Ƙarin Bayani
a Wannan furucin “farkon duniya” yana nufin watsa iri kuma hakan yana da alaƙa da haihuwa. Saboda haka, wannan furucin ya shafi zuriyar ’yan Adam da aka fara haifa. Amma, me ya sa Yesu ya ambaci Habila sa’ad da yake magana game da “farkon duniya” a maimakon Kayinu, wanda shi ne ɗa na fari? Domin tunanin Kayinu da ayyukansa sun nuna cewa ya yi wa Jehobah tawaye ne da gangan. Da halama cewa hukuncin da aka yi wa Kayinu ɗaya ne da na iyayensa, wato, ba za a ta da shi daga matattu ba.