Ƙarin Bayani
a A ganin wasu likitoci sashe huɗu na jini ɗaya ne da ƙananan sassan jini. Saboda haka, idan ka tsai da shawara cewa ba za ka karɓi jini gabaki ɗaya ko kuma sashe huɗu na jini ba, wato jajayen jini da fararen jini da kamewar jini da kuma ruwan jini, ka bayyana hakan ga likitan.