Ƙarin Bayani
d Ɗan’uwa Frederick W. Franz ya bayyana a cikin wata wasiƙa da ya rubuta a ranar 14 ga Nuwamba, 1927, cewa: “Ba za mu yi bikin Kirsimati wannan shekarar ba. Iyalin Bethel sun yarda cewa ba za su ƙara yin bikin Kirsimati ba.” Bayan wasu ’yan watanni, Ɗan’uwa Franz ya rubuta wata wasiƙa a ranar 6 ga Fabrairu, 1928, ya ce: “Da sannu a hankali, Ubangiji yana tsarkake mu daga koyarwar Shaiɗan da kuma Addinan ƙarya.”