Ƙarin Bayani
c Wani abin da ya sa ba su ɗauki wannan kashedin da muhimmanci ba da farko shi ne, an ɗauka cewa ya shafi ƙaramin garken Kristi ne kaɗai wanda ya ƙunshi shafaffu 144,000. A Babi na 5,za mu ga cewa kafin shekara ta 1935, an ɗauka cewa “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, ya ƙunshi membobin coci-cocin Kiristendam; kuma za a ba su ladar zama rukuni na biyu da za su je sama domin sun goyi bayan Kristi a lokacin ƙarshe.