Ƙarin Bayani
a Abin taƙaici, mafassaran Littafi Mai Tsarki da yawa ba su yi amfani da sunan Allah ba duk da cewa sunan ya bayyana sau da yawa a cikin Nassosin Ibrananci, wato Tsohon Alkawari. Akasin haka, sun sauya sunan Allah da laƙabi kamar su “Ubangiji” da kuma “Allah.” Don ƙarin bayani a kan wannan batun, ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, shafuffuka na 195-197. Shaidun Jehobah ne suka wallafa.