Ƙarin Bayani
b Septuagint yana nufin “Saba’in.” An ce an soma fassarar ne a Masar wajen shekaru 300 kafin haihuwar Yesu kuma an kammala fassarar wajen shekaru 150 bayan haka. Wannan fassarar tana da muhimmanci har ila don tana taimaka wa masana su san ma’anar wasu kalmomin Ibrananci da kuma ayoyi da suke da wuyan fahimta.