilawa.