Ƙarin Bayani
b Saratu ‘yar’uwar Ibrahim ce. Mahaifinsu ɗaya ne, wato Terah amma mahaifiyarsu ce ba ɗaya ba. (Farawa 20:12) Ko da yake a yau an haramta yin irin wannan auren, amma yana da muhimmanci mu yi la’akari da yadda rayuwa take a lokacin. Mutane ba su daɗe da zama ajizai ba. Don hakan, irin wannan aure ba zai kawo matsala ga ‘ya’yan da za a haifa ba. Amma abubuwa sun canja bayan wajen shekara 400. Shi ya sa Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa ta haramta auren dangi.—Levitikus 18:6.