Ƙarin Bayani
a Hakan ba ya nufin cewa Shaiɗan ne yake ja-gorar mutanen da suke ƙoƙarin hana ka yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Amma Shaiɗan shi ne “allah na wannan zamani” kuma ‘duniya duka tana kwance cikin Shaiɗan.’ Saboda haka, idan mutane suka yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Jehobah, kada ka yi mamaki.—2 Korintiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19.