Ƙarin Bayani
d Bayan mutuwar manzannin, Shaiɗan ya sa ridda kuma ta haɓaka a cikin ƙarnuka da yawa. A wannan lokacin, ba a mai da hankali ga umurnin da Yesu ya bayar na almajirtar da mutane ba. Amma hakan ya canja a “lokacin kaka,” wato kwanaki na ƙarshe. (Mat. 13:24-30, 36-43) Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafuffuka na 9-12.