Ƙarin Bayani
a Wani Farfesa mai suna Marvin Pate ya ce: “Mutane sun daɗe suna yin imani cewa ‘yau’ da aka ambata a ayar tana nufin sa’o’i ashirin da huɗu. Amma matsalar wannan ra’ayin ita ce ta saɓa wa wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa an fara binne Yesu a kabari sa’ad da ya mutu (Mat. 12:40; A. M. 2:31; Rom. 10:7) bayan haka, sai ya koma sama.”