Ƙarin Bayani
a Wasu marubuta sun ce Yahuda ya yi ƙaulin littafin afokirifa da ake kira Book of Enoch (Littafin Enok), amma wannan littafin ya faɗi abubuwa game da Anuhu da ba gaskiya ba ne. Ƙaulin annabcin Anuhu da aka yi a ciki gaskiya ce, amma da alama cewa an ɗauko shi ne daga wani littafi ko furuci na zamanin dā wanda ba a san inda yake a yau ba. Wataƙila Yahuda ya yi amfani da wannan littafin ko furucin, ko kuma ya sami labarin Anuhu daga wurin Yesu wanda ya shaida rayuwar Anuhu daga sama.